*Safiyyah galadanchi**JAJIRTACCEABUBAKARl SADEEQ*
*SHAFINAASHIRINDA BAKWAI*
Tana bacci ya fita danko wanka bai tsaya yayi ba dan haka bata san fitarshi ba, bata kawo wani tunani a ranta ba akan fitar tashi illa mamakin baccin da tayi da safen, aiki ta shiga yi na gyaran gidan da hada abin breakfast dan a tunaninta baiyi nisa ba.
Koda isarsa wurin saida yaji jiri ya debeshi yayi saurin dafa bangon wani shago zuciyarshi nayi mishi wani irin zafi yasan sanadin gobarar ne ake ta kiranshi, ga yanayin daya gani awurin ya tabbatar ba a fitar da komai ba awurin, karfin halin karasawa wurin yayi nan aka tare shi da mugun labari wani yace yana daga masu kwana waje acikin unguwar "shabiyun dare duk bamuyi bacci ba babu wani abu mai kamada wuta a wurin amma karfe biyu da rabi fitsari ya tasheni sai naga wuta naci balbal kafin na kirawo jama'a har ayi kiran fire service wuri ya gama cinyewa dan shagon ma kin budewa yayi babu wanda zaice maka ga musababbin wutar nan Allah dai ne yabarwa kanshi sani" sadeeq ya gyada kai yana cewa "to Allah ya kyauta yamayar mana da alkhairi idan yazo kuce masa wanda ya siya shinkafa jiya bai dauka ba yazo baya nan zan sake dawowa" sallama yayi musu ya wuce gida yanata kokarin danne zuciyarshi tareda yanke shawarar bazai fadawa koda ummee ba dan a ganinsa shi a halin yanzu yadda yake jin zuciyarshi inaga ita datake karkashinsa taga abinda ma yake takama dashi duk ya rasa to da me zai dauki dawainiyarta.
Koda ya shiga gidan tayi wanka ta saka riga da skirt na atamfa brown da zanen flower baki ta shafa powder da kwalli bakinta sai kyalli yake, oyoyo tayi masa tana rungumeshi sannan tace, "duk business dinne haka fita ba a sanar dani ba" daukarta yayi kamar baby ya karasa shiga palon da ita yana cewa "wani abu naje na danyi na dawoai ban dade ba kuma naga kina baccin gajiya" tayi dariya tana cewa "Allah ya bada sa'a amma ai dole na rama baccin daka hanani" shuru yayi yana murmushi ta sake cewa "Abinci fa"? Ya sake ta daga rikon dayayi mata a jikinshi yace "dauko mini" kamar zata gane yana cikin damuwa sai kuma tace aranta "sadeeq da wuyar shaani yau mutum yake gobe ba mutum ba" abincin ta kawo masa ya soma ci a hankali ganin kamar dole yake turashi yasaka tasa hannunta tana bashi tana yimai kallon soyayya har saida ya cinye shi duka sannan tace "idan bakayi wanka ba muje in hada maka ruwan" mikewa yayi batareda yayi magana ba, har lokacin bata gama yadda da yanayinsa ba wankan yayo ya fito ta tayashi shiryawa tana cewa "Ni wallahi banason ramar nan da kake kar ace ina cutar ka" ya rike baki yana dariya yace "sekace wani yaro nine dai na damu da ramar ki naga haske kawai kike baki kiba" ta kalli jikinta tace "ni yanxu nan har ramata ake ganewa? Dama haka nake ai" yace "amma ya kamata ki kara saboda kulawar da nake baki" ya fada yana mata kallon cikin ido kunya taji tayi masa shuru.
Har akayi sati biyu bata san abinda ya faru ba zuwa lokacin abubuwan amfanin su na gida sun soma karewa sannan gashi tana shirin komawa makaranta dan Monday mai zuwa zasu koma hutu ya kare, ranar lahadi din nan suka je gidan Anty wuni, Anty sai kallon ummee take taga kirjinta ya cika gashi tayi fari sosai, tayi shuru bata furta abinda yake ranta ba saida laila ta shigo dakin tana cewa "Anty don Allah kibani hamsin na siyo awara gidan yarlugga" Anty tace "awara dai ta zama miki jaraba ga abinci bakici se awara duba kan madubi na ajiye dari dazu ki kawo min canji" ummee tace "idan kin siyo ki kawo naji idan da dadi" Anty tayi dariya tace "siyo na darin duka to dan gaskiya ta iya awara" laila ta fita da sauri tana murna babu dadewa ta dawo da awaran a plate ta zauba gaban ummee tana cewa "yaya ummee gashi" tashi zaune tayi tasaka hannunta a tare suka cinye shi ya mata dadi tayi shuru sai tacewa laila "kin iya wainan fulawa"? Laila tace "sosaima ai da ba a sati banyiba Anty ta hana" Anty ta dago daga gyaran Farcen da take tace "ba dole na hana ba yarinya ta soma ramewa bata cin abinci sai kayan kwadayi" ummee tayi dariya tace "wallahi anty tun jiya abin nan shine araina to ban taba yi ba ina gudun nayi na kwabe lamarin" Anty tace "sai laila tayi miki yanzu kiga yadda akeyi kushiga kitchen din tare" bayan sallar magrib suna cikin soyawa sadeeq ya shigo yana cewa "me kukeyi hakane" laila tace "wainan fulawa" tsaki yayi yana cewa "duk duniya babu wanda yayi kwadayin mata wallahi" ummee tace "aiku inda maitar taku take daban ne ba a kayan ciye-ciye ba" harararta yayi dan ya gane me take nufi ya shiga cikin gidan.
Abinci yaci yana cewa ummee ta taso su tafi jabir ze sauke su gida, daki anty ta janyeta tabata leda tana cewa "tunda sauri kuke idan kinje gida ki duba" ta karba cike da kunya tana godiya dan ita a tunaninta irin kayan matan nan ne ita yanxu ma ta daina amfani dasu dan lamarin sadeeq ya soma isarta.
Suna zuwa gida wardrobe ta bude ta ajiye ledar inda babu kaya tana cewa "wannan katuwar ledar ai sedai nayi kyauta da kayan" shirin bacci kawai sukayi ranka ya dade da yakejin kamar yanzu aka kawo masa amarya ya sake tara mata gajiya, washe gari da ciwon kai ta tashi amma bata fada masa ba tayi shirin fita makaranta ameera tazo daukarta, dubu daya data rage masa ya mika mata da sukaje din ma basuyi lectures ba shabiyu ameera taga ita gata tayi nauyi dan tashiga watan haihuwa ga ummee na fama da zazzabi dole suka dawo gida ta sauketa itama ta wuce.
Tunda ta kwanta har laasar bata tashiba dan wasa-wasa akayi azahar bata ma sani ba, sai laasar din ne tayi kokarin tashi tayi salla tareda wanka ko zataji karfin jikinta, tasha pcm ta shiga kitchen tayi shirin hada jollof na shinkafa kawai ruwan na fara tafasa ta soma amai da sauri ta kashe gas ta rufe tukunyar amai kawai tayi ta sake langabewa sadeeq kuwa sai bayan ishai ya dawo duk hankalinsa ya tashi ganinta a haka ya sake daukar pcm ya bata tasha kafin safiya koda gari ya waye lafiya lau ta tashi kamar ba itace kamar bazatayi ba jiya.
Batayi niyyar zuwa makaranta ba dama tayi kwanciyar ta. Dayake ita abincin bai dameta ba dan ko girki yanzu daga ta dora take fara amai sai sadeeq yace ta dainayi ranar Friday ta shirya yakaita asibiti wurin jabir, amma ranar sai ya tashi bashida ko nera hamsin yace ta bari har Monday a haka kuma babu wani abu da zasu dafa mai dadi suci duk baya cikin tsarinta, yanzu da garin Allah ya waye ta soma zazzabi kenan sai azahar yake sauka kafin Monday ta gama galabaita acikin gida ga yunwa ga ciwo.
Koda Monday tayi shi kanshi bashida lafiya saboda ranar ma komai babu agidan sannan lahadi ma dayayi gangancin fita da kafa ya dawo, ranar kuwa jikinta ya dada yin tsanani dan batayi bacci ba bazatace ga abinda yake damunta ba kawai saita fashe da kuka.
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.