*Safiyyah galadanchi**JAJIRTACCEABUBAKARSADEEQ*
*SHAFI NA ASHIRIN DA TARA*
Tunani ta ringayi ta hanyar da zata bullo masa ta kasa samun hanya guda data dace sai ta dauki wayarta ta kira Anty saida suka gaisa sannan tace "Anty dama wannan ledar da kika bani ne ban bude ba sai dazu naga abinda yake ciki" Anty tayi murmushi tace "Ai ko zuwan da kukayi inata kasa kunne naji kin yi maganar bakiyimin ba nayi mamaki" hakuri ta bata tana cewa "kinsan tun ranar da muka dawo din nan ne banda lafiya, amma Anty meyasa sadeeq ya ajiye wannan abubuwa masu muhimmanci yana wahalar da rayuwarsa"? Sautin muryar anty kadai zai nuna maka irin jin haushi da takaicin dake cikin ranta tace "bazan baki labarin duka ba amma kece zaki taimakeshi saboda hanyar da yake kai ba daidai bane nayi tunanin tun a satin farko daya fara wahalar dawainiyar kula da gidansa zai nemi takardunsa amma naga bashida niyyar yin haka, matsala ya samu da dan uwansa har takai ga ya goranta masa akan karatun daya kaishi waje shiyasa yayi watsi da takardun da niyyar ya koma yayi wani karatun amma bai samu dama ba dan haka ya ajiye lallashi babu kalar da bamuyi ba yaki ya sauraremu har da barazanar bar mana gida yayi to yanzu ummee wannan yakin naki ne saboda ya saba dake kece zaki dawo dashi kan hanyar data dace ya daina wannan haukar dayake yi" Ajiyar zuciyar ummee ta sauke tana cewa "Amma anty ta yaya"? Anty ta danyi shuru tana jin nauyin maganar da zata fada tace "zan baki satar amsa guda biyu zuwa uku, na farko ko kadan bana zargin sadeeq da neman mata dan haka na tabbatar ba mazinaci bane zan iya cewa kece mace ta farko bayan ya aureki saidai yanada karfin shaawa irin yadda ya saba dake yanzu bazai iya hakuri yadda yayi abaya ba saboda yanzu ne ya last zumar yanzu ne ya dandana yaji dan haka satar amsar da zan baki shine ki kula dashi yanzu, ki daina kula dashi wani lokacin sannan ki guje shi" daga haka tayi mata sallama ummee tayi shuru tana saka maganar anty tana warwarewa daga baya ta dauki wayarta ta sake kira amma wannan karon Aisha kawarta ta kira suka gaisa tana cewa "maman Ahmed yakike dan Allah tambaya gareni" Aisha tayi dariya tace "na barmiki ahmad din zan haifo babyna mai kamadani" dariya suka yi a tare sannan ummee tace "idan kinada matsala da mijinki sai aka baki shawara ta gefen dayakeda weakness kamar ace kullum baya iya hakuri sai ya kusance ki idan kina alada baya iya hakurin kwana biyar ko shida sai akace ki kula dashi yanzu sannan ki daina kula dashi wani lokaci sannan ki guje shi me hakan yake nufi" Aisha tayi shuru sai can tace "daga bakin manya kikaji maganar nan"? Ta amsa mata da eh sai tayi dariya tace "nima kaina ya daure amma abinda na fahimta tunda bangarene na shimfida tsakaninki dashi ko tsakanin mata da mijin shine ta sakar masa jiki yayita murza son ranshi ya kara sabawa da ita ta bashi gudunmawa a fagen ta nuna masa so da kauna na dan wani lokaci idan bai gyara matsalar ba sai ta daina kulawa dashi kinga kenan ya saba yanzu kuma bazai iya hakuri ba to idan ta daina din ma bai canza ba sai tai masa yaji ta bar masa gidan mataki uku kenan idan bai canza ba sai a samo wata hanyar amma ina tausayawa wanda aka danawa wannan tarkon" ta karasa maganar tana dariya murmushi ummee tayi tana tunanin yadda zata kaya tsakaninsu dan ita ko kadan bata kaunar abin a yanzu kila saboda cikin nan ne zatayi magana ya shigo dakin tayiwa aisha sallama ta ajiye wayar tareda nufar inda yake ta karbi ledar dake hannunshi ta ajiye tana cewa "sannu da zuwa" ya gyada kai yana cewa "mekikeyi inata kwankwasa kofa baki ji ba" ta rike masa hannu tace "waya nakeyi, zo kayi wanka" yabi bayanta yana cewa "kinci abinci"? Ta girgiza kai tace "inci in sake kwanciya? Gara yunwa akan lafiyata ta tabu kaima kasan daga nayi kuskuren cin wani abu yanzu zancen zai sauya" shuru yayi mata yana mamakinta bakin kofa suka tsaya ta tayashi ya cire kayan jikinshi ta hada ruwan wankan sannan ta jashi ciki yayi zaton fita zatayi sai yaga ta fara wanke shi shuru yayi har ta gama suka fito saida yayi shirin bacci sannan tace "zaka sha tea? kasan bana girki dan banson warin dahuwa" yace "zansha amma fisabilillahi ummee har yaushe zan ringa shan tea" batayi masa magana ba ta fita daga dakin, ranar yaga kauna da so wadda bai taba tunani ba har bayan asuba saida ya nemi kari duk da karfin jikinta ya ragu amma bata hanashi ba ta shirya ya rakata ta wuce makaranta anjima kadan ta kirashi ya aiki haka ta ringa binshi har ta dawo amma karfin hali kawai take dan kwana biyu banda ruwa babu abinda take ci, fridge ta bude sai taga robar freshmilk a ledar daya shigo da ita jiya hakanan taji tanaso tasha ta zuba a karamin cup ta kwankwada kafin dare ta shanye duka sai murna take harda cewa idan ta fita skul zata siyo da yawa.
Amma ranar batayi bacci ba kwana tayi tana amai har saida aka sa mata ruwa washe gari sannan ta samu sassari, tun daga ranar ta sake zage Dantse wajen kula dashi nan take ya dawo da jikinshi dan kayan abinci ma batareda saninsa ba ta siyo, idan zatayi girki saita toshe hancinta, sanin irin kulawar da yake samu ya saka shi daina fita da wuri sannan koda za ayi sallar magrib yana gida ba karamar wahala take sha ba amma ta nace saboda tana so ta cika wannan buri da alkawarin data dauka.Yau koda ya dawo tana kwance a palo daga ita sai under skirt wai zafi take ji babu wuta tace masa "wai a haka zamuyi azumi cikin wannan uban zafin"? Ya zauna gefenta yana cewa "ba dole ba amma ai kekam bazaki yi azumi ba" ta zaro ido tana cewa "gaskiya zanyi ko banyi ba menake ci ai gara insan nayi azumin yafi min" kwantawa yayi ya dora kansa jikinta ta fara shafa kanshi tana cewa "ka gaji sosai ko? Ya kamata kayi wanka, yauwa sadeeq meyasa baka fada min kayi karatu ba har masters"? Ya rike hannunta yana cewa "saboda fada miki din bashi da amfani" yatsanta ya saka a bakinshi yana tsotsa ta sunkuya daidai kunnenshi tace "dan Allah kayi hakuri koma menene kayi amfani da karatunka kaga dai muna wahala" cire yatsan yayi yana cewa "turo ki akayi"? Ta girgiza kai tana cewa "Anty dai na tambaya ta bani labarin kayi karatu dan nace mata ta rarrasheka ko degree kayi" ya gyada kai yana cewa "to kibar maganar nan" dariya tayi tace "shine future dinka fa sadeeq dan Allah kabari anema maka aiki" kokarin tashi yake daga jikinta ta danneshi ta dora bakinta kan nashi tana magana "nasan ba karamin abu zai saka ka ajiye qualifications naka kazo kana yawon wahala ba amma dan Allah koma menene kayi hakuri Allah ma muna masa laifi mu rokeshi kuma ya yafe mana idan bazaka yi saboda da kanka ba ko saboda ne kayi saboda Allah da kuma abinda yake cikina karyazo duniya yana wuni da yunwa wata rana ka..." cikin tsawa yace "ki daina shiga abinda bai shafeki ba na fada miki" daga haka ya mike ya shige dakinsa harda rufo kofa karfi tabi kofar dakin da kallo a fili ta furta "lokacin da zan dauki mataki na biyu yayi indai kai baza a yi magana ta fahimta dakai ba ai idan kasan wata baka san wata ba" zamanta tayi a palon har aka dawo da wuta ta zauna tana kallo sai shabiyun dare ta shiga dakinta da niyyar wanka.
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.