*Safiyyah Galadanchi*
*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*
*shafi na goma sha uku*
Ameera ta zauna gefen gadon dakin tana cewa "kefa wata rana tunanin ba irin na mutane bane, kinga ba a shaidun dan Adam amma sadeeq Sam beyi kamada koda barawo ba balle abinda kikeso ki fada abinda nake nufi da yana boye miki wani Abu shine Kalar sanaar dayake inaga ba karama bace tunda duk kin San sauran sannan babu wacce takai yasiya koda Rabin kayan nan ne Dan haka ki bincikesa koda cikin dabara ne" ummee ta Dan taka kafarta kadan sannan ta zauna tana cewa "zai iya yin haka saboda yanada matukar son sirri da zuciya" Ameera ta sake cewa "wanene habeeb da naji ance tare suka zo da uncles dinsa wurin Neman auren nan"? Ummee ta daga idonta sama tana tunani sai ta tabe baki tace "ni wallahi bansan shiba nadai san sadeeq daga shi sai laila ne awurin mamansu kuma bansan mamansu tanada kishiya ba" Ameera tayi murmushi tana cewa "banaji ajikina akwai talauci gidan da zakiyi aure ummee hakanan nakejin hankalina ya kwanta da family dinsa, kinga matan da suka kawo kayan nan"? Ummee tace "ni ina zan gansu ba kun boyeni adaki ba sekace wasu kauyawa" dariya Ameera tayi tace "Anty Safiya Ce tasan halinki kar inbarki ki fito" ta bata rai tana cewa "ai ita antyn nan kullum haka take" tana rufe bakinta aka turo kofar kawarta ce Aisha da alamar ranta a bace yake tace "ni zan wuce Fatima" ummee ta janyota dakin ta rufe kofar tana cewa "wallahi babu inda zaki sena ganki tukunna" Ameera datasan Aisha din saboda shirin da suke da ummee a islamiya suka hadu yarinyar tana da kirki sosai batada hayaniya suna level 1 akayi mata aure da Dan uwanta, ba masu arziki bane asali ma a gidan wan babanta take Dan mahaifinta ya rasu tun tana primary se mamanta tayi wani aure shine yayan babanta ya hadata aure da babban danshi kuma basa son juna da aure amma duk suka hakura, tana kuma fadawa ummee matsalolinta dashi idan da taimakon da zata iyayi musu sai tayi har mijin ma yasan ummee.
Ameera tace "fushi fa take tunda tazo baki bi takanta ba kuma nayi nayi da ita ko ruwa taki tasha" zaro ido tayi tana kallon Aishan tace "pls besty Dan kira rakkiya ko a wayane ta kawo mata abinci kala hudu ko Biyar ta zaba Wanda zataci" Ameera tafita daga dakin tana cewa "dole kuwa" ummee ta maida idonta kan Aisha tace "meye haka naga kin rame" murmushi Aisha tayi tace "babu komai wallahi Fatima" "kin tabbatar babu komai? Naga kinyi wani iri ji kashin wuyanki se kirji kamar zai fasa riga" taja mayafinta da sauri tana rufewa tace "hakanan Nima naga kamar ajikina su Kadai suke girma" dariya ummee tayi tana cewa "lallai lecturern ki na basu kulawa dakyau" tana rufe bakinta ameera ta dawo dauke d tray da abinci da ruwa duk akai ummee ta mike da sauri ta kama mata tace "to Aisha wanne zakici kuma ki jira ni zan maidake gida" Aisha ta girgiza kai tace "koda naci amai zanyi" sai a lokacin ummee ta lura da Dan cikinta daya soma fitowa tace "laaaa matarnan bakida mutunci wallahi shine baki fada min ba" Aisha tayi murmushi tace "wallahi tunda akasan da cikin a kwance nake ina ciwo se ran alhamis aka sallameni daga asibiti ma shiyasa wayar ma banbi takanta ba seda na dawo gida" Ummee ta kalleta cike da tausayi tace Allah ya rabaku lafiya amma kici dambun insha Allah bazakiyi amai ba tunda bazaki zauna da yunwa ba sedai karkici wannan tarkacen na sama" haka ko tayi taci kusan Rabi tasha ruwa tacewa ummee "kinsan rabona da abinci tun jiya da rana da Yaya Abba yayi kamar zai dakeni naci tuwon da mama ta aiko" ummee ta bata rai tace "har yanzu shidai be iya lallashi ba ko"? Aisha ta tabe baki tace " har mari seda nasha ina da wannan ciwon saboda za a samin ruwa naki tsayawa saida bakina yayi jini" ameera ta tamke fuska tace "kekuma duk kina tsaye? Maza wasu basuda hankali ya dirka miki ciki kina wahala da cikin kuma ya dakeki" Aisha tayi murmushi mai ciwo tace "sanin yayi bayan Allah banida gatan daya wuce su da ace ina tareda iyayena da yanzu na tafiyata to inda Umma take aure mijin baya yadda ko sati muyi a gidan wai kishi yake da abbanmu" dariya ummee tayi tace "Allah ya kyauta" hira sosai sukayi sannan suka koma cikin kawayen Mommy ta aiko musu dakayan a daki tace su raba a tsakaninsu ummee tana kallo suka raba batasa bakinta ba dukansu seda suka cika kwali bibbiyu da ruwa carton guda da drinks bayan magrib duk suka watse Aisha Kawai da ameera suka rage bayan isha ameera tace "bari inwuce kinsan Ahmad zaizo yau" ummee ta dauko mayafinta tana cewa "muje ma daganan se in wuce da Aisha gida" fitowa sukayi ummee tasa wani daga cikin security ya sawa ameera Nata kayan amota ameera tayi shuru tana kallonta Dan kayan batasan adadinsu ba aishama kowanne kwali biyu ta hada mata sannan ta kalli ameera tace "zamu hadu gobe a makaranta ai" Ameera tace "Eh amma inaga nidai gobe se 10 zan Shiga Dan gaskiya yau na gaji" ummee ta gyada kai tana kokarin Shiga mota tace "Dama na fada miki ai Dr.AD funtua yayi covering ai so ba lecture 8" ta karasa Shiga motar.Tana fitowa gate Kiran sadeeq na shigowa wayarta kafin tabar layin, parking tayi sannan ta daga yace "ina zakije a Daren nan" ta kalli bayanta tana hangoshi tayi murmushi tace "zoka kaimu inda zamu tunda ka fito" tayi reverse tana karasawa kusa dashi" fitowa sukayi Aisha ta dawo baya shikuma ya Shiga ummee ta zauna a gaba ya daure fuska tamau kamar bai taba dariya ba. Ummee tayi mamaki amma taji sauki daya gaisa da Aisha lafiya har suka Isa ummee tace "Aisha kishiga da kayan amma Dan Allah ki kara hakuri mai hakuri koda yaushe shine Asama kuma abin na Dan lokaci ne duk zai daina kinji" Aisha tayi murmushi tace "babu komai ai dole zan cigaba da hakuri kuma babu Dama inda ake zama ace babu sabani" ummee tayi murmushi tana cewa "saida safe kawata".
Suna juyowa ya kalleta yace "kin kusa zama matar sadeeq" tayi dariya tana kallonshi cike da kauna tace "me kakeci na baka na zuba"? Yayi saurin bata amsa yana cewa "so da kaunarki nake ci suna zuba sultana" ya kalli cikin idonta tayi saurin dauke nata saboda abinda tagani cikin idonsa a hankali yace "meye haka se kace kinga dodo"? Ta yamutsa fuska tace " idonka wani iri ko kwalli ka Shafa" yasaka yatsunsa a hankali ya dalli lips dinta yace "kwalli sekace Dan daudu"? Ta rike baki tace "zan kira Anty in fada mata ka fara dukana" yayi dariya wacce ke nuna akwai farin ciki atareda maiyinta yace "zata fada miki dukan kauna da so ne" tayi dariya tana saka chewing gum a bakinta ya mika mata hannunsa yana cewa "bani abinda kika sa abakin ki" tana murmushi tace "mezakayi dashi"? ya harareta yace "zaki bani ko Yaya"? Cirowa tayi ta mika masa tana jira taga mai zaiyi dashi setaga yasa abakinshi yana taunawa a hankali tace "kazami" yayi murmushi yana cewa "bakiga komai ba indai wannan ne kazanta" suna isowa gida ta kalleshi kamar zata hada fuskarta da tashi tace "Nagode" ya daga gira sama alamar dame "tace da kake sona sultan" ya Shafa kumatunsa yana murmushi yace "abinda ya kamata nayi ne banyiba kikeyi sultana" ta goge hawayen idonta tace "Dan Allah karka juyamin baya za ayi mana dariya zaka karya min zuciya" wani irin tausayinta yaji ya kama shi wallahi yanaji babu Kalmar da zata iya fassara irin son dayakewa ummee har baisan lokacin da ya Dora hannunsa kan fuskarta ba yana share mata hawaye...
*idai inason soyayyar sadeeq da ummee*
*fiyyah na gaisheku*
*jini yafi ruwa kauri*
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.