JJT 7

17 1 0
                                    

*Safiyyah Galadanchi*

*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*

*shafi na bakwai*

"Dan Allah mana sultan ka rage min kalaman nan in fada kwatanta fada maka irinsu inaso kaji irin yanayin da nake ciki a yanzu wallahi ji nake kamar mu dawwama a haka, muryarka kamar karka daina magana" ya gyara kwanciyarsa yanajin dukkan gabobin jikinsa suna sake yadda da soyayyar da ya JAJIRCE akan ta da kuma ita kanta wacce aka dauki soyayyar kacokam aka mikawa kamar da gangana saiya sake karkace muryar ta yadda yakeda tabbacin hakan zai kara dulmiyar dasu kogin kauna yace "haba dai sultana muryata ko kadan batayi koda Rabin zaqin taki ba, wallahi idan kikayi magana inaji tamkar muryarki ta kasance abincina na safe har zuwa dare kuma hakan yacigaba da maimaituwa har ranar da za a shafe babina a duniya, muryarki batada kama sultana" tayi dariya kadan tsabar farin ciki dajin dadi ya saka ta rasa abin cewa sai daga baya ta tsinci kanta da fadar "um'um sultan banda zagi" ta wani bangaren tanaso ne taji yadda zai ci gaba da yabonta hakan yana yi mata dadi "dole nayi yabo awurin wadda yabon ya dace dominta, idan na zageki na tafka babbar asara kar Allah ya nunamin wannan ranar" ta sauke numfashi tana cewa "gobe inada lecture karfe takwas" yayi murmushi mai sauti yace "ki kwanta sultana ki kuma yimin uzuri ki tafi makarantar nan da kanki" ta bata rai tace "kai nake so ka kaini" da gaske idan harshi ya kaita makarantar tanaji tamkar ita wata sarauniyace kuma hakan yana kara mata karfin gwiwa wajen mayar da hankalinta ga abinda ya kaita makarantar, ya dan sauke numfashi alamar wannan yar rigimar baisan ya zaiyi da ita ba yace "Kinsan me ummee wani Abu nake shirya miki ba bazata idan har kikace na kaiki makaranta to kin tauyeni zaikuma shafi aikin dan Allah mana kiyi kokari ki tafi da kanki" ta sake shigewa bargo saboda sanyin Ac tace "to shikenan Allah ya kaimu ya bada sa'a" ya amsa da ameen ya Dora da cewa "ki kula da hanyar nan banda tuki irin na ganin dama pls" ta gyada masa kai kamar yana ganinta zatayi magana sai taji wayar ta yanke a tunaninta katin wayarsa ne ya kare sai tabi bayan kiran amma sai ake tabbatar mata da cewar wayar a kashe a fili ta furta "chajin ya kare kenan" tayi karamin tsaki tana gyara kwanciyarta a hankali ta shiga tunanin yanzu fa yana can zafi ya isheshi tunda babu wuta ya cire rigar jikinsa ya bude windows ga sauro tunda taga windows din gidansu ba irin na zamani bane wayanda ake budewa ne kamar kofa ga karafuna saboda security a jikin waccen kofar da ake turawa tanada glass babu net dinda zai hana sauro shigowa a hankali ta mike tsaye ta kashe Ac dake dakin dama bata kunna fanka ba ta bude windows a hankali ta furta "banaso naji dadin da ba tareda kai ba Sadeeq soyayyarka koda yaushe tana karuwa tareda tausayinka Allah yayi mana zabi na alkhairi idan har anfi karfinmu Allah ya bawa zuciyarmu karfin dauka" ta kuma amsa da ameen sannan ta dawo ta kwanta, saboda rashin sabo sai ta ringa baccin tana farkawa har gari ya waye, salla tayi bayan tayi wanka tayi shirinta sannan ta fito a Palo ta hadu da Momy tana magana a waya tace "ahh dama yau a makarantar ne Ummee? Dako har ina cewa zamuje walima tareda ke" zama tayi gefenta tana cewa "ohhh Auren Salima ko? Kinsan Momy na manta kuma wallahi tanada kirki sosai har iv ta turamin ta WhatsApp last week karfe nawa ne walimar" Momy ta kalleta tace "karfe uku suka sa acan gidan kawunta saidai unguwarce batada dadin zuwa"  tayi murmushi tace "zan fito karfe uku da Rabi Momy sai inzo Malam tsalha ya kaimu ai akace dai rana tsawo ce yakamata muje din naga suna tsayawa akan dukkan hidimar gidan nan" Momy tabita da kallo lokacin da take Barin palon wallahi tana son yarinyar nan gaba daya babu inda ta baro halin uwarta tanada matukar sanyin hali da dadin zama Sam batada girman kai akan abinda mahaifinta ya Tara ta tabbatar da wata ce irin wayan nan bukukuwan tafi karfin ta halarcesu a fili ta furta "Allah ya albarkaci rayuwarki".

Karfe uku da Rabi ta mike tsaye ta karasa kusa da lecturer din yana ganin girman ta saboda yadda take girmamashi gaidashi tayi ya amsa yana murmushi yace "yar gidan Danmadina ya akayi" itama murmushi tayi tace "akwai wani issue ne a gida zan fita tareda mama karfe uku naga uku da Rabi yanzu shine nake Neman alfarma saboda Allah ko zan samu abani dama na tafi" ya girgiza kai yana cewa "nabaki Fadimatu Allah yayi miki albarka" ta amsa da ameen adduar tana yi mata dadi babban mutum ne zai girmi dady sai take ganinsa tamkar mahaifinta kobashiba babu Wanda zaice tataba yi masa rashin kunya acikin malaman akwai malamanda sun san mahaifinta yafi karfin duk zuriasu amma idan tazo letti sai suyi kokarin kunyatata saboda sugani ko zatayi amfani da damar ta rama amma ko kadan saidai Indan sun hanata fita ta juya takoma ko kallon banza bata yi musu badan kuma batajin zafin hakan ba saidan tana girmama Kalmomin zaman lafiya da gamawa lafiya.

Tana fita lecturer din ya kalli sauran yan ajin ya cire madubin idonsa ya kallesu yace "kunga yarinyar nan?" Suka amsa da eh ya sake cewa "wallahi banaji a makarantar nan akwai dalibin da mahaifinsa yakeda koda Rabin abinda mahaifinta yake da shine bayan haka kuma ita kadai ce mace a wurinsa yana nuna mata soyayya fiye da tunaninku amma batada girman kai ko dagawa, a hirar da nayi da ita na fahimci ita takeson karatu a wannan makarantar da yanzu saidai kuji sunanta badai ganinta ba wallahi da inada da namiji Wanda ya Isa aure zan iya Neman alfarma awurinta ta aureshi ina muradin hada Jini da ita kuma sanin hakan da tayi bata taba kin karatu ba. Bata taba cin grade kasa da B ba ku kasance masu kwaikwayo da irin halayyarta. Nan take ajin ya rude da surutu masu fadin alkhairi da akasin haka.

Duk wunin ranar basu samu yin waya da sadeeq ba duk ta damu har saida dare shima basu wani dade ba saboda a gajiye yake Kansa na masa ciwo.

Ranar asabar da safe sha daya dawowarta kenan daga ilamiya da take zuwa karfe takwas ta gyara kwanciya zatayi bacci taji hayaniya a wajen gidansu bude window tayi ta leka ta hango duka yayyenta maza tareda Daddy dama yace mata yakusa dawowa tayi murmushi cike da farin cikin ganinsa ta saita dauki hijab dinta ta fita waje yana hada ido da ita yayi murmushi daya tsaya iya labbansa ta gaidashi ya amsa kamar yadda yakewa sauran sai taji jikinta yayi sanyi ba haka ya saba yi mata ba sau dayawa baya jin kunyar rungumeta agaban kowaye duk girman ta amma wannan karon ko kanta bai Shafa ba, hakanan taji gabanta yana faduwa ta fara karanto duk addua tareda maimaita Kalmar innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un sannan tabi bayansu har babban palonsa na sama mommy ma yayi mata dawowar bazata dan haka ta shiga hada-hadar hada masa abinci tareda sauran ma'aikatan gidan zama yayi yaci yana kallon yadda ummee ta makure gefe tayi shuru da alama tunani take.

Bayan ya kammala ya kalli Momy da sauran yayansa yace "yaushe aka sa date din auren su Haidar?" Momy tace "akwai sauran wata hudu ai daddy kasan ita juwairiyya matar haidar tana Spain saita dawo daga makaranta ana sa ranar wata uku suka rage ta dawo" ya gyada kai ya kalli ummee yace "ko kunyar nuna wannan kazamin bakyayi a matsayin saurayinki kalli ko yan uwanki da suke maza sun nemo mata a gidan daraja ke kinje kin kwaso wani bagidaje wai a aura miki" ta kalli cikin idonsa tana jin yadda yawun bakinta suka bushe a hankali ta sauke idonta kasa yace "lukman ka taba zuwa kacemin kanason ummee da aure ko" lukman ya washe hakori ummee ta watsowa lukman wani irin kallo numfashinta na wani kai kawo tana jiran babanta ya fadi ajalinta.

"Ka shiga cikin manemanta nayi maka alkawarin idan har ta yadda zan hadaku aure" shuru taji na dan wani lokaci a hankali kuma saita durkusa gaban Daddy tace "Daddy wallahi zance ya koma makaranta zance yayi karatu nasan zai yadda sannan insha Allah zai yi kudi daddy amma dan Allah karka hadani aure da lukman wallahi bana sonshi"

Daddy ya kalli sauran yaran yace "kubincika min yaron nan idan baya Shaye-shaye Kodai ya fara bawa ummee ne ji wata hauka da takeyi, malama tashi kibar nan kafin nayi miki abinda ni kaina bazan so shiba"

A hankali ta mike ta fita, ikon Allah kadai ya kaita dakinta nan take kanta ya soma ciwo ko karyawa batayiba a wurin baccin wahala ya dauketa.

*Jini yafi ruwa kauri*

*Fiyyah na gaishe ku*

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now