*Safiyyah Galadanchi*
*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*
*shafi na biyar*
Kafadarta ta makale masa tana cewa "nidai seka zauna gida ka huta duk kalli yadda ka rame"
"Ummee kinada son rigima dole gobe zan fita akwai wani aiki danake so nayi goben dan haka zama bai ganoni ba" tace to "kayimin alkawarin zaka dawo da wuri" ya gyada mata kai yace "insha Allah amaryata" bude motar ta tayi ta shiga tana yi masa bye bye.Bai Dade da shiga gidanba Abba ya dawo shima dakin Anty ya samesu zama yayi yace "ki kawo min abincina nan" ta mike tsaye tana cewa "nayi zaton wanka zaka farayi ai", karamin tsaki yayi yace "kekam baki Barin wauta" fita tayi tana cewa "kai kuma kullum da sabon salonka inda tambaya nayi kuma kace nayi wauta ko yaushe zan girma a wurinka"? Maida kallonsa yayi wurin Abubakar yace "nayita jiran ka can cikin gari baka zo ba" "dama na fadawa Anty sai bayan azahar zan dawo kuma aikin ma danaje bamu kammala shiba" ya gyada kansa yace "yayi kyau, sai maganar ka da Habeeb" sauke numfashi yayi yace "Abbah idan kunada ra'ayin hakan banida damuwa na fadawa Anty ko dazu Ku dubi girman Allah Ku barni nan babu abinda zai gagara da yardar Allah" cike da fushi Abba yace "menene amfanin wannan muguwar hallayyar taka sadeeq bana sonta wallahi na tsani kafiya da taurin kai har yaushe za a zauna kullum ana maimaita magana daya kai kafi kowa zuciya ne wallahi ka guji matakin da zan dauka akanka, kuma daga yau ka tabbatar babu wata alaka tsakaninka da yar gidan Danmadina" ajiye plate din hannunsa yayi yace "amma kuma ai Abba na fada maka Sonta nake da kuma aure" "shi kuma ubanta baya sonka da yarsa, ya nanata maka bazai bawa dangin talakawa matsiyata fakirai yarsa ba, to kai wane irin maye ne da bazaka rabu da ita ba" sadeeq ya karkace kai ya sake cewa "Abba nifa mahaifinta bashi nakeso ba bana bukatar ya soni ni ita nakeso kunsan kuwa ko shekara nawa muna tare rana daya ace za a rabamu Abba wallahi konace maka zan iya rabuwa da ita karya nake maka" Anty ta tsaya daga bakin kofa dauke da tray din abincin Abba tace "wannan maganar yakamata kabarta har kaci abinci, kai kuma Abubakar sai yaushe zakayi hankalin da za a saka ka Abu kayi ko kuma za a hanaka ka hanu? Koda yaushe ana nuna maka hanya kana kaucewa yarinyar nan ince ba ita kadai ce mace a garin nan ba" ya maida kallonsa gareta yace "amma Anty idan akace So ai ya shafe komai ni na fada muku duk yarinyar da zata aure ni idan ba ummee ba wahala kawai zatayi" dukansu shuru sukayi sadeeq dayaga haka sai kawai ya tashi ya fita daga dakin direct adaidaita sahunsa ya ja ya fita Neman halak, Anty ta kalli Abba tace "ina baka shawara dan Allah ka dauka ka zubawa sarautar Allah ido ka kuma yiwa yaran nan Addua, Allah ne kadai baiyi zaka hadu da yarinyar nan ba yau wallahi zuwa tayi ta zauna tana min kuka na tausaya mata tunda har mukaga sunyi haka kamata yayi mu kyale su mu kuma yi musu addua" cin abincinsa ya farayi yana cewa "bazan kyaleshi ba yaron dana Haifa yana janyowa ana zuwa ana wulakantani sai kace ubanta ke dauke da nauyinmu bayan ban taba zuwa kofar gidan uban kowa maula ba sannan wallahi yaron nan mu muka haifeshi bai Isa yace bamu da ikon sakashi ko hanashi ba zai hadu da Bacin raina mafi muni wallahi" "babu kyau raba masoya manzon Allah ya hane mu dayin haka akwai hadisi ingantacce dayace idan mace da namiji suka hadu suna son juna to ayi musu aure idan kuma aka rabasu to za a haifar da barna mai girma bayan kasa barna mafi muni" kallonta yayi yace "shi ubanta baisan da haka bane" tace "to ai ko yasani ya taka sanin sannan bai kamata kai ka biye masa ba ina tsoron abinda yaran nan zasu iya aikatawa idan aka hanasu" shuru yayi yana nazari daga baya yace "Allah ya shiryesu ya shige mana gaba wallahi abubuwan yaron nan sun soma isata gaba daya yabi ya takura rayuwarsa" anty tace "ameen abinda na fada masa kenan dazu kuma ni duk wannan wahalar da yake bansan ina kudin da yake samowa suke tafiya ba"
Abba yace "ai sadeeq bai iya almubazzaranci da kudi ba kijira kuma ki ga abin mamakin da zai sake bullo miki dashi" murmushi kawai tayi bata sake magana ba.Bayan magrib sai ya wuce gidan abokinsa Jabir daga waje ya tsaya ya kira wayarsa, yana fitowa ya kalleshi cike da tausayi yace "shigo da adaidaita sahunka sai mu shiga ciki" baiyi musu ba mai gadi ya bude masa gate ya shiga, cikin gidan yajashi suka Shiga yarinyar jabir guda daya ilham tazo ta makale masa tana ta bashi labari dakyar jabir yace "jeki cewa ummanki ta kawowa uncle abinci da ruwa" sadeeq ya kalleshi yace "nifa a koshe nake" karamin tsaki jabir yayi yace "bazaka daina wannan banzan halin naka ba, ya ake ciki ne wai" sadeeq ya dage gira yace "komai yana nan yadda yake jabir babu abinda ya sauya mai wuyarma tsanani nake ganin yana karawa dazu Abba kamar zai dakeni" dafa kafadarshi jabir yayi yace "nidai shawarar da zan baka shine akan habeeb ka ajiye waccen maganar gefe don Allah sannan ka samu wata yarinya kayi aure ko zaka dawo yadda kake da ji yadda ka karame inyaso ummee din idan hankali ya kwanta sai kayi kara da ita" kallon mamaki sadeeq yayi masa yace "da kuruciyata in auri mata biyu? Kai nifa ko arayuwata babu raayin mace biyu zanjira ummee koda babanta bazai yadda ba har sai munyi furfura nidai ita nakeso ita kadai kuma sauran mata duk kallon maza nake musu" jabir ya harareshi yace "meyasa kakeda wannan kafiya newai, tsakani da Allah ji yadda kake wahala wallahi kasan kafi karfin Jan adaidaita sahu a garin nan kafi karfin duk abinda kakeyi amma duk saboda taurin kai irin naka bazaka barsu ba" sadeeq yayi murmushi yace "nafi jin dadin rayuwata a haka jabir ni nake fita nema insamo ba kyauta ake bani ba bawanine yayimin hanyar da zan samu ba ballanta ayimin gori banaso harka ta kudi ace sai naje neman alfarma wurin wani wata rana har a goranta min haka shiyasa na kudurta araina zan JAJIRCE akan duk abinda nakeso sai dai idan ya kasance ba rabona bane Abu biyu zasu rabani da ummee ko ayi mata aure kokuma mutuwa wannan nasan dole zata sa na hakura" Jabir ya sauke numfashi yace "Allah yayi maka sassauci Sadeeq wallahi ina tausaya maka Abubuwa sunyi maka yawa" murmushi kawai yayi ya mike tsaye yace "bari na wuce dama kalambaina zani inaso yau karfe goma na wuce gida" tsaki yayi yace "wahalalle meye na komawa gida da wuri bakada mai ko baka abinci abaki ta duba irin gajiyar da kayi tayi maka tausa" yayi dariya mai sauti yace "duk ummee tayimin alkawarin hakan harda abubuwan da yake sirrine tsakaninmu" jabir ya bi bayanshi yana cewa "bakuda hankali Ku duka"
Karfe goma da Rabi ya dawo gida har sai shadaya ya kwanta bayan yayi wanka daganan yayi kiran ummee suka sha soyayyar su.
*Jini yafi ruwa kauri*
*FIYYAH NA GAISHEKU*
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.