*Safiyyah Galadanch*
*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*
*shafi na shida*
Washe gari bayan ta dawo daga gidansu Ameera tana zaune a daki wayarta tayi ringing dagawa tayi saboda gain numbern daddynta "ummee saboda ina Nuna miki abinda yafi dacewa dake shiyasa zaki fito da sabon salon rashin kunya, zanyi tafiya for 3wks amma ki kasa fitowa muyi sallama ni zakiyi fushi dani har ki kashe waya bayan haka kuma nazo sau daya ki dauki waya ki kira bakiyi ba, kin kara saka mini tsanar yaron nan saboda shi kika fara zubar da irin tarbiyar da kika samu to zan dauki mataki akan hakan" jikinta yayi sanyi a hankali tace "Daddy kayi hakuri bazan sake ba" tsaki yayi yace "sory for your self" ya kashe wayar kallon wayar take tana tunanin mafita wani bangare na zuciyarta yace "ki rabu da sadeeq din nan shine kwamciyar hankalinki, amma saita runtse idonta a fili tace ranar da duk na rabu dashi na tabbatar ranar itace ajalina" ciwon kai taji ya sameta ta kwanta shuru saita tuna da alkawarin da tayiwa laila a hankali ta mike tsaye ta saka hijab dinta tare da daukar key da handbag ta fita mall dinda ke kusa dasu ta shiga ta size dinda take tunanin zaiyi mata ta siyo ta kashe kudi zasukai 80k awurin kamar mai hada lefe harda wasu kananan hijabs masu kyau ta siya mata da pants da turaruka, kofar gidan ta Isa ta bude motar ta kwaso kaya sannan ta nufi cikin gidan Da sallama Anty kadai ce a gidan laila ta tafi islamiya, Anty ta kalleta cike da mamaki tana amsa sallamarta tace "lafiya lau ummee daga ina" zama tayi kan kujerar robar dake tsakar gidan tana cewa "wallahi Anty daga shago nake harna kwanta saina tuna da alkawarin danayiwa laila yau shine na fita ba siyo mata" Anty ta girgiza kai tana cewa "wane irin alkawarine wannan ummee" cewa tayi "Anty bari in bude miki kigani naci Sa'a Inaga kayan yau dinnan ma aka budesu sunada kyau" saita koma kan tabarma ta zube kayan tana nunamata anty ta rike baki tace "ummee wannan sai kace zata bude shago? Kuma girma take yanzu ai nan gaba sai duk suyi mata kadan wannan Abu haka duk na mutum daya aiko a lefe ta samu irin haka ta godewa Allah" murmushi tayi tana cewa "idan sun mata kadan anty sai ta bayar kyauta ga wasu yan uwa sai a sake siyan wasu" Anty ta girgiza kai tana cewa "amma dai ummee asan irin yadda ake kashe kudi wannan Abu yayi yawa" murmushi kawai tayi ta tashi tsaye tace "Anty bari na wuce agajiye nake yau" Anty ta gyada kai tana cewa "Allah ya hutar da gajiya" ta amsa da ameen.
Da dare tayi ta kiran Daddy bai daga ba alamar har lokacin fushi yake da ita, ta kalli Momy ta bata rai tace "har yanzu fa Momy bai daga ba" Momy ta kalleta tace dauki wayata ki kira shi sannan ina baki shawara a zaman da zaiyi can ki nuna masa yadda yakeso hakan za a yi ba dan kina nufin hakan da gaske ba nasan duk Inda yake yana tareda damuwa akan lamarinki kuma tunanin Neman mafita zai hanashi yin abinda yaje yi kinga ko ansamu cikas a wannan bangaren bazanso hakan ya kasance ba" gyada mata kai tayi sannan ta kara wayar a kunnenta Daddy kuwa bugu daya ya daga yana cewa "sweetheart ayimin uzuri duk yau sau daya nakira" ummee tayi murmushi da bashida sauti sannan tace "Daddy kayi fushi dani inata kiranka inbaka hakuri baka daukaba" yayi shuru yana bata rai ta bangarensa ta sake cewa "Daddy kayi hakuri tunda bakason sadeeq bazan sake kula shi ba" tana furta hakan kuka yazo mata ta danneshi amma dukda haka saida muryarta tayi rawa Daddy ya sauke ajiyar zuciya badan ya yadda ba koda karya takeyi kokuma uwarta ce ta shirya mata ta fada masa haka to zaiyi mata uzuri saboda tayi masa biyayya yace "shikenan zuwa next week zan dawo saboda a yau dinnan ma kawai na kammala abinda nazo yi anan" ta gyada masa kai kamar yana ganinta tace "Nagode Daddy" murmushi yayi yana mata sallama.
Bayan ya ajiye wayar ya gyara zamansa a fili yace "dole zan dauki mataki idan na koma Barin ummee haka a garin can tareda yaron nan bazai taba bari hankalina ya kwanta ba saina tabbatar nayi abinda zai rabasu rabuwa ta har a bada".
Bayan komawar ummee part dinta ta kwanta babu dadewa wayarta tayi ringing tana dubawa taga sunan sadeeq yadda tayi saving Sultan(king👑❤) har zata daga saita tuna da maganar data gama yi da Daddy yanzu har ta yanke bata daga ba, sake kira akayi ta dauka tana kara wayar a kunnenta tareda yin sallama ya amsa tareda cewa "Nayi zaton Kinyi bacci Allah yasa ban tashe kiba" tayi kirkiro murmushi mai Sauti tace "bayan bamu saba yin haka ba? Dole ne zanji muryarka kafin in kwanta baccin kasani" ya gyara kwanciyarsa yana cewa "wannan gaskiya ne ya gida ya aiki, Anty tace inmiki godiya kinyiwa laila hidima" tayi murmushi tace "ai yiwa kaine, idan ban tayaku Kare mutuncin laila ba ai kaina nayiwa sharri yadda take zuwa makaranta tana yawo acikin mazan nan haka hankalina bai kwanta ba" ya danyi shuru amma murmushi yake Wanda ya saka duka hakoransa suka bayyana yace "ai itama rashin kunya ne kuma inaji Anty tana yawan yi mata fada saidai tana da kafiya" "ai fada bayayi shi kadai sai an hada da dabaru tunda wata kila ita bata tunanin akwai illa ga hakan yanzu dai bazata kawo wani amuzuriba tunda anyi maganin hakan" ya gyada mata kai yana cewa "amma ummee kayan sunyi yawa" tayi saurin katseshi tana cewa "babu ruwan mutum dan Allah" yayi dariya mai sauti sannan yace "to bari in kwanta saboda wayar ba caji kuma babu wuta" ta yamutsa fuska tana jin wani dandano Mara dadi daga zuciyarta ita a wurin ta bakomai bane dan ta dauki Abu ta bashi amma tun kafin yayi complain akan wayarshi data samu matsala kwanaki ta gwada bashi kyautar daya daga cikin wayoyinta yaki karba, "to idan har kafi karfin kyautar wayar Dana baka ka dubi girman Allah ka siya wata menene amfanin wayar da bata awa biyu babu chaji ita ba android ba daga kira sai radio" sautin da muryarta ta sauya kadai ya fallasa tarin da tulin takaicin da taji saboda kin karbar wayar da yayi a nashi bangaren kuma zai iya cewa yana masifar son wayar data bashi sai dai akwai abinda bata saniba tabo akayiwa zuciyar sa wanda baya tunanin nan kusa a rayuwarsa tabon nan zai shafe duk wani Abu da wani zai dauka ya bashi da sunan kyauta yana matukar tsoronsa saboda gudun tarihi ya maimaita kansa hakan zai iya sakawa zuciyarsa ta tarwaste saboda tayi raunin da bazata iya daukar makamancin tarihi na farko ba sai yayi murmushi yace "zan siya wata ummee idan Allah ya yadda amma bazan karbi wayarki ba duka wayoyinki suna kara mini sonki da kaunarki ganinsu kawai da nakeyi a hannunki, suna kara miki kyau tamkar su wani adone ga kwalliyarki, yadda kike rikesu a tsakanin yatsunki yana kara fitar musu da wata ma'ana wayayinki tamkar wani sirrin adone a gareki dan haka ko daya bazan karba" zata iya rantsuwa da Allah tunda take a rayuwa bata taba jin murya mai dadi irin tashi ba, muryarshi tanada girma sai akayi mata ado da wata murya kamar wanda yayi mura bai gama warkewa sautinta baiyi amo mai karfi ba idan yana magana sai kiji tamkar a kunnenki ana sosa miki shi, ta tabbatar da asaman ruwa take yau tabbas kalamansa zasu nutsar da ita saita ringaji kamar gadon da take kai yana juyawa a hankali tace...
*Jini yafi ruwa kauri*
*FIYYAH NA GAISHE KU*
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.