JJT 34

13 0 0
                                    

*SAFIYYA GALADANCHI*

*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*

*SHAFINATALATINDA HUDU*

Ummee ta dan kalli gefen sadeeq tana jira taga ya dauki wayarshi dan ta tura masa sako taga bai daga ba saita yi masa flashing ya duba wayar yaga itace ga sako tareda miss call dubawa yayi ya kalleta suka hada ido ya girgiza mata kai ta dan marairaice fuska sai yayi saurin dauke idonsa daga gefenta.
Anty ta leko tana cewa "Habeeb kuje inji Abbanku yana magana"  mikewa sukayi a tare suka fita, lokacin laila ta shigo da plate da robar yaji ta ajiye ta koma kitchen ta dauko kula data zuba wainan fulawan aciki ta ajiye musu sannan taja yaran dakinta suci tare.

Ummee duk bata cikin walwala dan gida take son komawa kar suyi zargin wani abu dakyar ta daure taci wainan suna dan hira da ummu tace "duk plan dina babu ciki yanzu wallahi naso sainan da shekara uku ko zan sake haihuwa" ummee tahi murmushi tace "ai gara kiyi da wuri ki huta" ummu ta girgiza kai tana cewa "badan karna tsorataki ba dana dan baki labari akan yadda nake wahala" dariya ummee tayi tace "Aida zan tsorata da tuni na cire tsarin haihuwa a rayuwata dan ummata  wajen haihuwa ta rasu, Allah dai ya rabamu lafiya da cikin" ummu ta amsa da ameen ta dora da "ya akayi kika shawo kan wannan kanin namu" murmushi ummee tayi tace "tafiyata nayi fa har yanzu ban koma gidan ba jiya ne yaje ya sameni gida yacemin ya amince amma koni na wahala" "dama ance duk iya shegen namiji mace na iya gyara shi ya saba da kwasar gara kin gudu ai dole ya sauko" ummu ta fada da sauri ummee ta toshe baki tana dariya tace "ahh wannan lamari sai ku aimu har yanzu saurayi da budurwa ne" tana fadin maganar yaji ya sarketa ta fara tari.

Abba yaji dadi sosai yadda yaji labarin sadeeq ya hakura yaringa sanya musu albarka yana nuna jin dadinsa sai yace "ina yar matarka baiwar Allah dakaina zanje in dawo da ita" sadeeq ya sauke kanshi kasa yana jin kunya, sallamar ummu ta saka Abba dagowa yana amsawa ta kalli habeeb tace "ummee ce take ta sheka amai daga tari to naga aman yaki tsayawa" a tare suka mike suka fito tana nan kwance palon ta amayo abincin karin da suka ciyo da wainan fulawa gaba daya batada karfi da sauri sadeeq ya isa inda take ya dagota ya rungumeta yana ta jera mata sannu, Anty tace "ta wanke bakinta ta kwanta intayi bacci insha Allahu zata tashi lafiya lau" kasa mikewa tayi tsaye saida anty ta riketa duk ransu babu dadi saida suka ga tayi bacci.

Habeeb yace "zafa a kwaso kayanku daga gidan can ya matse wallahi" sadeeq ya gyada kai dan bayason musu ko kadan da habeeb yanzu yace "babu matsala yadda kakeso haka za ayi nan gaba sai na gyara shi dan gaskiya bana ji zan iya siyar dashi" habeeb yace "zaka iya bada shi haya amma saidai ka raba shi biyu gaskiya dan mutum daya bazai iya kamawa ba" yana magana yana danna waya yaci gaba da cewa "idan ta samu sauki sai kuje ta kwashe kayan sawanta da naka zan saka su iliya da faruku suzo su kwashe kai kuma jibi tare zamuje Abuja"
Saida gabansa ya fadi danshi gaskiya baya son abinda zai raba shi da ummee. sai yamma ummee ta farka tadanji sauki tacewa anty zataje gida zuwa dare idan ta hada kayanta" Anty ta rungumeta tana samata albarka sannan ta bata kayan data siya mata na salla tace "ba a dai dinka ba keda ummu na siyawa sai ki dinka yanzu kisamu na rainon ciki" durkusawa tayi tana godiya ta fita da sauri dan bataso sadeeq ya dawo ya sameta gidan.

Momy taji dadin ganinta sosai ta zauna tana fada mata labarin abubuwan da daddy ya sanar da ita jiya tace yau da dare ma yace zaije har gida ya roki gafarar mahaifin sadeeq, momy tace "ainayi zaton kin tafi kenan" ta girgiza kai tana cewa "A'a yanzu ma kayana nazo zan dauka" momy tace "kije zan saka a kawo miki su har gidan" godiya tayi ma momy ta sake yi mata nasiha sannan ta hada mata kayan gyaran jiki tace ta tafi can gidanta da su ta fara"

Koda driver ya maida ita gidan sadeeq ya cika da takaicinta kamar zai fashe dan a tunaninsa dady zai iya hanata dawowa ko ishai bai bari sunyi gidanba ya kwasheta suka tafi, kafin su isa duk ta wahala dan saida ya tsaya ya siya abubuwan bukata tunda ta dade bata gidan, rai a bace ta shiga gidan ta godewa Allah gidan fes yake dan kamar tana gidan haka yake gyarashi kullun, wanka ta shiga tayi ko mai bata shafa ba ta nemi wuri ta kwanta, shikuma yana kitchen yana kokarin dafa musu indomie dan yaga alamar ta gaji bayan haka kuma kamar jiraye take dashi, har daki ya biyota da indomie din tana jin kamshin ta toshe hanci tace "don Allah ka fita dashi" yayi saurin juyawa palo ya ajiye ya dawo ya riketa dan yaga tana yunkurin amai yana shafa bayanta har ta dawo daidai, yace "me zakici to? Dama haka yake miki duk wannan lokacin" ta girgiza mai kai tace "dama bana cin indomie amma na kwana biyu banyi irin haka ba" cike da tausayinta yace "me zaki iya ci yanzu"? Ta kwantar da kanta a kirjinsa tace "bana son komai inda dai akwai kunu da zansha" kwantar da ita yayi yace "to jirani" ya fita daga dakin tana nan kwance taji ya bude gate ya fita yakai awa daya sai gashi ya shigo da cup yana fifita kunun ta tashi zaune tana cewa "ina ka samo kunu a wannan daren" ya kai cup din bakinta yana cewa "gidan yaya habeeb ummu ta dama miki koda naje ma wallahi har sun kwanta nace ta bani gumban amma tayi karfin hali ta dama miki" saida ta shanye shi duka tace "ina sauran" yace "yana kitchen acikin flask na ajiye miki" ta gyada kai har zata kwanta ta rike masa hannu tace "indomie din fa kaci" ya girgiza kai yana cewa "yanzu zanci" ta bata rai "yayi sanyi ai yanzu bari na toshe hancina in dafa maka  wani" yayi murmushi yace "karki damu sweetheart zanci wannan yunwa nake ji kuma ga gajiya bayan haka kuma kinsan ba lafiya gareki ba" rufa mata bargo yayi ya fita dakyar yaci rabin indomie dinnan yaje yayi wanka yazo ya kwanta gefenta duk a zatonsa tayi bacci sai yaji ta dawo jikinsa gaba daya tana shafa kanshi tace "nayi missing bacci irin haka a jikinka" ya sake riketa yana cewa "mezan samu a daren nan" ta tura furkarta gefen wuyanshi tace "bacci dan Allah mu huta da safe duk abinda kake so I will be ready insha Allah" kissing gefen kumatunta yayi yana karanto musu adduar bacci, kusan shekara hudu zuwa biyar rabon dayaji rayuwarsa irin haka babu wata damuwa lallai ya tabbatar da aure rahama ne dace da matar kirki arziki ne Allah ya barshi da ummeenshi.






JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now