*Safiyyah Galadanchi*
*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*
*shafi nagoma sha tara*
Bawani shiri da take illa na gyaran jikinta sai na kayan da zata saka, ameera kawarta sai Aisha da suke cikin system din sunsan abubuwan dake gyara jiki ciki da waje.
A bangaren mommy ma tana iya kokarinta a lokacin ne ta kara tabbatar da rashi na mahaifiya kawai tayi amma batayi rashin uwa ba dawowa tayi dakin Momy da zama lokacin duk Inda Momy tayi a gidan nan suna tare sai idan Daddy yana nan ne basa kwana daki daya."Kin kuwa je kin duba kayan nan kinga ko akwai abinda babu"? Momy ta tambayi ummee "Momy kayan nan ai inaga babu abinda babu aciki abin mamaki Daddy harda standing fan ya siya min sunkai guda goma sha biyar harda rechargeable fan" Momy tace "Ac fa?Dan cewa yayi duk abinda babu induba a fada masa, sannan kin tambayeshi daki nawa ne a gidan"? Ummee ta girgiza kai tace "nifa duk Daddy ya haukata min shi kwanakin nan fa wata rana sai dare yake kirana sannan nakai Sati ban ganshiba amma zan kirashi yanzu" Momy tace "Ai bansan menene ya shiga kan Daddy akanki ba ummee sai kace Wanda aka shiga aka fita Dan araba Ku ni banga aibun sadeeq ba da zai yanke wannan hukuncin babu alamar kauyanci ko jahilci a tare dashi" "ummm kuma fa Momy wallahi yayi boko fa dandai bayason zancen ne" ummee ta fada tana gyara zamanta gefen gadon, mommy tayi murmushi tace "ai dole kiji kuma namiji duk iskancin shi idan aka yi dace sekiga mace ta gyara shi tsaf, yanzu dai ko zaki ban layinshi nayi magana dashi"? Wayar momy ummee ta dauko ta rubuta lambarshi ta bawa mommy, ringing biyu wayar tayi sadeeq ya daga da sallama yana jin muryarta ya gane ya gaisheta sosai ta amsa tana murmushi tace "zamu turo ne gyaran daki zuwa jibi ran jumu'a babu matsala ko"? Yana daga tsaye saida yakai zaune ya kalli cikin gidan komai yayi iya kokarinsa saura masa fenti amma ko dubu uku beda duk dangi ya bata dasu saboda kafiyar dayakewa su Abba yaki jin magana Dan haka duk gudunmawar da aka kawo se ace abawa Anty ko Abba, yauma wajen gidan yake gyara plaster akewa bangon wajen gidan tareda karawa ginin tsayi, ya kakaro murmushi yace "babu laifi Momy Allah ya kaimu jumua din" taji wani sanyi aranta ta sake cewa "to sadeeq sai maganar daki nawa ne Dan mu dauko kaya daidai gidan" yayi kasa dakai yana jin kunyar fada mata Dan a ganinshi ko daki goma ne bazasuga kokarinshi ba dakyar yace "daki hudu ne Momy sai Palo uku da" ta gyada kai tace "masha Allahu sadeeq, gobe idan Allah ya kaimu zanzo kaina ingani, ka gaishemin da mamanka kuma ka fada mata zancen da mukayi dakai yanzu" ya amsa da to.
Kallon ummee tayi tace "kinji gidan wai daki hudu ne da Palo uku" ta zaro ido tace "hudu mommy"? Mommy tace "kinsan yanada gida ko gidan haya ne" ummee ta danyi shuru tace "bai taba cemin yana gini ba amma kuma nasan ba gidan haya bane" Momy tace "to Allah yasa" ameen ummee ta amsa.Yana kashe wayar yabar yaran a gidan bayan ya wanke kafafuwansa yafita gida ya wuce ya samu Anty zaune a daki ga wasu kudi a gefenta zama yayi ya gaisheta ta amsa tana cewa "daga ina haka kamar wanda aka koro"? Ya kalleta yace "Anty daga gidansu ummee ne Momy ta kirani a waya" saida gaban Anty ya fadi ta maida hankali gareshi tace "se aka yi Yaya" ya Sosa kai yace "zasu zo gyaran daki ran jumua tace gobe zata zo ganin gidan kuma Anty ko fenti ba a yi ba" tabe baki tayi tace "to me kazo in maka illa ka tashi kaje ka nemi masu fentin suje su fara" ya Sosa kai yace "jira kawai suke in kirasu tun satincan muka gama magana amma Anty kudin ne babu wallahi" gyara zamanta tayi tace "dauki ga wayan nan Dana gama hadawa kaje a fara Inda suka tsaya a tsayanan seka fadamin inji ya za'ayi" murmushi yayi ya dauko kudin yana kallonta yace "Anty nagode Allah yabar mini ke yanuna mini ranar da zan faranta miki da arziki na" murmushi itama tayi tace "ameen saika hanzarta ko kuma ayi Wanda zasu yaba" fita yayi yana kiran waya yaje dakanshi tareda masu fentin aka siya Wanda zai Isa har waje da bakin gate ya kalli kudin har lokacin da sauran kudin, idan yakoma ze tambayeta nawa ne Dan gaskiya kudin sunyi albarka.
Basu samu gama fentinba saboda dare yayi sai washe gari da safe yazo gidan tareda Abba da Anty da laila.
Anty tace "amma da ka shafa mata wallpaper din nan a Palo da bangon corridor zaifi kyau" yana tafiya yace "ai duk jiya an siya yau idan sun karasa fenti za a saka" Abba ya gyada kai yace "masha Allah gidan kyaunshi sai kara fitowa yake gaskiya kayi kokari" murmushi yayi yana Sosa kanshi. Laila tace "Yaya ina dakina" yana dariya ya nuna mata dakin mai gadi yace "harda toilet aciki" ta kalli Abba tana bata rai kamar zatayi kuka tace "Abba dakin mai gadi" yace "kyaleshi kema mijinki zai miki gidanki Wanda yafi wannan haduwa ma" ta boye fuskarta ajikin Anty.
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.