28

565 53 2
                                    

Bafa kwa Voting da comment ko dai labarin babu daɗi ne.

Washe gari da wuri Faruk yazo dan suje asibitin, kasancewar tun jiyan ta sanar da Hajiya ita kuma Hajiyar ta ce su tafi da Aisha ko Sadija duk da cewar an ɗaura musu aure anma tunda ba kowa ya sani ba kamar mutan unguwa tafiya da ɗaya daga cikin nasu zaiyi kyau.

Tsaf suka shirya duk su biyun sun yi kyau, duk da kasancewar sadija ƙarama anma kyanta ya gama fitowa dan tafi Ummu kyau sai dai kawai ummu ta fita kwarjini.

Yana tsaye jikin motar sa, ya zubawa ƙofar gidan nasu idanu hannayen sa harɗe kan ƙirjinsa yayi kyau sosai kana ganinsa kaga angon.

Kamar kuwa Ummu da sajida sun san ya tsure ƙofar gidan nasu da idanu, Ummu ce ta fara fitowa karaf suka haɗa idanu ya sakar mata murmushi yayin da ita ma ta mai da masa, a ɓaɗi ni kuma godewa Allah tayi domin tasan in da badan ikon sa ba babu abin da zai kawo faruk ya ce yana sonta har ya iya auren ta..

Ta ko ina ya mata zarra, wani zubin har tunani take ko me yasa yake son ta, in ta rasa amsa ta ce ikon Allah kawai.

Shi gashi mai kuɗi, ɗan mai kuɗi, kuma ɗangata me illimi, ga kyau wanda ko da ace iya shi kaɗai yake da shi da yawan ƴan mata zasu soshi.

Ita kuwa gata marainiya, cikin marayun ma mara gata, ba illimi ne da ita ba gashi ba wani kyaune da ita ba, hasalima duhun fatar ta yasa take ƙara mamakin yadda yake sonta kuma so na gaske, eh mana na gaske tunda har zai iya aurenta.

Yadda ta sani shine matasa munana ma marasa gatan faruk basa son bakar mace bare irin sa.

Ɗan hura mata fuska yayi, ganin tunanin nata yaɗan yi zurfi Mr Faruk tunanin me ake ne haka.

Murmunshin da bata san ta iya shi ba ta sakar masa, yayin da ya sandare a tsaye ransa cike da abubuwa, ko yaushe da komai na yarinyar birgeshi yake, yanzu sai ya ji inama inama....

Samun kansa yayi da cewa wai yaushe zaki tare ne, murmushi tayi sai na yaye Muhammad.

A tsorace ya ce what, kina hauka ne?, dariya tasa ta dan zagaye shi ta shiga cikin motar muje ko ta ce dan taga sadija tun ɗazu zaune a baya. Lokacin da tai nisa cikin tunani sajidar ta shiga.

Ɗan langaɓar da kai yayi ya kalleta, gami da girgiza kai, kafin ya zagaya ya shiga shima daga bisani yaja motar.

Ɗan ruko hannun ta yayi, yanzu ke bakisan Genotype dinki ba?, ya tambaya, kalar tausayi tayi oh ni sau nawa zan ce maka ban sani ba, nadai san ba sikila ba ce may be As, da hanzari yace ina ke AA ce, dariya tayi yadda yayin ya bata dariya shi kuwa sauya topic din yayi zuwa wani

Wai tunanin me kike ɗazun?, ya tambaya cike da kulawa, kallon sa tayi kafin ta ce kai dai bari kawai zuciya ta ce ta dinga faɗamin yanzu ya zanyi inda matsala a gwajin, nidai inason ka anma fa inason ƴaƴan da zan haifa.

A tsorace ya kalle ta me kike nufi?, nasan ka fahinta anma bari in ma bayani dalla-dalla, ina nufin in da wani abun sai ka turo ka amshi kayan ka afasa.

Banza yayi mata yama ƙure radion motar, yayin da ita kuma ta guntse dariya yana kallon ta haushi ya cikashi bai dai ce komai ba har suka isa asibitin Muhammad wase wato Nasarawa.

Da sauri ya fice ita da sajida suka rufa masa baya, ɗan gaba tayi ta riƙo hannunsa, haba nawan Mijin Ummu bama haka da kai, mene na fishin?, ai ni da kai mutu ka raba.

Juyowa yayi yana murmushi haba ko da naji da kina wani batun rabuwa ana zaune ƙalau, murmushi mai kashe jiki ta sakar nasa wanda duk yadda Umarancin ya tashi in ta masa yakan manta da shi din Umar ne dan Usman yake komawa.

Office ɗin Abokin sa Umar suka nufa, cike yake da Marasa lafiya dan haka baima yunƙurin shiga ba, kawai gefe suka samu suka zauna kafin ya fara neman Number ɗin Umar ɗin.

Bugu guda ya ɗaga, yawwa mun iso ya za'ai kenan?, Faruk ya tambaya ok ku jira am busy zan aiko wanda zai kai ku lab ɗin, umar ya faɗa daga ɗaya ɓangaren ok kawai Faruk ya ce ya katse kiran.

Zaune suke suna hira Ummu da tsokana ta ciyota sai ta rafka tagumi, hankalin sa ne ya tashi wannan kuma na mene lafiya?.

Kai dai bari kawai nawan ayyana yadda zan ji nake in muka rabu, wai ke me ke damun ki ne?, ba nace banason maganar ba.

Yo to banda abinka ai dole ce, tunda kuwa kai kaja da tun farko anzo anyi gwajin nan da inma rabuwar ce da tuni mun manta da juna.

Allah Ummu hani ranki zai ɓaci, dariya ta guntse wato Umarancin ya tashi ta faɗa aranta, dan duk da cewar ba Umar ake ce masa ba Faruk ne amma yakan taɓa faɗan su Umar ɗin, abinka da masu iya magana da suka ce suna linzami tabbas ta yadda haka ne kan Faruk ɗin ta.

In dai kaji ya ce Ummu hani to faɗan ya tashi, dan Ummu yake cewa wataran hani.

Dariyar da ta ƙunshe ƙara ƙona masa rai tayi, wato daman ba sona kike ba ko.

Kallon sa tai a shagwaɓance tayaya zan ce bana sonka, kawai dai nafison future ɗin yarana, tsaki yayi to kuwa sai inga mai sawa in sake kin, dariya tasa aiko dole ne, ni kaga ma da takarda ta nake tafe sai mu ari biro gun Yaya Umar tsaki ya saki sai kuma kiyi, gami da miƙewa sabida zuwan yaron da zai kaisu lab ɗin.

Guntse dariya tayi in da ta miƙe su ka bi bayansa.

Sai dai yadda yake ta kumbura yasa ta kasa jurewa dariyar sai da ta fito fili a hasale ya ce wannan wane irin rashin mutunci ne zakizo kina ta wani yiwa mazan waje murmushi.

Hannun ta ta haɗe ayi haƙuri yallabai bazan kuma ba, kima kuma ɗin ya faɗa bata ce komai ba sai murmushi da tayi.

A lab ɗin an gwada su, sunyi jiran kusan awa biyu kafin komai ya haɗu faruk ya rasa me ke masa daɗi, daga ya zauna sai ya miƙe ya koma ya buga tagumi in ya kuma tuno wani abin sai ya miƙe zunbur.

Sajida tun abin na bata dariya har ya koma bata tausayi, ta koma iyiwa yayar tata faɗa kan ta dena masa dariya.

Don't forget to follow

Ummu HaniWhere stories live. Discover now