Takaicin duniya ya ishi Ummu, ta rasa me yasa ta kasa danasanin zuwan ta, gashi kuma ta kasa yin farin cikin zuwan, kawai dai gata nan gatanan ne shiko Alhaji Faruk zato yake bacci take, hannunta ya ruko inda ɗayan kuma ya ɗan shafa kanta, farin ciki ne fal aransa a zahiri kuma a hankula ya ce Allah ya biya ki, taya ni riƙon mutuncin ki da kikai, samun kanta tayi da cewa Amin aranta.
Bugun kofar ɓangaren nasu yasa shi tashi ya fita, yayin da Ummu ta bude idon ta ahankula takaicin duniya ya ishe ta, Allah dai yasa koma waye kar ya shigo ta samu ta rarrarafa ta tafi gida.
.Da alamu addu'ar ta bata karɓu ba dan kuwa muryar mace taji tana cewa Wallahi Faruk baka da kirki, wato shine kayiwa ƴar mutane fyaɗe ko, sosa kai yayi yana dariya, kai yaya mata ta ce fa, Allah ba inda zata ma ni ta tare.
Ware ido Ummu tayi ta yun ƙura zata tashi, itakam bazata zauna ba, baza'ai wannan abin kunyar da ita ba dan sabida ita ta kawo son miji duniya kawai sai ta kawo kanta tace ta tare, sai dai duk jarumtar ta sai da taji babu dadi.
Tsaki Farida tayi gami da shiga ɗakin ita ta taimakawa Ummu tayi ta mita dan me zata biyewa Faruk sai alokacin ta samu ta sa kuka.
Shigowa yayi haba Yaya dan Allah kawai sai kisa yarinya kuka, hararar sa tayi ya juya ya fice kan tayo kansa da masifa.
Ruƙo hannunta umnu tayi dan Allah Yayarmu karki faɗawa su Hajiya nama zo dan Allah.
Karki damu bazata sani ba, Faruk ya ce kasuwa zaki muje sai in sisiyo miki kayan in yaso sai in sauke ki, hakan kuwa ba karamin daɗi yayiwa Ummu ba.
Koda ta fito Faruk na tsaye yai saurin matsawa kusa da ita ya riƙo hannunta Please tawan kiyi haƙuri, watsa masa harara tayi, ta yi inda motar yaya Farida take.
Murmushi ya yi.
Shi komai tayi birgeshi take, bai ce komai ba ya koma cikin gida yayin da Farida taja motar suka fice.
Yadda ta faɗa ɗin haka ne ya faru, a mota tabar umnu ta fita ta siyo mata abinda ta ce danma Ummun tayi ta roƙonta karta ƙara kan abin da ta fada mata da siyayya sosai zata mata.
A gida ta sauke Ummu ɗin yayin da ummu ɗin ta aika aka amso mata makullin, Yaya Faridan ce ta sauke mata kayan sukai sallama ta tafi.
Bata jima ba aka aiko Khadija da Muhd yako sha kukansa ya more tausayin sa ya cikata.
Ta rungume shi a ƙirjinta tanajin ajiyar zuciyarsa, zataje ta roƙi malamin su Aisha gaskiya in dai zata fita ba tare da Muhd din ba gwanda Aishan ta tafi dashi makarantar, tunda yaƙi sabawa da maƙotan.
*********
Zaune take tun inda ta zauna tun shigiwar ta ta kasa tashi gyaran tattatasai take komai sai dai ta ce ƴan biyu su niƙo mata, inda akai sallama.
Amsawa tayi kafin ta juya dan gano me sallalar dan bata ɗauki murya ba.
Matashiya ce da ba zata wuce shekaru ashirin da biyar zuwa da shida ba.
Fara ce doguwa kyakkyawa sanye take cikin baƙin lesi mai adon golden,wanda ya dace da kalar Fatar ta da sauri ummu ta nuna ma Hasana kujera ta ce miƙo mata.
Sai da Matashiyar ta zauna tukunna suka gaisa da Ummu kafin kowa yayi shiru.
Kunin aya ummu ta ajiye mata
Mata shiyar ta ɗan kurɓa.
Tabbas kam yarinya ce, Matashiyar ta faɗa aranta yayin da take kissima shekarun Ummu tasan ta girmi Ummu ita a tunanin ta ma ta bata shekaru bakwai zuwa takwas, ta ce dole Faruk ya rikice yaga yarinya duk da yadda take jin irin son da Faruk kewa yarinyar tayi zaton zata ganta wata tsaleliyar Mace, sai taga Normal mace kawai.
Ummu ce ta katse mata tunani sai dai ban gane ki ba ko gun Hajiya kika zo?.
Murmushi tayi a'a gunki nazo ke ce Ummu hanin Faruk ko?, Matashiyar ta tambaya.
Eh ni ce ummu ta faɗa gami da faɗa ɗa murmunshin ta dan tayi zaton ko ƙanwar Faruk ce musanman ma ganin kalar su tazo ɗaya.
Sunana Fatima matashiyar ta faɗa ni tsohuwar budurwar mijin ki ce ko in ce dadiron sa.
Cike da mamaki Ummu ta kalleta, Dadiro kuma ba kece Fatimar Gidan Aminin baban su Faruk ba?, ya ban labarin ki amma ni bai faɗan wani aibu daga Tarayyar ku ba.
Murmunshin Fatiman tayi yo daman ta ina zai faɗa miki, nima da nazo in faɗa miki ne sabida abu guda wato kishi amma da na ganki sai tausayin ki ya kama ni baki can canci miji irin faruk ba.
Ɗaga mata Hannu ummu tayi koma dai mene yanzu shi ɗin miji nane kome yayi ya wuce ya kuma tuba.
Dariya Fatima tasa au daman ai haka zai ce miki bari kiga ta zaro wayar ta, ta ɗanyi danne danne ta miƙowa Ummu.
Wannan da kike gani jiya ya faru, kallo ɗaya Ummu tayi ta kautar da kai Domin yafi ƙarfin idon ta innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ta faɗa mijin ta da wata ba ita ba kiri kiri suna lalata tama kasa magana, ta kuma kasa miƙawa Fatima wayar.
Yayin da ita kuma Fatima ta zuba mata ido dan son gano me Yarin ke kullawa aranta.........
Last chapter da zanyi posting a watan nan, zan iya yakice wasu abubuwan in rubuta wasu in comments da vote suka birgeni.
Ya kuke ganin labarin shin Ya auren ummi da Faruk zai kasance?.
Kuna zaton itama ɗin moriyar ganga zai ci ko kuwa soyayyar gaskita ce?.
Shin zata haƙura ta tare bayan ganin sa wata daban a video suna lalala?.
Yanzu aka fara ku biyo ni.
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...