Mugani ya ce bayan ya riƙo ta, muryar Salma da suka ji tana faɗin eyye ah lallai masoya tana faɗi ne cikin dari ya sa da sauri Ummu hani ta ture hannun sa shiko bai damu ba yake faɗin badai kiji ciwo ba ko, turo baki tayi yo dana ji ciwo ai da kuka zaka ga nasa.
Ajiyar zuciya yayi ta wasa ah to Alhamdulillah har na fara tunanin kiran Umar muje asibiti, dariya Ummu hani ta yi kawai kafin ta koma ta zauna.
Shima ɗin guri ya samu ya yiwa kansa mazauni sai da ya zauna ɗin tukunna Ummu hani da Salma suka gai dashi.
Hajiya bata nan ne ya tambaya eh sunje unguwa ita da Khairat.
Mikewa Salma tayi bari in tafi tun kan afara korata da sauri Faruk ya ce da ko kin kyauta wallahi, eyye ƙawar tawa kake kora inji Ummu hani, kafin ya ce wani abu Salma ta ce ah ni bashi ya koreni ba ke ce naga kina ta harara ta alamar na takura muku.
Harara Ummu hani ta watsa mata kan ta ce wani abu Salma ta ce a'a kika kuma to kin jawo sai na faɗa masa.
Da sauri Faruk ya ce mene? faɗamin, dariya Salma ta yi ai ka bari kawai tunda nazo gidan nan magana ɗaya take min shine na yadda take sonka.
Daɗi ne ya cika Faruk ya wani washe baki zan bawa khairat Tukwicin ki ta baki ki gaida gida.
Eyye wato korata kake ko, Ummu tasa dariya bake kike goyon bayan sa ba.
Samun kansa yayi cikin Nishaɗi da kallon yadda Ummun ke dariya, dariyar da ya jima baiga tayi ba duk da sun koma Normal yanayin ta yana nuna masa da damuwa aranta sai dai yau daɗi ne ya cika shi yadda yagan ta cikin farin ciki.
Ai dole kiyi dariya tunda kun haɗu keda mijin ki kun kore ni zamu haɗune ta faɗa kafin ta wuce.
Aɗan kasalan ce Faruk ya dubi Ummu hani Ya akwai abin da zanci kuwa yunwa nake ji.
Ɗan kunbura fuska tayi wato so kake Umma ta ce na hanaka cin abincin ta ko, Ni kinga in rowar taki ce ta motsa kawai ki faɗan in miƙe in san nayi.
Murmushi tayi ni karka min sharri ta faɗa tana ƙoƙarin zaro kofi a kwando.
Sai da ta kuma ɗauraye kofin kafin ta zubo masa kunun tsamiya ne ban sani ba ko kana sha.
Hararar wasa ya watsa mata ina ludayi da sauri Hasana dake gefensa ta miƙo masa yawwa ta wajena, Usaina ta turo baki ni ta wajen Umma ce tana nufin Ummu hani, duk suka sa dariya.
Indai Faruk yazo gidan bazakai tsanmanin shi ɗin wani ne ba yadda yake maida kansa tamkar yaro yana biyewa yarintar ƙannen Ummu hani da ita kanta Ummun.
Yana shan kunun tana kallon sa yana ɗaya daga abinda yasa ta haƙura taji tana son zama dashi taji zata masa Addu'a Allah ya shirya shi, saboda yadda tun kusan farkon haɗuwar su bai taɓa nuna musu kyama ba.
A kullun in ta tuna da wani zuwan su shida Umar ta kawo musu ruwa da lemo Umar yana faɗin towo to ina ganin sai dai ni ɗin,aa dan mutumin naki kyankyami ne dashi kofin sa na gida ma shi yake wanke abin sa.
Karki damu karya yake ni inma zan kyankyami ai bazan kyankyanmin abin da nake so ba, mutumin da zaka aura mene na kyankyamin sa.
Tuna haka yasa ta Samun kanta da yin murmushi sai ji tayi yana faɗin kunun yayi daɗi nasan Hajiya ce tayi ko.
Kana shan abu me zafi kace Hajiya ce tayi bacin na ce ma tun safe ta fita.
To gaskiya wannan nasan Hasana ce tayi ya faɗa cike da zaulaya.
Ah wannan sedai Muhammad, ummu hani ta bashi amsa.
Ni fa ince ko da naji suka sa dariya.
Duban sa Ummu hani tayi bayan ya gama shan kunun ta ce yawwa kaga inata zuci zucin in faɗa ma.
Yadda tayi maganar ya gane yanzu da mahinmanci maganar da zata yi.
Inajin ki mene ne?.
Yawwa daman ɗazu muke magana da Salma ta ke faɗan Admission list ya fito ba ita, shi ne muke neman alfarma dan Allah ko zaka samu cikin waɗan da ka sani ka nema mata alfarma ko zata samu Admission ɗin.
Yanzu wannan ne yasa kike ta wani ƙasa da murya da sun sun da kai se kace wani babban abu na sha faɗa miki ko mene komai wuyar sa ki dinga tambaya ta kai tsaye.
Yanzu gobe ki amso takaddun ta zan bawa Abban su Umar insha Allahu zata samu musanman ma da yake ta ci komai ɗin ta.
Yadda take ta zuba godiya yasa Faruk miƙewa ni kinga bari in tafi.
**********
Fatima ce duk abin duniya ya isheta musanman da saƙonnin Mansur suka isheta ayanzu bata son Dad din ta yasan da Mansur ɗin yana son ta dan tasan zai iya roƙon ta alfarma ta haƙura ta auri Mansur ɗin.
Tun jiya take tunanin mafita bayan Dad din ta ya faɗa mata Alhajin su Faruk ya masa maganar yanaso zasu je suyi magana kan tarewar Faruk ɗin da ummu hani.
Ta rasa abinyi sai dai tanajin in dai har Faruk zai tare da wannan shegiyar yarin yar ita kam ita da shi ko alahira tasan zasuyi hannun riga ne, ita kuma dashi ta tsara rayuwar ta.
Zuciyar ta ce ta bata shawara tana kuma jin jaymar shawarar zata mata amfani.
Wayar ta da ke gefen gado ta sa hannu ta ɗauko Number ɗin Alhajin su Faruk ta danno kami da danna kira.
Bugu ɗaya ya ɗaga Fati na ya a kai ne ya faɗa Fatiman ta ce daman dan Allah Abba alfarma nake nema amma nafi son sai nazo kana gida ne.
A'a na fita anma yanzu zan dawo ki tawo kan kizo na dawo tom ta ce ta kashe.
A shirye ta ke Mayafi kawai ta yafa tayi bangaren Antin su.
A'a Fatin Dady unguwa za'a eh ta ce kafin ta ce zani gidan su Faruk ne.
A'a kaga kirjin biki ana bikin aminin ai dole kiyi ta zarya, haushi ne ya cika Fatiman kafin ta ce ni na wuce zan kira Dad in faɗa masa.
Ok tom ki gaidasu inji Antin ta faɗa tana maida kanta.
Alhajin su Faruk yana zaune a falon sa yana cin abinci Fatima ta same shi bayan sun gaisa ya ce itama ta zuba ta ce ita ta koshi lemon kawai tasha.
Inajin ki mene ne Alhajin ya faɗa.
Daman Na jima ina yiwa Dad Magana kan yayi maka magana inason Faruk anma ya ce tunda Faruk baya so na shi bazai masa auren dole ba.
Murmushi Abba yayi karki damu tunda ya zaɓi wadda yake so ɗin, kema zaɓin ki zan aura miki sai ku tare ku biyun keda wadda yake so ɗin.
Ran Fatima ba daɗi ba haka ta so ba anma dai dole ta hakura, ba kishiya a tsarin ta, sai dai akan Faruk ko ata huɗu ne zata je bare ta biyu.....
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...