shafi na bakwai

895 74 0
                                    

Ranta aɓa ce tai makarantar ƙannen nata, wanda take itama ɗaliba ce a cikin ta, mutuwar nan yasa dole ta haƙura da zuwa, duk da tanason karatun anman dole ta haƙura dan kula da ƙannenta.

Tana tafe tana mita aranta, dole in magananin yaran nan, dan ta fahinci tun mutuwar nan suka koyi rashin dawowa gida da wuri.

Ahanya ta gansu, Khairiyya ce ta ce lah, yaya aiko wata uwar harara ta watsa musu, ba tare da ta ce komai ba kawai ta juya suka bi bayan ta.

Tana shiga cikin gida ta juyo a fusace, ina kuka je eyyi? sukai tsuru suna kallon ta, ba tambayar ku nake ba ina kuka je?.

Yaya makaranta fa mukaje, inji Khairiyya, makarantar gidanku, Aisha tun ɗazun ta dawo, ta ce kuma an riga tashinku zaku, faɗan inda kuka je ko kuwa Ummu ta faɗa a zafafe.

Yaya wallahi makaranta mukaje, sajida ta faɗa, cikin karaji ta ce to daman na ce ba ita kuka je ba ina kuka biya.?

Daman ba yaya kairiyya ba ce ta tsaya hira, sajida ta faɗa cikin rawar murya ganin yadda taga yayar tasu ta tada hankalin ta.

Khairiyya ta kalla rai ɓace, wato kunga umma bata nan shi ne kuke san zama ƴaƴan kanku ko, to wallahi bazan laminta ba, in mutim nasan hira ya fara dawowa gida inga lokacin da aka tashe ku, in yaso in naga ya da ce sai in bar mutin yaje hirar.

Har ta shiga toilet tai wani tunani ta fito da hanzari tsaya waima da wa ta tsaya hirar? ta faɗa tana maida hankalinta ga Sajida.

Ita da ƴan ajinsu ne, sajida ta bada amsa.

Ajiyar zuciya Ummu hani ta saki, dan haƙiƙanin gaskiya tayi wani mummunar tunani ne, watakan kar dai da namiji ta tsaya, dan tana tsoron kar wani yai anfani da rashin gatansu ya cutar mata da ƴan uwa.

Zama tai sannan ta dube su baki ɗaya, bawai inasan takura muku ba ne a'a inaso ne kawai mu zamto yaran da su umma zasuyi alfaharin haifa, ku daure ku tayani kula da mutuncin mu, ni kaɗai bazan iya ba, ɗayanmu in ya lalace tamkar dukkanmu ne a idanun duniya, karkuyi zaton dan muna zaune haka mu kaɗai bazamu iya zamowa na gari ba, karku bari wani ko wata yai anfani da rashin galihunmu ya cutar daku kunji ko, suka ce to baki ɗaya, ta miƙe ta shiga wanka.

Sai da ta shafe jikin ta da mai sannan ta ma muhd wankan yanma ta shafe shi da mai ta goyawa sajida shi, kasan cewar bata salla ranar ɗaki ta shiga bayan ta rufe musu gidan, duk da mangari ba ce anman tana tsoron kar bacci ya rufeta su fi ce.

Batafi minti biyar da kwanciya ba bacci mai nauyi ya ɗauke ta, dan agajiye take sosai sabida tashin safe, tama su sajida abincin tafiya makaranta wani zubin kuma muhd sai yaita ihu da daddaren bata iya bacci sosai.

Aisha ce ta zubawa su Hasana tuwonsu da taga takwas tayi, suna gama ci sukai bacci ta ɗauki hasana taje ta kwantar ta dawo ta ɗauki usaina.

Hira suke tayi tsakanin su, ganin har goma ummu hani bata fito bane yasa A'isha taje ta tasota, dan tasam halinta sarai naƙin cin abinci.

Cikin bacci ummu hani ta ce dan Allah ki kyaleni Aisha na ƙoshi, cikin fishi Aisha ta ce wallahi yaya ki tashi, sai kinci, haba wannan wane irin abu ne, ina lura da ke rabonda ki wani ci abin kirki tun kan umma ta tarasu.

Kinga malama ki kyaleni cikin ki ko nawa na ce na ƙoshi ummu ta faɗa tana gyara kwanciyar ta

Hannu A'isha tasa ta ɗagota wallahi sai kin taso kin ci, haba ya kike son muyi kinzo kina kwana da yunwa, in cuta ta kamaki bamu da kuɗin magani, in kuma kika mutu ni yazanyi da sauran, gaskiya inke bakya bukatar lafiyar ki mu muna bukatarki.

Jiki a sanyaye ummu hani ta taso ta fito, idanunta a lumshe alamun bacci, kusa da Khairiyya ta zauna sajida ta miko mata kwanon abincin nata, tana ci tana bacci, in ya ɗan ɗauketa ɗaya cikin su ne zai ce yaya bakya ci fa, sai tai sauri tai loma kamar suyi dariya suka daure.

Sai da sukaga ta cinye suka miƙe sukai ɗaki Aisha da sajida da Khairiyya ɗaki ɗaya suke kwana, inda ita kuma ummu ke kwana da ƙananan dan in sun tashi rikici suke su Aisha kuma ba haƙuri.

Muhammad nata wutsul wutsul a katifarsa ta sameshi, ta ce kaga ɗan albarka wato an tashi kenan, tashin hana bacci, sai da ta fara bashi mama sannan ta goyashi jikin filo ta jingine a bango, sannan ta kwanta ganin yai luf duk da ba bacci yake ba.

Motsi kaɗan take buɗe ido, duk da gidan a kulle yake haka ɗakunan da suke dan tana tsoron kar wani ya shigo ya cutar dasu.

Kamar kullum tun bayan mutuwar ummansu yauma da wuri ta tashi, ta fara dumama tuwo sannan ta azama ƙannen nata ruwan wanka, shida da arba'in kamar kullum ta tashe su, Aisha na wanka, Khairiyya da Sajida na cin abinci duk dan tattalin lokacin suke haka.

Kamar kullum yauma babu wanda ya makara cikin ɗari biyar ɗin data musu saura ta basu ashirin ashirin, suka mata sallama suka fice.

Tana ƙoƙarin haɗa ruwan da zatawa su Hasana wanka kamin muhd ya farka, yaro ya shigo wai Ummu ta zo, gabanta ya faɗi ko waye zaizo nemanta, cikin ƴan sakannin da tayi tunani ta kasa gano ko waye, ta dubi yaron Ummaru jeka kace wai wane? ya ce to yai waje.

Dawowa yai wai inji Alhaji Ubale, Daram gabanta ya faɗi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ta faɗa.

Ba kowa bane fa ce mutumin da suke haya gidansa, gabanta ya faɗi ne tunawa datai cewar kwanaki yazo amsar kuɗin sa ummansu taita roƙonsa ya basu wata ɗaya in lissalinta dai dai ne yau wata uku kenan.

Jiki a saluɓe ta shiga ɗaki dan ɗauko mayafinta, fatanta kar ya koresu tunda dai ita bata da kuɗin bashi ba kuma ta bada ajiya ba.

Ummu HaniWhere stories live. Discover now