shafi takwas

871 83 6
                                    

Saida ta goya muhd sannan ta yo waje riƙe da tabarma, su Hasana suka amsa suka bi bayanta.

Mutumin yana tsaye daga jikin motarsa, Ummu hani ta ƙarasa har ƙas ta gaidashi, kamin ta ce ga tabarma can na shinfiɗa a soro, ba musu ya bi bayanta dan ko yaushe yazo tun Abbansu nada rai a soro ake masa shinfiɗa.

Kuma gaisawa sukai, kamin ya ce ashe kuma abinda ya faru kenan, Allah ya jiƙanta bansani ba sai da na shigo garin nakejin labari, Allah ya mata rahama.

Amin ummu hani ta ce har lokacin gabanta faɗuwa yake, shiru sukai tana tsammanin batun kuɗin haya zaiyi

Gyaran murya yayi, kamin ya ce yau sauri nake, kiramin wadda kuke tare in mata gaisuwa.

Ɗagowa tai kamin ta ce, wa?

Ina nufin wadda take kula daku mana.

Oh ai ba kowa, mu kaɗai ne ta faɗa jiki a saluɓe.

What? ya faɗa a tsorace.

Eh Da yake dangin namu duk basu da hali, sannan babu tsoffin da zasu zauna damu.

Gyaɗa kai ya yi anman duk da haka wannan ba dai dai bane, ta yaya zasu bakku ku kaɗai yanzu a ina manyan suke?. Ya tambaya

Girgiza kai tai Dan Allah ka kyalesu inma ansa sun ɗaukemu nasan bazasu kula da mu ba, banda kuma gashi an rarrabamu in muna tare ko yaya ne zamuyi iyawar mu dan temakon juna zakuma mufi shakuwa.

Shi kenan, Akwai wata mata an faɗamin mijin ta ne ya rasu, basu haihu ba Danginsa sun saida gidan da take ta na neman haya, da zan sata awani shikenan yanzu zan mata magana, in zata karɓi wannan da kuke ciki ta biya kuɗin rabi, sai ku zauna tare ku basai kun bada ba, aƙalla kuna da wadda zata ganku babba.

Tunda ya fara magabar sai yanzu taji sanyi aranta, hawayen farin ciki ya zuraro mata, godiya kawai take masa.

Jaririn ne abaya ya faɗa, murya a sanyaye tausayin yaran duk ya cika shi.

Cikin sauri ta ce eh.

Kawo shi muganshi ta Kwantosho jiki na rawa.

Masha Allah ya sunansa? Ummu Hani ta ce muhd Usaina tai saurin cewa Ɗan ƙani.

Murmushin yai, ah ki ce Ɗan ƙani ne Eh mana Hasana ta faɗa tana matsawa kusa dashi.

Kasan mene? Yaran suka faɗa, girgiza kai yayi alamar a'a, Ummanmu ce ta haifeshi, kan ta tafi yanzu yaya ce ummanmu, shiru kawai yayi ya kasa magana, yanzu inba zalincin danginsu yarannan ba ta yaya za'a ce yarinya ƙarama haka ita zata kula da yara harda jariri.

Miƙo mata shi yai, ni zan wu ce in ta amince matar zakuga tazo, ku gyara Ɗaya ɗakin ya faɗa yana zira hannu a aljihu dan ciro kuɗi.

Dubu goma ya miƙa mata ga wannan ko wani abunne ku dinga siyarwa, yadda take godiya kai kace ya bata duniya ne jiyai da ace yanada wanda yafi haka da tabbas sai ya daɗa masu sai dai bashi dasu.

Alhaji ubale Ba wani babba bane, zamu iya cewa matashi ne, dan bazai gaza shekara arba'in da biyu ba, yana zaune garin Kaduna yana aiki, shida iyalinsa gidansu Ummu hani gidansa ne da ya ci gado, inda duk shekara yake zuwa garin kano dan karɓar kuɗi gurin masu hayarsa, gida uku ne ɗaya nasa biyu na ƴan uwansa mata, wanda duk shi yake kula dasu.

Daɗi biyu ne ya cika ummu hani ga kuɗin da bata ya kuma tunatar da ita zafata iya sana'a, ga kuma alƙawarin kawo musu wata akalla zasu samu raguwar tsoro aransu.

Koda su Aisha suka dawo bayan sunci abinci kasantuwar alhamis ba islamiya suna gida, ummu taga ga damar yi musu maganar sana'ar.

Yawwa Daman Ɗazu Alhaji ubale yazo, me innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yaushe? me ya ce? su biyun suka faɗa atare zaton su ko ya ce subar gidan.

Murmushi Ummu hani tai, gami da ciro kuɗin da ya bata, shi ya bani ajiyar zuciya sukai Aisha ta ce to me ya ce?.

Bayanin yadda akai komai sannan ta ce to yanzu wa ce sana'a kuke ganin ya da ce muyi? Wadda ba tallah cikin ta.

Duk shiru sukai, kamin sajida ta ce yaya tunda muna da shinkafa ki dinga Dafawa, kinga munaci muna sedawa kuɗin sai ki siyo su kayan miya, sauran ki adana sabida irin siyan su magani.

Murmushi Ummu tai sajida akwai tunani duk da ba wani shekaru ne da ita ba.

Aikam yaya wannan shawarar tayi wallahi, kuma kinga babu mai shinkafa nan kusa anjima sai mu je mu farfaɗawa jama'a inji Aisha.

Tam shikenan Ina ganin innaje siyo kayan miyar har fulawa zan siyo sai mudinga fanke da safe inji Ummu, hakan ma yayi duk suka faɗa.

Duk ihun da su Hasana suke, ƙin tafiya dasu Ummu hani ta yi, dan tasan kaya ne zasu mata yawa, shima Muhammad da kamar ta barshi, ganin su Aisha zasu fita farfaɗawa jama'a yasa ta goyashi tai kasuwar rimi.

Aisha ce ta kulle gidan tana riƙe da Hasana inda sajida ke riƙe da Usaina Khairiyya a gefe, gidan dake kallonsu suka fara shiga suka bada ajiyar makulli sannan suka faɗamata zasu fara saida shinkafa da fanke sannan sukai waje.

Gida gida suka dinga bi, gami da gun masu shaguna, duk matashin da suka gani suna faɗa masa, dan sun san kowa kuma kowa yasansu su kan ce ya tayasu talla.

Sai yanma liss ummu hani ta dawo Aisha da sauran suka gyara kayan miya dan kaiwa markaɗe Na miyar gobe.....



Ummu HaniWhere stories live. Discover now