54

194 21 12
                                    

Daurewar da marar tata ta mata ne ya ɗan saki dakyar ta yunkura cike da juriya ta miƙe gami da karasa cikin soron kuma gaida mutanen ta yi sannan ta ce dan Allah bawan Allah ku taimaka ku kara mana lokaci wata guda bai isa mu samu wani gidan da zamu koma ba koda wata uku ne ku taimaka mudin bamu da gata bamu da inda zamu in lokacin ya cika in har bamu samu wani gun ba maimakon azo ku kuna korar mu, mu kuma muna ganin baku mana adalci ba da zaifi kyau ku sa mana lokacin da ko an samu akasi sai da aka koremun zamuji kwarin gwiwar barin gun gami da cikakken tunanin ai kun bamu lokaci.

Shiru dattijan sukai kafin dayan ya ce eh gaskiya ne to matsakar mu dillalai ne bamu da iko da gunnan sai dai adalci guda da zamu muku mu haɗa ku da wanda ya siyan din in yaga zai iya kara muku sai ya kara, godiya sosai su Ummu din sukai har ta kulla musu kosai kafin su tafi.

Rayuwa kam ta ma Ummu zafi sosai cikin ta kullum cikin damun ta yake da motsi tunanin kannen ta ya cika ta tsoron ta biyu ne a kullum ta wayi gari yanzu in ta mutu fa wurin haihuwa kamar umman su ya su Aisha zasuyi in kuma tana raye wanne irin bayani zata yiwa jama'a game da hallacin abinda ta haifa tasani Allah ya sani abin cikin ta na halak ne sai dai anma ai mutane basu san gaibu ba.

Yawan yadda maganar cikin ta ke yawo agari da yadda in ta fita kai markade ko sayen wani abu ake yada mata da magana ya kuma tada mata da hankali tsoro ya kuma cikata wanda shine dalilin da yasa ta fara rama silar haka cikin yadan fara nuna kansa fite da ada daya bi jikin ta yanzu kam bata da kwanciyar hankali mutuwar Faruk ta jefa ta cikin tashin hankalin da bata taɓa tunanin zata shiga ba.

Tana zaune a dakin su tana tunanin yau wata guda ya rage mai gidan yazo ya tashe su tunda sun samu ya kara musu wata biyu sun gaza samun gun komawa ita ayanzu ma tafi subar unguwar dan abin ya fara yawa ko yan biyu yara sun dena wasa da su da sun fita zaka ji ana ihun Umman su tayi cikin shege.

A'isha ce ta leƙo ɗakin yaya an gama abincin za'a fiddashi mai kikeson a zuba miki girgiza kai tayi a'a na koshi kawai ta ce, Aishah bata ce komai ba ta fi ce kausar ce ta shigo riƙe da abinci ta zauna kusa da yayar tata kafin ta ce Yaya dan Allah ki daure ki ci abincin kinji kodan abinda ke cikin ki, kuma ko dan kiji kwarin jikin ki kar haihuwa tazo miki alhalin kina cikin yunwa zaki galabaita.

Tsoro ne ya cika Ummu sosai gabanta ke faduwa wato kannen ta sun san tana da ciki kenan wato sunma yadda, tsoro ne ya kuma kamata kardai suma kallon matsinaciya suke mata innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ta hau faɗe aranta.

Kausar kamar tasan abin da Ummu din ke tunani ta ce kusan tun dawowar ki bayan mutuwarsa nasan kina da ciki maganar da mutane ke ta yadawa ta kuma tabbatar mun sa zargina Su Aisha har yanzu basu yadda ba sun dauki abun kawai sharri ne ake miki dan anga mu marayu ne muna rayuwar mu ckin rufin asiri

Ummu HaniWhere stories live. Discover now