Umar na tsaye yana kalle kalle ta fito riƙe da Muhd, yana hangota ya saki fuska itama daurewa tayi ta ɗan murmusa kamin ta ƙarasa ta gaidashi.
Cikin sakin fuska ya amsa gami da cewa sai kuma kika ganni ko, murmushi tai eh wallahi.
Shiru suka ɗanyi kamin ya ce eh to daman batun Faruk ne, sai da gabanta ya faɗi jin sunan Faruk ta daure bata ce komai ba.
Ɗazu ya zo ya samen ya faɗan komai da ya faru, banji daɗi ba sai dai abu ɗaya yamin daɗi.
Ɗagowa tayi ta kalle shi, ya ce yes abu ɗaya yamin daɗi aƙalla cewar yau faruk ne da bakin sa yake faɗamin cewa ya shirya barin abinda nai nai in hana shi ya ƙi hanuwa.
Ɗagowa tayi ta kalleshi kamin ta ce in har kai da kuke tare ka hana shi yaƙi hanuwa ta yaya zan samu tabbacin zai dena.
Ɗan sosa kansa yayi kamin ya ce wannan dalilin da yasani farin ciki shine Faruk mutun ne da baya furta abin da bazai aiwatar ba, ina da tabbacin tunda har ya ce zai bari na tabbatar ya bari ɗin.
Ki yadda dani bazan taɓa yadda a cuceki ba, dan yana abokina bazan kareshi ba inda ace banda tabbacin cewar sa ya dena ɗin gaske ne wallahi bazan zo in tare ki da batun sa ba.
Ki daure ki masa uziri ki daure ki ci gaba da sauraron sa, nasan da sannu zaki gyara shi zuwa yadda kike son miji kuma uba ga ƙannen ki da yaran ki ya zama.
Ɗan numfasawa tayi kamin ta ce shikenan naji Allah ya gafar ta mana baki ɗaya, amma wallahi duk sanda na gano bai sauya ba tabbas zan barshi.
Shikenan mun gode Amaryar mu, murmushi tai kayya bari faɗin amaryar mu har yanzu ban gama tunani ba.
A'a dai kiyi haƙuri ki daure ki amshi sunan nan, ya faɗa yana murmushi itama murmusawa tayi kamin ta ce shikenan na amsa dan kai, to godiya muke ya faɗa yana rissinawar wasa sukai murmushi tare.
Sallama ya mata ta amshi Muhd dake hannunsa tayi cikin gida, yayin da shi kuma ya tsaya neman yaro.
Kaya ya bawa yaron niƙi niƙi da naira ɗari sabuwa ta yaron ya ce ya miƙawa ummu hani cikin gida yako amsa cike da murna.
Ummu na zama yaro ya shigo da kaya ta zubawa kayan ido wato dai da gaske ne sai hali yazo ɗaya ake abota shima Faruk haka yake haya taɓa cewa ta tsaya ta amsa bare ta samu damar godiya ko cewa ya basshi sai ta shigo yake aiko yaro dasu ko da ta je ya tafiyar sa.
Abin ka da zuciya cikin ruwan sanyi Faruk ya lallaɓa ummu hani ta haƙura dan babbar wayarsa ma ita ya bawa ta aje masa yasai mai madannai sai da kuma yasa ta kira gidansu ta tambaye su in yanzu suna ganin sa da waya.
Ya takura mata sosai kan ta amince ya turo a ɗaura musu aure tun tana zillewa har ta fara tunanin to ma ita yanzu waye zai ɗaura mata aure sai yanzu ta kuma yadda bafa ta da gata.
Shiko Faruk ya damu burin sa kawai aɗaura musu aure kwana da yinin da yake baya ganin ta daƙyar yake iya kaiwa.
Damun da Faruk yake mata ya fara yawa wanda har ya fara bayyana a fuskarta tanason sa sai dai bata son faɗa masa itafa bata da inda zata kai shina ɗaura mata aure.
Yau suna zaune ita da Hajiya su A'isha duk basa gida Hajiya ta dube ta Ummu wai meke damun ki ko kun kuma samun matsala da Farukun ne.
Yaƙe tayi a'a Hajiya ba komai kawai yanayin rayuwa ne.
Murmushi Hajiya tai kin ga Ummu ki faɗan gaskiya ko da ace ban haifeku ba ni ƴaƴa na m, na ɗaukeku hakan yada duk na karance ku duk wanda ya sauya a cikin ku nasani ki faɗan meke damun ki.
Kuka ummu tasa kamin ta faɗi meke damun ta.
Shiru Hajiya tayi ku ai ba shegu bane kuna da dangi koda basu riƙeku ba haƙƙinku na su aurar da ku na kansu kije ki same su ki faɗa musu kin samu miji kuma danginsa zasu zo gun su.
Shiru ummu tai tana tunani ina ma ace muhd dinsu shine Babba kai ita inama ace yakai kamar Aisha da wallahi shi zata bawa wakilcin su dukansu ya dinga ɗaura musu aure.
Kinji dai ko me na nace miki, Hajiya ta katse mata tunani to kawai ta ce ranta fal tunanin yadda sukai da su kawu ran bakwan ummansu anman ba komai haka zata daure ta je.
Washe gari taja Kairi sukai gidan Kawunsu yana Kofar gida suka gai dashi ummu ta ce gunsa tazo yako haɗe rai zaton sa ko kuɗi tazo amsa.
Ganin haka yasa daman ba batun kuɗi bane kallon ta yai da mamaki yarin yar akwai raini ya faɗa aransa a fili ya ce ina jinki.
Eh to daman akwai wanda mukai batun aure shine yake son turowa na ce ba inzo in fada ma ka fadi ranar da zasu zo din.
A fusace kawu ya kalleta eyye kince ba batun kuɗi bane yanzu batun ubanki ne, wato sai yanzu muke da anfani nan nan kan shinkafa kika ci mana mutunci yanzu da yake kinsan shinkafa bazata miki kayan ɗaki ba, shine kika lallaɓo kika tawo kin manta me kika ce ni ba ubanki bane haka kika faɗamin ku tashi ku bani waje ya faɗa a fusace........
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...