Shafi na Sha biyar

798 97 2
                                    

*Ummu hani*

*15*

*Dan karanta sauran books ɗina biyo ni a shafina na wattpad da Instagram @Fadimafayau nagode*

Girgiza kai kawai ya yi gami da murmushi kamin ya bar gun, ya nufi inda Nasir ya kwatan ta masa

Yaron Nasir ɗin ne ba lafiya, ga ba kuɗi sabida malamin private ne, hutun corona da akai ya sanya basa samun albashi kullun sai buga buga, shi ne leburanci shine dako.

Tare sukai islamiyya da Ayatullah nan zubairiyya da ke Galadanci lokacin su Ayatullah suna cikin gari, kamin su koma GRA.

Duk wani taimako Ayatullah ya bada, shi ya ɗauki Nasir da yaron da matar Nasir zuwa aminu kano, sabida an mai dasu can.

Ita kuwa Ummu hani Ɗakin likita tayi, da gudu suka dawo atare likitan ne ya juyo ya ce da wata nurse ta fitar da Ummu Hani, daga ɗakin yadda take kuka kai ka ce ya ce mata muhd ya mutu ne.

Jijjiga ce irin ta maleria ga ƙyanda abinka da jariri jiki bai kwari, dole ciwo ya wahalar da shi.

Da taimakon Allah likitan nan ya shawo kan lammarin ya na fitowa ummu tai gunsa da sauri, murmushi ya mata hakan yasa ta saki ajiyar zuciya.

Ki je ki kula dashi insha Allah babu komai anman zai kyau ki nema masa gidan sauro gaskiya, koma in ce dukan su dan asibitin nan akwai sauro.

Godiya tai ta yima likitan, inda yai office ɗinsa ita kuma tai ciki.

Muhammad na bacci ta zuba masa ido, ayyanawa take aranta in ya mutu ya zataji, sai da Kursum taga hankalin aminiyar tata ya kwanta sannan ta mata sallama ta fice, Ummu kasa raka ta tai dan gani take kamar in ta kuma barin muhd wani abun zai same shi.

Shi ko Ayatullah daga Aminu kano gida ya wu ce, bayan ya ci abinci ya yi wanka ya motsa jiki, kamar yadda al'adar sa take gami da nafila ya faɗa gado dan kwanciya.

Sai dai me kasa bacci ya yi idanunsa yarinyar ɗazu kawai ke hango masa, yayin da kunnuwansa ke tuno masa da sa'adda take bashi haƙuri cikin sanyin murya.

Fulo yasanya ya danne kansa, wai duk ko ya samu yai bacci anma ina shi har mamaki yake daga ganin mutun for few seconds ace kana tunaninsa haka.

Tashi yai dan duba agogo ƙarfe sha ɗaya da wani abun, ahankula ya sauka daga gadon ya fito daga ɗakinsa yana sanɗa.

Yasan yanzu a tsarin gidansu duk da shi namiji ne dare yayi ya fita, amma yana jin bazai iya bacci ba, in ba zuwa ya yi ya tambayi yarinyar nan me yasa ta tsays masa arai ba.

Bai ɗauki mota ba dan yasan dole Dady zai ji shi, tunda iyanzu yana falon da bai da nisa da bakin gate yana kallon labarai, dan mami da wuri take barci dan kar ya tashe ta sai yazo nan ya zauna zuwa 12 ya koma.

Ɗakin mai gadi ya nufa aransa yana Addu'a Allah yasa bai tafi boys Quarters ba, inda ya ke shi da iyalinsa.

Yayi sa'a yana zaune yana jin Radio.

Ah Ayatu lafiya dai ko, eh daman zan ɗan fita ne shi ne na ce kar a saka sakata, kawai a kulle da key.

Anman baka ganin dare yayi kasan dai Dokar da Alhaji yasa kar in bari kowa ya fita after 9 ko.

Murmushi Ayatullah yayi karka damu ka ce baka ganni ba, bare ma bama za'a kaiga nemana ba insha Allah.

Shiru Baba yayi Ayatullah yai ta roƙonsa, kamin ya ce tom shi kenan dan Allah karka ka daɗe, to ya ce ya fi ce da sauri danma kar Baba ya canja ra'ayi

Yana fitowa tsoro ya kamashi duk da hasken da ya galmaye unguwar ya saba baya fitar dare a inda ya ke karatu kuma duk dare sai kaga wasu a waje.

Daurewa yai ya yi gidan ya Fatima dan basu da nisa, yana tafe yana juyawa bakajin komai sai bugawar iska karar bishiya na tashi, sai lokaci lokaci karnukan na ɗan kuka.

Da sauri ya ƙarasa hango Ya Abbakar na ƙoƙarin shiga da mota, tsayawa Abbakar ɗin yai ganin Ayatullah ɗin dan hasken da ke unguwar yasa ya ganeshi.

A'a sarkin na ci wato sai da ka biyo ta, Dariya Ayatullah yayi ya gai dashi kamin ya ce a'a ba gun ta nazo ba daman gunka na zo.

Towo ni kuma Ayatu, eh Abba, sunan da yaransa ke ke faɗa masa shi Ayatullah ke faɗa masa.

Ok tom mu shiga daga ciki ko, da sauri Ayatullah ya ce No nan zaifi daman niyata insa mai gadi ya kiramin kai.

Towo Ya Abbakar ya ce ya fito daga motar.

Daman frnd ɗina ne ya kirani yaronsa ba lpy, Ayatullah ya masa bayanin ɗazu kamin ya ce shi ne nake son ka aran mota mami da Dady bazasu bari in je ba, cewa zasuyi sai da safe kuma yana buƙatar kuɗi.

Shiru Abbakar ya yi kamin Ayatullah ya riƙo hannunsa Please Abba, shi kenan Karka jima ya miƙa masa key ɗin motar, gami da zaro kuɗi ungo ka daɗa masa.

Sanin Halin Abbakar in yaƙi amsa masifa zai masa, yasa ya amsa yana godiya ya ja mota yabar gun.

Kai tsaye Asibitin Hasiya Bayero ya nufa inda yaga yarinyar ɗazu tayi nan shima ya yi, so kawai ya ke ya tambaye ta me yasa ta tsaya masa arai.

Gado gado yake bi yana kalla ko zai ganta.

Kasan cewar dare yayi su ummu Hani basa saka rai da zuwan kowa dubiya, yasa ta aje hijab ɗinta a gefe muhd na cinyar ta tana bashi mama, yayin da suke hira da maƙociyar ta, wadda itama matashiya ce zatai shekara 19 tana jinyar ƴar ta tafari ne, sun saba sosai da Ummu hani.

Kallon gaban sa da zai ne, suka haɗa ido da ummu, da sauri ummu hani ta ja hijabinta ta lulluɓe jikin ta, shi kuma ya yi saurin juyawa baya....

Ur view about the story and don't forget to vote and share.

Ummu HaniWhere stories live. Discover now