37

444 51 2
                                    

Bakwa commenting fa, faɗin ra'ayin ku da yadda kuke jin labarin shi zai sa in dinga posting akai akai...

Washe gari Bayan ummu hani ta siyar da fanke ta dawo gida, miya ta ɗora ta abincin gida na rana da kuma na siyar war da take.

Tana zaune tana yanka kabeji suna hira da Hajiya Ummu ɗin ta ce dana sauke abincin nan shiryawa zan yi in zo in tafi gidan kawu kan sha biyu tayi masu siyan abinci su fara zuwa.

Anya zaki iya gamawa kan sha biyun nan kuwa, har kije ki dawo yanzu fa tara ta wu ce ga waken ma ban gama tsinta ba, Hajiya ta faɗa lokacin da ta buɗe labulen ɗakin ta dan ganin ƙarfe nawa.

Yau inaga haƙura za'ai da waken kawai in ji Ummu hani.

Kusan sha ɗaya ummu hani ta kammala shinkafa da miyar ta zuba a kulolin da suke zubawa, kan ta shiga wanka.

Ummu na wanka Hajiya na yiwa Muhammad dan in dai Ummu zata fita bazai zauna ba ko ina yana ɗafe da ita.

Sai wurin sha biyu sauran kaɗan Ummu ta kammala shirwa Hajiya ta dubeta anya kuwa bazaki jira su Hasana su dawo ba kin san Halin Usaina in tadawo taga bakyanan zatayi ta nunƙufurcin nata ne da ɗacin rai.

Leƙawa ɗaki ummu ta yi kai har sha biyun ta yi bari kawai ma in kai abin cin in Aisha ta dawo na je.

Hakan ma zai fi dan na tabbatar yanzu inma kinje da wuya ki samu ɗaya cikin kawunnan naki se ma dai ki jira ko ki bada saƙo.

Aikam se da yanma ma kawai zan tafi Ummu ta faɗa lokacin da ta ɗauki botikin da ta yanka salak a ciki.

Da hanzari Muhammad yabi bayanta Hajiya tana zo ba inda zata yayi burus da ita, sai da yaga ummun ta zauna a tebur ta suna maga da Ado wanda zai fito mata da abincin sannan ya koma cikin gida.

Hajiya tasa dariya lallai Muhammad wato se ka tabbatar ba inda zatan ko yayi dariya irin tasu ta yara kan ya zauna ya hau wasan sa.

Sai wurin biyu da wani abin su A'isha suka dawo abinci kawai Aishan ta ci ta can ja kaya ta fito dan amsar yayar tata.

Itama Ummun abinci ta ci bayan ta shiga wanka ta shirya Usaina dan bata yawo da Hasana, ita bata damu ta ce sai ta bita ba.

Duk da kasancewar Husaina tafi hankali bata da hayani sai dai akwai ta da kwalaficin Ummu hani, ada kan umman su ta rasu ko yaushe yarin yar na jikin umman daga baya kuma da ta rasu ta dawo mannewa yayar ta su.

Sai wurin huɗu suka tafi, aiko har ƙofar gida Hasana ta biyo su tana faɗin wallahi Hus saina faɗawa Malam Umar lafiyar ki kalau kika ƙi zuwa islamiyya.

Hararar da Husainar ta watsawa Hasanan gami da faɗin kiji da makarar da kika yi, yasa Hasanan cewa Umma adawo lafiya, ta ɗakawa Muhammad da ke baya duka, kafin ta koma gida, tsoron Husainar take sosai dan ko a makaranta Hasana baki ne kawai da ita da tsokana, anma yara sun raina ta in tayo tsokanar ma sai dai ta zo bayan Husaina ta buya, duk da cewar kamar su daya ba'a gane su anma hali yasa tuni yara suke gane wace Hasana Wace kuma Husaina.

Kusan yayyen su ma kai Har hajiya ba da kama suke gane su ba da haline, Ummu hani ce kawai ko suna bacci kuma ko daga bacci ta tashi zata nuna wace Hasana wace Husaina.

Shiga iri ɗaya ummu hani sukayi da Husaina material ne wanda Faruk ne ya ɗinka musu dukan su, dark blue ne da adon pink yayi kyau sosai duk da kasan cewar Ummu hani baƙa ya mata kyau,ba wata kwalliyar fuska tayi ba dan Kullun mitar Faruk shine ta dena kwalliya in zata fita, wannan yasa mai kawai ta shafa ta goge fuskar ta da tsuma, sai dai duk da hakan ta yi kyau sosai, dan kwana biyun nan ta kuma yin wani fresh har wani haske ta ɗan kuma.

Goya Muhammad da ta yi take kuma riƙe da hannun Husaina shi zai sa kawai wasu su kasa tsaida ida dan zato zakai sabuwar amarya ce mai yara biyu.

Ummu hani ta yi sa'a tana zuwa gidan Kawun nasu ya dawo kusan dawowar sa kenan.

Ba kamar da ba ya na zaune a kan tabarma yana ganin su ya sake fuska yana murmushi, a'a su Ummu ne a gidan namu ya faɗa da fara'a.

Ita ma Murmushin ta yi kan ta durkusa ta hau gaidashi, lafiya kalau Alhamdulillah, ya yan uwan naki ya tambaya. Lafiya kalau wallahi ta bashi amsa.

Tabawa!! Ya kwalawa matar sa kira ta fito daga madafa, itama Murmushin ta saki kan ta ce ah yau su Hani ke tafe murmushi ummu hani ta yi kan ta ce inna ina wuni.

Miƙo musu tabarma inji kawu, ajiye mabirgin da ke hannunta ta yi kafin ta shiga ɗaki tana kuma faɗin lale maraba.

Bayan sun zauna ne inna ta ce ummun ta kwanto da Muhammad.

Miƙo mata shi ummu hani ta yi bayan ta sauke shi yako makale alamar bazai zo ba kawu ya ce kaga sulaiman sarkin ƙiwa.

Murmushi ummu hani ta yi kafin ta ce Muhammadu ne, kunya ce ta rufe kawu dan shi azaton sa Ummu hani ɗin sunan Baban su zata sawa yaron.

Shirun da ya ɗan ratsa ne yasa ummu hani nisawa kaɗan kafin ta ce.

Daman kawu zuwa nayi in faɗa ma gidan su Faruk sun na ce sunason in tare su anasu lissafin ma sati uku suka ce na ce sudai bari abin da kuka yanke shi za'ayi banason a muku tutsu.

Tsuke fuska kawu ya yi jin batun tarewa yasan yanzu za'a fara batun kayan gado.

Kallon ta yayi rai aɓace kan ya ce to in ce dai kunyi kayan gado, ko suma mijin zai miki dan in zan tuna kamar sun ce basai munyi komai ba ko....?

Ummu HaniWhere stories live. Discover now