Shafi na Goma.

807 73 8
                                    

Motoci ne da suka amsa sunansu na mota, ƙirar sabuwar yayi, ajere suke tafiya, kai tsaye airport suka nufa wato muhd murtala da ke nan garin kano.

Tawagar gidan Alhaji lukman kenan, Hamshaƙin ɗan kasuwa, kan hanyarsu ta tarɓo Autan gidansa, kuma namiji tilo da Allah ya bashi cikin yaransa shida, wato Ayatullah.

Basu da ɗe da isa ba girgin su Ayatullah ya sauka, sun isa da wuri ne dan baya son jira.

A nitse ya ke sakkowa daga girgin kai ka ce bayason sakkowa, sai dai ba haka bane ɗabi'ar sa ce haka, komai nasa a nitse yake abinsa.

Koda ya ƙaraso, dai dai inda masu tarar matafiya suke tsayawa ya yi tsai yana bin gurin da ido dan gano mataryansa.

Ya Fatima ya fara hanga, gurin ya nufa yana murmushi da saurinsa.

Ta baya ya rungumeta, I missed you so much yaya, ji yo dashi tai bari kawai My boi nafi missing ɗin ka.

Dady dake gefe ya ce eyye wato yar uwarka kawai kai missing, mu ko oho ko, Mami ta ce kyale shi Dadin zainab zo mu tafi.

Da sauri Ayatullah ya ƙarasa inda suke, habawa kuma kunsan nai missing ɗinku sosai daga ku sai yaya da kowa da kowa kawai ita na fara gani ne ya faɗa yana langaɓe kai.

Eh mana ai dole ita zaka fara gani, tunda ita ce aranka, mami ta faɗa tana masa hararar wasa.

Duk su biyun ya haɗa yasanya ajikinsa, yana faɗin haba sai yanzu naji sanyi araina, rashin iyaye kusa ai ba daɗi gabaki ɗaya sika sa dariya.

Kaga malam sakar min iya ye zainab ta faɗa da salon tsokana.

Juyowa yai ke kuma wa ce, nasanki, harararsa tai.

Oh na tuno ke ce wadda su Dady suka tsinto ko, ta kai masa duka ya kauce yana dariya.

Haka yabi sauran ƴan uwan nasa sukai yaushe gamo, Zainab ce ta ƙarshe ahankula ya raɗa mata a kunne, nifa ban missing ɗinki ba, ture shi tai kaɗan alamar wasa, to ni ce maka akai na damu ka dawo ne, ni intani ne kama bar ƙasar ka dena dawowa, masa mu sarari, cikin wasa duk take faɗin haka.

Kyaji dashi ni karki cika ni da abinda ba har zuciyarki yake ba, nasani ji kike tamkar kije ki jawoni.

Turo baki tai, ni kaga yan zuma ka koma, baka ji ke ɗazu me mami ta ce ba Dadin Zainab, meaning ba wanda yai missing ɗinka Dadinma anbarmin.

Yatsina fuska ya yi, ya yi rau rau da idanunsa, ya matsa jikin yayar su Yayata kinganta ko.

Ya Fatima ce ta kai mata duka, Allah zainab ki kiyaye mu, duk aka sa dariya sukai gurin motacinsu.

Dady da mami sun shiga tasu motar, Mami ta ce ka shigo nan kawai mu tafi, Zainab tai saurin cewa ai gwanda dai ya shiga ɗin, danni wannan sabuwar ni ce a cikinta, ba me hanani shanawa.

Aiko kanta rufe bakin ta ya shige motar itama kuwa ta shige kinge, malama wallahi bazai yiwu ni inshiga tsohuwa ba, sai dai mu shiga wannan ɗin tare, tagumi ta yi, da sigar wasa Baba Habu muje ta ce da driver ɗin.

Ayatullah kenan Matashi ɗan gata gaba da baya ta gun iyaye da ƴan uwa.

Ya Fatima ita ce Babba, sun shaƙu sosai dashi, kusan ita tai rainonsa hakan yasa kamin ma ya ambaci mamin su sau ɗaya, sunan yaya ya fito daga bakinsa sau goma.

Zainab ita ce daga ita sai shi, sai dai ta bashi shekara bakwai, dan har su mami sunyi zaton ita ce auta, Allah ya kawo Ayatullah sai dai tazarar shekarun su bai sa ya be zama kamar sakonta ba.

Yadda suke rayuwa kai kace baifi shekara biyu ko ɗaya ta bashi ba, wato sako da sako suyi faɗa su shirya tun yarinta, yanzu da aka girma babu faɗan sai dai sukan gwada sakuntar...

*************

Ummu Hani ce zaune a zauren gidansu inda kulolin abincin ke daga ƙofar gida, kamar ɗazu da safe, tai mamakin yadda ake ta siya daɗi da farin ciki ya cikata.

Zuwa huɗu saura ta siyar tas, tasa Usaina ta kira su sajida suka shigar da kulolin.

Tana gida sai aikowa ake siyan shinkafa, tana cewa ta ƙare sai gobe, dan duk wanda ya siya musamman matasa sai ya faɗawa abokinsa dan kuwa ummu Hani ta iya girki.

Rainon ummansu kenan, tun yaranta suna ƙanana take sanyasu aika ce aika ce hakan yasa ummu ta horo ta ko ina.

Zaune suke a tsakar gida, A'isha na wanke wanke Muhd na hannun sajida inda Ummu hani ke lissafa kuɗi.

Kunga cinikin da albarka wallahi inaga indai zamu ɗore ahaka koda abincin mu ƙare zamu iya rayuwa.

Aisha ce ta ce gaskiya kam, nima fa yaya nayi mamakin yadda daga farawa har an waye damu.

Nima dai gaskiya inji sadija.

Ina ga ko dan jiyan mun yawata da yawa mun farfaɗa in wasu sun mance wasu zasu tuna kairiyya ta faɗa.

Yawwa na ce ba, ya kuke ganin zamuyi da ribar da muke samu ummu hani ta tambaya.

Inaga kawai banki zamu samu mu tara kinga kamar yadda kika faɗa ɗazu in abincin sadakar can ya ƙare mu kuma already mun tara na siyan wani buhun shinkafar, A'isha ta ce tana ƙokarin dire kwandon data kife kwanuka.

Bari to in wanka sai innaje rimin siyo kayan miya in ta wo da banki insha Allah, ummu hani faɗa gami da ɗaukar muhd daga cinyar sajida.

Yau tunda kuna gida agunku zan barshi sabida naga gajiya yake abayan, ga iska jiya sai da na shafeshi da rab da daddare sabida yadda hancinsa ya toshe, inaga yau ma sai na siyo man shanu in saka kasa ahancin sa girjinsa. Ummu hani take faɗawa ƙannen nata

Tom shi kenan sika ce.

Mama ta bashi sai da ta tabbatar ya ƙoshi ya yi gyatsa ta miƙawa Aisha shi, tana faɗin sauran amai mugunta, gabaki ɗaya suka sa dariya dan sun san da Aisha ta ke, ita ce gwanar yima yara mugunta, dan haka ne basa shiri sa su Usai.

Sai da Ummu hani tai wanka ta shirya tsaf duk da ba wata kwalliya tai ba mai kawai da kwalli ta shafa ta goge fuskarta da tsumma anman hakan baisa kyanta ya ƙi fitowa ba.

Har ta ce musu ta fita, ta dawo ku maida wa da momin walid kulolinta tunda sana'a ba yar ƙare ba ce, zan siyo mana bokitai masu murfi muga zuwa musamu wani abin sai muma musayi ta mu.

Khairiyya ce ta miƙe da sauri tana faɗin ba in miƙa mata.

To uwar yawo zauna, Sajida ki miƙa mata kuma wallahi na dawo aka ce kun fi ce zan gamu da yaro, ta faɗa tana shafa kan muhd ji take tamkar karta barshi sai dai ta na gudan masa mura, tai waje ita da Sajida inda ita Sajida ta shiga maƙota Ummu tai titi.....

Ummu HaniWhere stories live. Discover now