last chapter

353 41 62
                                    

I might change my mind to post more chapters  depending on the comments

Ran Ayatullah ba daɗi ya ce au ashe kana gida Kawu Barka da yanma kawu ne ya ce to shan kunun na mene badai dan na ce kaje gunta ba ran Ayatullah ya kuma ɓaci sai dai kan ya ce wani abu Umma ta ce Malam gaidaka fa ya ke sai a lokacin ya ce lafiya kalau maza ku je. Gida ne Babba sosai kusan duk Area din babu ya shi duda cewa ba wani na masu kuɗi bane anma kasancewar sa cikin gine ginen talakawa sai ya fita zakka a ƙofar gidan Ayatullah ya parker Tijjani ya shiga. A'isha suna farfajiyar gidan sun kure waka gami da kafa ring light a gaba suna rawar wakar da take trending a Tiktok kwana biyu wato ashe daga zaune ma ana Tijjani ya kusa minti uku sannan suka katse Aisha ta haushi da masifa bana ce kar wanda ya biyoni ba ni wallahi na tsani damu Tijjani bai damu ba ya ce to ai Baba ne yace in rako Ayatullah wai zakuyi maganar aure.

Dariya Balkisa ta sa hajiya su Pops fa da gaske suke aurar da mu zasuyi nima dazun Ib yazo wai Boos dinmu ne ya turo shi, tsaki Aisha taja aiko wallahi Ni ban shirya aure yanzu ba jeka kace ya shigo inji Balkisa Tijjani na fita suka kuma kunna wata wakar da take trending ta Warr Aisha ta cika kaya a ciki da mazaunan ta rike da hoda yayin da Balkisa ke acting tamkar namijn Ayatullah tuni ya kufula kan Tijjani ya fito kawai baya son batawa Abban sa rai anma da tuni ya tafi wallahi.

A ciki sa suka shiga sai da suka gama rawar su sannan Balkisa ta matsa gefe ta hau editing don so suke suyi posting yau dan suma su samu su shiga challenge din kar viewers dinsu suga basuyi ba yayin da Aisha ta zare kayan da ta zira a jikin nata ta matsa kusa tana goge fuska. Sannu ko ta faɗa bai iya amsawa ba dan yasan yana buɗar baki zai iya zaginta.

Bata damu ba ta ce yanzu Tjee ke faɗan kazo batin aure to gaskiya ni ban shirya aure ba kaje ka faɗa musu though u are my type but yanzu dai am not ready in zaka jirani to no i mean u have to wait for me, tsaki yaja lallai ma yarinyar nan ta rainashi cikin fishi ya ce sabida me zan jiraki, dariya ta yi sabida ina sonka mana kai lallai bata da hankali ya kuma fade a ransa, yes ina sonka kawai ban shirya aure ba anma in kaga zaka barni inyi Tiktok dina it's ok am good to go.

Balkisa da ke gefe ta ce Film din fa Aisha ta ce ai shi kinga dayan nan kawai nai niyar yi Bama sai ansa shi cikin sharadi ba, what film fa are u mad u mean ni zan auri yar film ya kuma faɗa da ɗan karfi, dariya tasa to ya zakayi kwafa kawai ya yi bai ce komai ba. To ya zaka barni in Tiktok din ta faɗa bayan shirun da ya ratsa.

A fusace ya ce baki da hankali ne ni wallahi matata bazatai Tiktok ba fuu ya fi ce taɓe baki ta yi taja tsaki Balkisa ce tace ke baki da hankali ki samu wannan guy din in ya kufce miki to wallahi ko irin su Mai baranda baki samu shi yasa nake lallaɓa Ib in akai auren na haihu duk wani rashin mutunci zan fito da shi fili lokacin ko beso darajar yaranmu ya zauna dani.

Shiru Aisha ta yi eh kuma fa hakane ni kaina nasan inna rasa Ayatu nayi asara ga kyau bana filter ba ga nutsuwa ga illimi banji ko shiga Tiktok fa yanayi, to kin gani kawai ki basar ayi komai in an daura kun haihu bazai sake kiba koda ba ɗan uwanki bane bare jinin ki ne doke darajar yara da iyaye ya kyaleki.

Koda Ayatullah yaje gida Hajiyar su ya lamintawa komai ta tsani Tiktok da yan film ta yi ta faɗa dakyar ta shawo kan Alhaji yace shikenan zai samu kanin nasa, ilai kuwa ta same shi ya ce indai Aisha zata cigaba da Tiktok to gaskiya shi bazai yadda ayi auren ba.

Koda Kawu ya dawo gida ya yi tama Aisha faɗa umman su ta haushi da faɗa danme zai dungawa Aisha faɗa mene aibun Tiktok bayan a gida suje video din bawai yawo suke zuwa ba A'isha ce ta ce Umma kyale Baba badai Tiktok bane na daina ai aure yafi komai murmushi Umma yasa yawwa yar albarka ai gwanda da kika watsa masa aniyarsa kika dena nima nafiso kiyi auren ki, yawwa ko kefa yar kelen Baban ta yanzu taso muje mu samu yayan tunkan ya maganar fasa auren ta yi nisa kawu ya faɗa.

Ummu HaniWhere stories live. Discover now