Kai tsaye asibitin suka wuce da musa, office ɗin likitan suka wuce batare da wani biye biye ba, dan su Faɗawa likita ga Musa yana so su gwadashi.
Ba ƙaramin tashin hankali Ummu ta shiga ba, da likitan ke faɗa musu sai dai suyi haƙuri Allah yaima umma cikawa, kukanma kasayi tai, baby ɗinsu ta amsa ta rugumeshi cike da tausayi.
Da taimakon likita, da su Musa aka basu gawarsu suka yo gida da ita, ummu gani take kamar umman kawai bacci take, tama kasa yadda da cewar wai umman gawa ce.
Kusan da asuba suka dawo gida, kwata kwata ummu bata rintsaba, ita da inna da Su umma Balara maƙotan su suka yiwa ummanta wanka, ita ta tsefe mata kai ta gyara mata shi, duk gani take umman zata farka ba mutuwa tai ba, kawai faɗe likitan yai.
Tun asuba gidan ya fara cika yan uwan umman da na Abban su, duk sun hallara jira ake kawai gari yai haske a kaita.Har lokacin ummu ta kasa kuka riƙe take da baby ɗinsu, ta shiga ɗakin da umman ke kwance cikin likkafani, ahankula ta zauna ta bude mata fuska.
Fuskarnan tai wasai, hancinta toshe da audiga, ahankula tasa hannu ta cire audigar, ta dora jaririn a cikin umman, ita kuma ta dora kanta akan ƙirjin umman, tana shakar turaren almiskin da aka fesa mata, umma yazanyi da jariri, dan Allah ki tashi nasan baki mutu ba, ta faɗa ahankula.Ke mai kike haka cikin faɗa kawunta ke faɗe, tashi ki fita bata ce komai ba ta ɗauki jaririn da tun jiya ba'a sanya masa kaya ba tai waje.
Takwas dai dai masu ɗaukan gawa suka shigo, tana kallo suka ɗauki umma sukai waje, ta kuma rungume jaririn ranta na mata zafi, wato ashe ma hawaye rahama ne, yau da ta kasa kuka ji take tamkar ana tafasa zuciyarta, sabida yadda take mata ciwo da raɗaɗi.
Wajen tara inna mai Ɗanwake tasa Muklisa ta je ta ɗebo su kairiyya a gidanta, dan ta hana akawo sune dan karsu ga gawar umman nasu hankalinsu ya tashi tunda yara ne.
Tare suka shigo da muklisa, tana ɗauke da Usaina inda Aisha ke ɗauke da Hasana, khairi na riƙe da hannun sajida ajere suka shigo, sai alokacin Ummu hani taji kuka ya tawo mata, ganin ƴan uwan nata.
Daurewa tai ta shanye kukan, da sauri usaina tasa zillo sai Muklisa ta sauketa, tana direta tayo gun Ummu tana kuka, tana cewa, yaya wai ummanmu ce ta mutu shiru ummu tai, batace komai ba kawai ta rungume ta, tanasan kuka anman tasan in tayi zata raunana ma ƙannen nata zuciya, hakan yasa tai shiru dan yanzu tasan tana buɗe baki kuka zai tawo mata.
Wurin goma Alhaji Bala maƙocinsu ya aiko da buhun shikafa har uku, da galan ɗin mai, kan kace me har mutane sun ware anata girke girke.
Sosai gidan ya cika, kai bazaka ce gidan mutuwa bane, hira kawai kowa yake ciki kuwa harda shaƙiƙan umman, wanda ya kamata ace bayan su ummu hani, su zasu fara jin mutuwarta anman da alamu ko ajikinsu.
Batun dangin Abbansu Ummu hani kuwa daman su ko oho, dan bason umma suke ba, dan haka mutuwarta ba damunsu tai ba.
Zaune suke aɗaki, ummu hani na rike da baby, wanda duk cikin dangin nasu babu wanda yai ƙokarin yace zai sa masa suna, dai dai da ɗaukansa babu wandai ƙoƙarin yi, bare jin lafiyarsa.
Hasana dake manne jikin ummu hani ce, cikin muryarta ta yara ta dubi Ummu tace yaya, wai wannan ƙaninmu ne?, ummu hani tai murmushi, eh ƙaninmu ne, to ya sunansa yarinyar ta tambaya.
Duban yaron ummu hani tai, sai yanzu ta tuna, anafa sawa jariri suna, bakinta tasa akunnensa tai nasa huɗuba, sannan ta dubi Hasana tace sunansa Muhammad.
Yeee muma munyi Muhammad, Hasana ta faɗa, ummu tai murmushin ƙarfin hali.
Ummu hani da kanta taiwa Muhammad huɗuba, dan taga iyayan nasu da alamu sun mance da anbar jariri, tunda har biyu ga mutuwar, dai dai da biyu da haihuwarsa sun kasa bi takansa, kayan da take saka masa ma Makociyarsu ta ɗebo cikin kayan jaririnta sabbi da kwance ta bawa Muhammad ɗin.
Ranar biyu ma sai da wani ya kuma kawo shikafa, buhu guda sai dai me kaf zuwa uku dangi sun dafe ta sun kwashe wata.
Da yanma haka kowa ya tattara kayansa, da yaransa sukayi gaba da zummar sai ranar bakwai.
Ummu hani tayi zaton ko mutun ɗaya ne zai zauna tare dasu zuwa bakwai, ararrabasu dan tasan dole sai dai kowa yadauki daya ko biyu, anman sai taga babu ma wanda yai maganarsu.
Haka ita da kanta cikin dare taje ta rufe musu ƙofa, ko bayan rasuwar Abbansu bata taɓa zuwa ta rufe ƙofa ba, umma ke rufewa, asoro ta durƙushe tasha kukanta, tun mutuwar sai yau tasamu tai kuka, abinda ya tsaya mata a maƙogwaro yaƙi gaba yaƙi baya sai yau ta samu yaɗan motsa, yabar inda ya tokare mata, duk da cewar bawai yai kasa bane, sai dai taɗan ji sanyi aranta.
Washegari rasa me zasuci tai, dan ko kwayar shikafa babu agidan, bugun kofar dataji ne yasa tai saurin buɗe gidan, Imrana ne yaron maƙotansu rike da kwanon sha, wai gashi inji ummanmu daɗi ya kama ummu hani, dan yanzu tunaninta me zata ba su Usaina.
Kan goma sun samu abinci sosai na maƙota, masu kawowa gidan mutuwa.
Madara kamar kullin ta dafawa Muhammad, yasha rabi ta bawa su Hasana rabi, dan in bata basuba in suka hau rigima, mai rarrashinsu sai ya shirya, umma kawai ke iyawa yanzu kuma babu ita.....
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...