Eid Mubarak!
Miƙa mata wayar Ummu hani tayi, kafin ta ce haka ne bancan canci miji kamar Faruk ba sai dai kaddara ta zaɓa min shi, na karba Allah yaban ladan hakuri zam cigaba da yi masa addu'a, shidin mijinane an riga an ɗaura bacin haka ma yanada wani bangare nasa na gari zan kalli wannan ɓangaren in cigaba da zama dashi, karki damu inaji araina zai daina ko me yake.
Sakato Fatima tayi tana kallonta ada ta raina shekarun yarinyar tana zaton tana nuna mata zata rushe da kuka ta tubure sai ya sake ta, sai yanzu ta kuma Yadda mace da wayon ta ake haifaeta bawai shekarunta ba.
Shiru sukai na wani lokaci kafin Fatima ta ɗan yun kura ni zan wuce anma dai ki sake tunani.
Murmunshin Ummu hani tayi ki gaida gida, Nagode ta bawa Fatima Amsa ba tare da ta bata amsar mai ta ce ba.
Dakyar Fatima ta iya kaiwa motar ta yadda ƙafafunta sukai sanyi tama rasa me ke wakana aranta, ta jima a motarta kafin ta iya janta ta bar layin.
Tana barin layin ta faka motar yadda taji bazata iya tuƙin ba, wayar ta ta ɗauka ta hau laluben lambar da take son kira.
Bugu ɗaya aka ɗaga kamar kiran nata ake jira, kana ina ta Faɗa a kasalance banji me ɗayan ɓangaren yace ba sai ji nayi tace ok ina inda ka min kwatance ta aje wayar.
Kamar minti biyar ya iso, Matashi ne da bazai wuce shekaru talatin da biyu ko uku ba, Ba fari bane sai dai bama ce masa Baƙi ba kyakkyawa ne dogo ba can ba, sanye yake da manyan kaya na Hausawa ruwan madara duk da a rikice yake bazaka kasa gano kamalar sa da tsantsar nutsuwar sa ba.
Daga Ɗan gaba kaɗan ya aje motar sa ya ƙaraso inda motar Fatiman take har da ɗan gudun sa.
Kishingiɗe take jikin kujerar motar idanun ta a rufe sanin halinta yasa bai kwankwasa ba ya buɗe yadda ya zata a buɗe kuwa motar take, cikin Muryar sa mai cike da kwarjini yace me ya faru bana ce kar kizo ba.
Hararar sa tayi tace ni buɗen baya kwanciya nake sonyi bai ce komai ba ya buɗe mata, ta miƙo masa hannu alamar ya tai maka mata ta fito kamar bai san me take nufi ba ya juya baya.
Ɗan ƙaramin tsaki tayi ta fiti ta koma baya ya rufe ƙofar ya koma mazaunin driver gami da jan motar.
Tafe suke kowa da abin da ke wakana aransa kamin Matashin saurayin yace wai me ke damun ki ne.
Ban sani ba tace inda ka damu da me ke damu na ai da ka taimakan ka dawo dani baya anma tsabar wuƙanci ka wani juyar da kai.
Wai dan Allah Fatima ke wace irin mutun ce, sau nawa zance miki azabar Allah ta tabbata ga wanda ke taɓa jinsin da ba Muharramin sa ba.
Kaga malan wannan lalura ce ba wa'azi nace kamin ba.
Ba wata larura......ka tseshi tayi cikin faɗa fitar min a mota.
Bai kuma cewa komai ba ya faka motar a gefen titi ya fita, inda ita kuma ta dawo gaba taja motar ta tabar gun a guje. Girgiza kai kawai yayi ya hau ƙoƙarin tsayar da Ɗan sahu.
Mansur kenan Ɗa ga Alhaji Muktar hamshaƙin ɗan kasuwa da yai ƙaurin suna a fannin sa Mansur yaro ne Ɗan gata abinso ga iyayen sa a nutse yake ga hankali da sanin ya kamata duk cikin Abokanan mahaifinsa kowa burin sa inama Mansur yaron sa.
Shi kansa mansur zamu iya cewa ya shahara a nasa fannin dan ba irin yaran nan bane masu dogaro da abun iyayen su tun yarinta Allah yayi shi da son neman nakansa.
Sauƙin kansa bazai sa kayi tunanin shi din wani bane.
Tun tasowar Fatima Allah ya jarabce shi da son Fatima sai dai ita ko kaɗan bashi bane agabanta hasalima bata kallon sa a matsayin Namiji.
Duk da cewar yasan abinda suke da Faruk, sai dai ko sau ɗaya zuciyar sa ta kasa tsanar ta shi kullum burinsa ɗaya ne ta shiryu ta zama ta kwarar ta so shi ko da ƙimar ƙwayar zarra cikin kason soyayyar da yake mata ne.
****************
Fatima na Futa Ummu ta sa kuka dauriya take tun ɗazun tasan da Fatiman ta kawo yanzu a gidan nasu da tabbas kukan nan zai iya kwace mata a gaban Fatiman kamar yadda ya kwace mata yanzu.
Muhammad ne ya sa hannu ya hau goge mata hawayen yana gwalan gwanton su na yara, goge hawayen tayi sai dai ba alamun zai tsaya Usaina ta kalla ta ce karku fita karki bari Hasana ta Daki Ɗan ƙani to Usaina tace ta cigaba da fige tattatasan da take kar kace wata babba ce.
Ummu na shiga ban ɗaki kukan ya kuma kwace mata kuka tayi mai isarta da tayi shiru sai abin da ya faru da ita da Faruk a gidansu ya tasomata gami da abin da ta gani a wayar Fatima duk da aranta bata yadda jiya akai video ɗin ba anma tanajin wani ɗaci aranta ganin mijin ta da wata a gado.
Sai da taji faɗan su Usaina daga tsakar gida sannan ta tuna bafa iya tata rayuwar ce mai mahimmanci ba akwai ƙannen ta aƙasanta. Wanke fuskar ta tayi ta fito da sauri dan jin yadda faɗan ya gauraye Muhammad na kuka Hasana na kuka.
Ilai kuwa Usaina ta gani na haki riƙe da kwano wanda da alamu bugawa Hasana tayi, kwanon ta amshe kafin tayi ƙarfin halin cewa mai yasa zaki buga mata kwano bana hanaki mugunta ba ke bakisan Yayar ki bace.
Cikin rawar Murya Usaina tace Allah Umma ita ce muguwa nace mata karta daki Ɗan ƙani taƙi wai dole sai ya bata tumatirin da kika bashi bacin ga wasu nan da yawa nace ta ɗauka a ciki taƙi shine ta makeshi nima na make ta.
Murshi Ummu hani tayi yaran akwai rikici Muhammad ta ɗauka ta hau lallashi yai luf aƙirjinta, tahau rarrashin Hasana da haka ta ɗan samu damuwar ranta tayi sanyi suka cigaba da gyaran kayan miyar.
Suna nan zaune su Aisha suka dawo ta ce bari ta kai markaɗe Khairiyya da Sajida sukai sukai ta bari su kai kamar yadda suka saba tace ita zata kai tanason zuwa gidan su Ummul kairi dole suka kyaleta badan sun so ba.
Ba inda zata kawai tana son samun sa'ida aranta ne dan tasana in ta fita zata iya jin sanyi a ranta.
Tafe take tafiyar ma juriya kawai take zuciyar ta babu daɗi yanayin garin da yanayin zuciyar ta sai in gizata suke tasa kuka anma tana daurewa.
Kamar ance ta kalli gefe karaf sukayi ido biyu da Bashir murmushi ya sakar mata daurewa tayi ta maida masa bayan yaƙi datai da hawayen da ke ta yun ƙurin sai ya zubo kuncin ta.
Tasowa yayi yayo inda take ba haka taso ba dan ko kaɗan bata shirya yin magana ba ayanzu sai dai Bashir ya wuce ta ganshi ta wuce.
Gaidashi ta farayi kafin cikin sauri tace Dan Allah karka min magana banson bakin umma ya kamata ta dalili na. Yadda tayi din yasashi dole tsayawa inda ita kuma tayi gaba wani abu ya kuma zuwa mata wuta ya tsaya ji take tamkar ta rushe da kuka inda tasan zata ga Bashir da tabbas bazata fito ba maimakon zuciyar ta tayi mata sanyi sai ma wani baƙin cikin da ya kuma cika mata zuciya.
Dakyar ta iya ƙarasawa gidan markaɗen tana ajiyewa ta yo waje dan ƙarar injin bata mata rai kawai yake kuma yi ta jima a kofar gidan Markaden kafin ta shiga ta dauko bayan an markaɗa....
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...