22

741 91 13
                                    

Ranta a ɓace ta shiga gida tama kasa yin tunanin da yake dai dai.

   Wayar ta da ke hannunta ce ta hau ruri alamar kira, tasan Faruk ne kashe wayar ma tai baki ɗaya takai ta ɗaki ta aje cikin kayanta.

   Aikinta ta cigaba yayin sauran ƴan uwanta keta hira.

   Shiko faruk iska ya kaima naushi, cike da takaici inda ya ɗan mari goshinsa, ya jima agurin kamin ya iya tafiya gida, ba tare da sanin me zaiyi ba.

  Koda dare yai kasa bacci Faruk ya yi ransa fal tunanin Ummu, tare da kewar muryarta dan ya riga yasaba jin sanyayyiyar muryarta, dan kullum dare kamin su kwanta sai sun sha hira.

  Wayarsa dake yashe saman gado ya kai hannu ya ɗauka, inda ya hau kiran Ummu da yai saving da Abokiyar rayuwata.

   Sai dai kamar ɗazun wayar akashe take.

  Ya Allah, ya faɗa inda ya miƙe yana kaikawo a ɗakin nasa,  cike da tunanin yadda zai shawo kan abin, mai zai faɗa mata yake tunani, sai dai kamar an toshe masa kwakwalwa ya kasa tunani mai anfani.

   Kamar Faruk, Ummu kasa bacci tai itama bayan ta gama komai, mai makon ta kwanta sai ta hau nin ke kayan da suke daman a ninke suke.

   Koda ta gama wayar ta da ke gefe tajawo tahau kallo kamar ta kunna sabida yadda take kewar muryar Faruk anman zuciyarta ta haneta.

  Haka ta maida wayar ta koma gefen da ƴan biyu suke ta gyara musu kwanciya, ta koma ta kwanta duk da cewar idanun nata a bushe suke kamas babu alamun bacci a tattare da su.

  Abinda yafi tsaya mata shine wato tun farko ko yaushe da take ganin Faruk na maida hankali a waya abin da yake kenan, ada tayi zaton ko chatting yake ashe kafi chat matsala yake.

     Batasan sanda Bacci ya ɗauke ta ba, sai kukan Muhammad taji, wato ya tashi shan kokon sa lokacin ana kiraye kirayen sallah na farko.

Sai da ta bashi kokon ya shanye, sannan ta mai dashi ya koma Bacci, maimakon ta koma bacci kayan fanke ta fara haɗawa dan yanzu shida ma ta fara suya, dan ana ciniki sosai ya bunƙasa, tun kan su buɗe ƙofa ake fara zuwa, tuni ƙullin ya tashi, komai takai soro inda ta dawo cikin gida dan ɗora abincin kari na ƴan makaranta su Aisha.

Kamar yadda ta saba bayan sunyi sallah  ta ɗora mai dan toya musu nasu fanken, inda su kuma suka koma bacci sai shidan ta tashe su.

   Yau komai take yinsa kawai take, duk da batajin yanzun zata iya auren faruk, anman tana jinjina rayuwarta babu shi, sabida yadda take jin sa aranta tasani tana sonsa sai dai ba irin mutumin da take fatan ya zama abokin rayuwar ta bane, dan batajin zai iya yima ƙannen ta da yaran da zasu haifa isasshiyar tarbiya.

   Kusan Da sassafen Faruk ya shirya koma gun aiki bai je ba, sai gidansu Ummu, tana zuba fanke ta hange shi sai da gabanta ya faɗi ta daure tamkar bata ganshi ba.

  Yayi kyau sosai ga haiba da ya ƙara, kamar ko yaushe manyan kaya ne ajikinsa wanda suka amshe shi.

  Baiyi gangancin matsawa ba, daga nesa ya tsaya dan yasan bata wuce tara da zummar da zarar ta tashi sai ya ƙarasa.

  Ilai kuwa tana gamawa yana ƙoƙarin ƙarasawa, tai gida da sauri sai su Usaina ne suka zo suka shigar da kayan, jigum yayi kawai ya jima agun kamin ya koma motarsa dan barin gun.

  Kai tsaye office ɗin Umar ya wuce yai sa'a baya komai hakan yasa sakataren sa ya masa iso ya shiga.

    Towo lafiya dai na ganka kamar an gefoka, umar ya tambaya.

   Bari kawai Umar ina cikin wani hali wallahi nan ya bashi labarin duk abinda ya faru.

  Dariya Umar yasa, kace Allah ne yaso ta, ta gane tun yanzu kaga sai ka ƙara gaba tunda dai nasan ba dena kallon abinka zakai ba.

  Haɗe rai Faruk yai kaga Malam banson iskanci ni nace maka bazan dena ba, and wallahi ka dena min maganar rabuwa, na faɗa ma san yarinyar nan nake ba sha'awa ba aurenta zanyi.

  To naji yanzu ni me kake son in maka, Umar ya tambaya yana kallon Faruk.

  Yawwa ɗan gari yanzu kai magana, so nake kaje ka bata haƙuri, ka tsaran ita ta amince kuskurene kasa ta dinga ɗaukan wayata.

  Naji zanje but sai kamin rantsuwa tsakani da Allah kake sonta aurenta zakai, dan bazai yiwu inje in shawo kanta ba ƙarshe kaje ka ɓata musu yarinya laifin araba mana.

  Tsaki Faruk yai in da zan lalata ta da tuni ban yi ba, bana fatan inzama silar gurɓacewar rayuwar Ummu hani, ita ɗin sonta ajini na yake, burina ta zama uwar ƴaƴa na ta yaya zanyi gangancin ɓata uwa ga yara na.

  Tom shikenan zanje duk da dai naji ka ne, nasan halinka in kana buƙatar abu gun mace ka iya shirga ƙarya.

  Shiru kawai Faruk yai yayin da Umar keyi masa tsiya, wai duk tsala tsalan ƴan matan da yake buri, da masu sonsa ya ƙare a ƙaramar ƴarinya baƙa kuma.

  Sai yanma Umar ya shirya bayan ya dawo daga aiki ya huta yai gidan su Ummu.

  Koda ya aika cewa tai bata nan, sai da ya kuma aika yaro ya ce ace mata ba Faruk bane Umar ne.

   Kamar bazata fito ba dan batason wani abu ya haɗata Faruk sai kuma ta canja shawara bayan tayi wani tunani.

  A kintse take kamar koyaushe mayafi kawai ta yafa tai waje...

Inbakwa following don't forget to follow, Voting bafa kwayi shida comments kodao labarin babu daɗi ne adena

Ummu HaniWhere stories live. Discover now