49

57 2 0
                                    


Na gaji da rubuta labarin nan few chapters to go insha Allah.

Fatima na barin ɗakin kai tsaye ɗakin ta nufa inda ta hau haɗa abin da zata buƙata in sunje can, duda ranta babu daɗi kusan tun haɗarin Faruk anma yau sai ta ji sa'ida a ranta sakamakon yafe mata da Abban ta ya yi da kuma yadda da ya yi taje duba Faruk ɗin. Sai can dare ta samu ta runtsa ji take tamkar ta jawo goben ta je ta ga Faruk yadda ta tsara aranta shi ne in har suka je da sunyi kwana kaɗan zata takurawa Dadin su Faruk a ɗaura musu aure dan tasan in har ya warke sarar to tabbas Faruk zai iya cigaba da hutsewa.

Washe gari da Sassafe suka nufu filin jirgi dan tashin safe zasuyi ilai kuwa kan tara sun tashi ayanzu hango kanta kawai ta ke a matsayin matar Faruk.

Da rana sosai suka sauka a garin Abba yai yai Fatima ta tsaya su huta zuwa dare su karasa asibitin taƙi dole ya bita sukai asibitin.

Yau Mami bata zo ba tana masaukin su Ummu ce kawai ta zo ko Muhammad ɗin ma bata tawo da shi ba tana zaune suna hira da Faruk gwanin ban sha'awa bakin sa tar yake yadda suke hirar bama zakai tunanin mai muryar bai da lafiya ba, dariya yake sosai yadda yaga Ummu ta taɓe fuska dan ya zaulaye ta

Ummu HaniWhere stories live. Discover now