Tun a hanya Faruk ke faman gwada layin ummu hani sai dai bata shiga sitiyarin motar ya murda bisa titin da zai sada shi da gidan su Ummu din, ransa a bace yake hankalin sa a tashe yake, ji yake kamar yayi tsuntsu yaje ya fadawa ummu ba yaudarar ta yake ba hasalima shi ya jima da tuba.
Wayar sa da ta hau ruri ne yasa shi saurin dauka dan azaton sa ko Ummun ce ta biyo kiran kamar yadda ta saba in taga missed called din sa, sai dai kash! ba ita din bace, Fatima ce dan Allah Aliyu ka tsaya muyi magana nasani na yi kuskure abin da ta faɗa kenan, cikin zafin nama da bacin rai kai kace Fatiman na gabansa ya taka burki Allah yasa babu wani mai binsa abaya da sai haɗari ya afku.
Cikin kausasa murya yace ke dallah malama dakata, karki sake kirana ya fada rai ɓace kafin ya kashe wayar, ya jima yana ta tunane tunane wanda shi kansa baima san takai mai mai mai yake tunani ba kafin yaja motar sa yayi gidan su ummu hani ɗin.
Batayi zaton ganin sa a yanzu ba ta fito zubda shara cikin buhun da suke zubawa a zaure juyawar da zatai ta dora idanun ta bisa nasa da sauri ta zube sharar ta koma cikin gida.
Ya Allah Faruk ya faɗa bayan ya ɗan dungule hannu gami da naushin iska shi a yanzu ma baisan ta inda zai tunkari ummu ba gabaki daya haushin kansa yake ji, ga kunyar ta da ta cika masa rai yanzu kawai ganinta da yayi sai da gaban sa ya fadi, ya jima a tsaye kafin yayi Sallama zuwa gidan su Ummu din.
Tanajin yadda yake sallama tai biris dashi, Bayan da Hajiya ta fito ne tace ya shigo ummun ta mike tayi dakin su inda Muhammad ya bita abaya dan tuni ya fara tafiya abinsa duk da kasancewar sa a ido bama zaka ce ya fara rarrafe ba.
Tun giya Hajiya ta fahinci ummun na cikin damuwa wannan yasa da suka gaisa da Faruk ɗin bata kwalawa ummin kira ba tace kawai ya shiga dakin, aikam yaji dadyi dan yasan da ta kiratan ma ko ta zo bazata ce masa komi ba.
Tana zaune ta rafka tagumi Muhammad na cinyar ta Faruk ɗin ya shiga bata ko motsa ba sai amsa salmar sa da tayi wadda iya labbanta ne kawai suka motsa Faruk din bai damu ba ya matsa kusa da ita ahankula ya samu guri ya zauna har tana jiyi hucin sa dan dab da ita ya zauna.
Ɗagowar da tayi da zummar yi masa masifa sai taga duk yayi mata kwarjini wannan yasa tayi ƙasa da idon ta kawai ba tare da ta ce komai ba, ya fahinci ta ɗan yi la'asar cikin sanyar yiyar murya can ƙasa yake magana dan baya son Umma taji wani abin.
Ummu Hani ya kira sunan ta a nutse bata amsa ba ta ɗago ta kalleshi kafin tayi ƙasa da idon ta, bai damu da rashin amsawar ba ya ci gaba.
Nasani yanzu kin tsane ni anma inason dan Allah kimin adalci ki yadda dani ki sake tunani, wallahi tun da nake ban taɓa kokarin cutar da ke ba, ni har raina wallahi sabida Allah nake son ki ki fahince ni.
Miƙewa tayi kafin ta ce Adalci dai kake so in ma ba, to abu ɗaya ne shine inaso ka daure ka taimaka ka sake ni.
Da hanzari ya kamo hannunta wallahi ummu bazan iya sakin ki ba, kedin rayuwata ce, kedin kin riga kin zama wani sashen na jiki na, ke ce farin ciki na, ki fahince ni wallahi video din da kika gani yafi shekara uku ki yadda dani.
Taɓe baki tayi kafin ta hau ƙoƙarin kwace hannun ta yayin da shi kuma ya riƙe su gam ganin yafi ta karfi yasa ta kurma ihu cikin kuka na ce ka sake ni ta faɗa rai aɓace.
Da sauri ya saki hannun ta tsugunna tasa kuka shima kukan yasa ganin haka yasa ta miƙe ta share hawayen ta, kafin ta ce Malam zoka bar mana gida ta faɗa, bai ce komai ba ya goge hawayen sa da baisan sanda suka fara zuba ba yayi waje.
Duk abinda suke Hajiya najinsu sai da ya fita sannan ta shigo ɗakin tayi ta rarrashin ummu din kafin ta fara tambayar ta mai ya faru ganin taƙi faɗa yasa ta koma yi mata nasiha.
Shiko Faruk ya jima a mota kafin ya iya jan motar ya bar gun shikam ko mai ummu zatayi wallahi bazai sake ba ya fada a ransa.
Da mangariba bayan yayi Sallah gidan su ummu din ya koma kamar dai ɗazun bai samu wata fuska ba kukan dai ta sa masa sai dai shi yanzu ya daure baiyi kukan ba sai hakuri da yayi ta bata.
Kusan tun daga ranar kullum sai yazo sau wurin uku ko hudyu, kwata kwata ma ya fita sabgar ta in yazo in tana gun abinci zai ɗauki Muhammad ya shige cikin gidan su, in kuma tana ciki zata shige daki shi kuma yayi zaman sa tsakar gida su sha hirar su da Hajiya da kuma su Aisha.
Yauma kamar kullum ummu na zaune cikin ƙannen ta suna ta dariya Faruk ya shigo ta miƙe gami da ɗaukar Muhammad taja ƴan biyu sukayi ɗaki suna shiga Hasana ta kwace hannun ta gami da fitowa ta faɗin ga Baba, Muhammad ma kuka yasa ta dire shi yabi bayan Hasana Haushi ne ya cika ummu hani ,Usaina ce kawai tazo gefen ta ta zauna.
Tana ɗaki tana jiyo hayaniyar su cikin farin ciki sai rarraba musu tsaraba yake, a fusace ta fita da zummar yi masa masifa Hajiya ta ce Ummu kiyi ma Faruk godiya fa baya gajiya da hidima.
Rai aɓace ummu hani ta kalleshi ta ce angode ɗaga mata gira yayi gami da sakin murmushi kawai takaici ya cika ta juyawa kawai tayi ta koma ɗaki.
Tun Ummu hani na basar da faruk gami da tashi in ta ga ya shigo har ta gaji dan ta fahinci abun nasa bana kare ba ne tunda kullum in ya tafi aikin da ta tashi ta bari sabo yake dawowa wannan yasa take zaman ta tai aikin ta.
Tun amsa sallama ke haɗa su har ta kai ta kawo takan gaishe shi wannan yasa ya kuma dagewa wurin zuwa burin sa shi kam ya samu yarin yar ta dena fushi dashi.
Zaune yake suna hira da yayar sa ta ke tambayar sa Ummu hani din yayi murmushi ki bari kawai Yaya ummi na fiku matsuwa yarin yar ta tare kawai ban son in mata dole ne, Harar sa Yaya ummi tayi kafin ta ce so kuma na nawa nan ina ka kawota gida kayi abin da ka so.
Ƙasa yayi da kan sa yaɗan sosa ƙeya, kallon sa tayi na ɗan mintina ni tsorona wallahi karka yiwa ƴar mutane abin da kayiwa Fatima.
Cike da tsoro ya kalleta haba yaya taya kike tunanin ni zan cutar da Ummu hani wallahi bazan iya ba.
Hmm Faruku kenan dafa bakai bane ta faɗa tana kallon sa.
Allah yaya ki yadda dani kuma kunsan inason Ummu hani kuma kunsan bana son Fatima tunda duk da kanku kun sani ni ban taɓa ce muku inason ta ba kullum ma kukai maganar son ta nake ina jadda muku ba soyayya muke ba, Ummu hani kuwa da kaina na roƙa aka je aka nemar min auren ta aka kuma ɗauro auren.
Shiru yaya ummi tayi kan ta miƙe hmm Faruku nifa ban yadda da kaiba zanje kawai in samu Hajiya tayi Magana asamu ku tare dan kar aje yarinyar nan ta samu ciki kaga yau zamu wuce America dole in fita hakkin ummu hani kar in tafi ka yi wani abin......
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...