shafi na tara

784 72 2
                                    


Zuwa isha Ummu hani ta gama soya tattasan ta, ta sa kanwa miya kawai yake jira a haɗa dashi, saukewa tai ta raba biyu ta barshi dan shan iska kamin ta rufe da abin tace shinkafa.

  Tuni ta tafasa naman ta shima ta so ye abin ta, haka ma kifin ta ta soya shi.

  Sai da ta tabbatar ta gama komai, sannan ta zuba wa ƙannenta abinci, ba komai ba ne face Dafadikan shinkafa, cikin naman da ta siyo dan abincin siyarwar ta sanya musu, mutun ɗaya biyu, naman yasa su Hasana suka kasa bacci tun da ta kawo suke murna zasu ci nama.

   Sunaci yaran suna nishaɗi, yara ne ba masu rainuwa ba, duk da cewar rabi rabi ta basu yadda suke cikin farin ciki, ka ce ta ciccika musu kwano ne.

  Kamar ko yaushe ita kaɗan ta zuba ta ci, danma tana gudun mitar Aisha ne da itakam bazata ci ba.

  Ummu Hani na ɗaya daga cikin mutanen da basa son cin abinci sai kayan kwalama.

     Kamar yadda ta saba sai da ta kulle gidan, sannan tai ɗaki dan kwantawa sabida tashin da Muhd ke kamata yasa dole take baccin wuri.

A tsakar gida tabar su Aisha nata hira Kasancewa da wuta, bawai sakata take sawa ba a'a kwaɗone tun ummansu nada rai tasa me walda ya musu yadda za'a iya sanya kwado ta ciki, hakan yasa ummu hani batajin komai take kwanciyar ta ko ƙannen nata basu kwanta ba, dan tasan bazasu iya buɗe gidan ba bare su fice.

  Kamar yadda ya saba, yauma kukansa ne wato muhd ya tashe ta, bata da nauyin bacci tanajinsa ta farka.

   Mama ta fara bashi sannan ta saɓa shi a kafaɗa yai gyatsa kamin ta goyashi yai luf abaya.

  Agogon da ta kalla taga uku saura yasa ta fasa komawa bacci, ta ɗauko kayan fanken data siyo ta hau kwaɓi.

   Ba me yawa ta kwaɓa ba, Gwangwani biyar ta kwaɓa dan tasan ko bai ƙare ba su da kansu zasu iya cinye shi a yini guda.

   Sai da ta gama ta tabbatar ta rufe yadda zai tashi kamin safiya sannan ta koma ɗaki ta ajiye gefenta sannan ta sauko da muhd ta kwantar itama ta kwanta.

   Da sassafe ta tashi sai da ta tabbatar ta haɗawa ƙananan ta abinda zasu ci ta soya musu fanken su, sannan ta ɗi bi kayan suyar ta ta yi soro dan anan take son yi, bata son ta ce cikin gida maza su dinga anfani da haka suna shigar musu gida.

     Tai mamaki sosai yadda duk da kasancewar da wuri ta fara, anma ta fara samun masu fitowa siya, tana zuba wa mutun na farko da yazo siyan na ɗari tana zuba wa tana murmushi har ranta take jin daɗi, dan batai zaton zata samu masu siya ba a yau.

    Zuwa bakwai da wani abin, ƙulli kaɗan ya rage, bata tashi ba su Aisha suka fito yaya mu zamu tafi.

  Tom sai kun dawo Allah ya bada sa'a, suka ce amin ta ciro ɗari ta basu gashi ku raba.

  Aisha ce ta zaro ido, yaya ɗari tai yawa murmushi ummu hani ta yi, kudai kuje ai ku uku ne ina ɗari zatai muku yawa.

  To kawai A'isha ta ce, ta amsa sukai waje ahanya ta samu canji ta bawa biyun ashirin ashirin ta ce wannan zamu ajiye sabida wataran kunsan yaya tunda ta bada, in na tsaya musu yanzu zatai fishi.

   Hakan yayi suma suka ce dan goyon bayan Aisha.

   Kan takwas Ummu ta gama suyar ta tas, ta kwashi kayanta tai cikin gida sai da ta wanke komai sannan ta haɗa ruwan wankan muhd ta kai ɗaki.

   Sai da ta masa wanka sannan ta tashi su Hasana suma ta musu, ta basu abincin su, ta ce su kula da muhd ta haɗa ruwa, me dumi ta shiga wanka yadda take jin jikin ta na ciwo dole tasan sai tai wanka da ruwan zafi zata samu sa'ida.

    Koda ta fito karyawa ta yi ta ce kar su hasana suyi hayaniya ta kulle gida tai kwanciyarta kamin wasu mintina bacci yai gaba da ita.

   Bata farka ba sai wurin goma, su Hasana nata wasa da Muhd ta miƙe ta ɗora  shinkafa kamar wadda zasu iya ci har dare, ta ɗora yadda tasan ko ba masu siye zasu ci abar su.

  Zuwa sha biyu ta gama komai, har miya tana juye wa a kular da ta aro a maƙota ne, su A'isha suka dawo kasancewar juma'a ce yau da wuri aka taso su.

  Aisha tai mamakin yadda yayar tasu tai sauri haka, tun a period ɗin karshe take burin ata shi suzo su taya ta aiki sai dai har ma ta gama.

  Yaya mai zai hana ki huta ki kawo in siyar inji Aisha

  Ce miki nai nagaji, kije ki zuba muku abinci in kunci ku kwashe kayan ɗakinku ku dawo dasu ɗakin mu, ku gyara shi kar muje matar tazo bamu gyara ba ummu hani ta bawa A'isha amsa.

   Tom shikenan Aisha ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaukan kula guda, bara mukai miki soron sajida tai saurin ɗaukan ɗayar sukai waje.

     Yauma yaran cikin farin ciki suke dan ummu tasa musu kifi, gashi kuma da miya.

   Aisha da sajida ne suka hau gyaran ɗaki inda Khairiyya ta goya muhd su Hasana sukai soro gurin ummansu kamar yadda yanzu suke kiran yayar tasu, bayan sun gama cin abincin nasu.....

Ummu HaniWhere stories live. Discover now