Kwana biyu bana jin daɗi ga haushin gogewar da yai yasa bana rubutawa
Koda suka koma gida Umman Bashir tai ta surfa masa masifa, bai ce komai ba ganin yai shiru ta ce ya maidata mahaukaciya, wato ga ta tana magana yai burus yaƙi cewa komai.
Umma dan Allah me kike son ince kince in fita sabgarsu na ce to, yanzu kin dawo kince in auri Bushira, naji zan aure ta, anman in har ke zaki min komai ki kuma ci damu.
Tunzira ta kuma yi wato ka mai dani yar iska, inma aure in kuma ci daku in ita waccan yar iskar ce, ai bazaka ce ayima aure ba nasan da kanka zaka nema kayi.
Ni ai bance inason aure ba Umma, Sannan mu ba soyayya muke ba, koda inason ta ban shirya surenta anan kusa ba.
Kinsan banda hanyar samu sai ta kanti duk, da cewar nawa ne anman taima kawa akai aka ban, inna dauko aure dole in raunana shagon, tunda kuɗin ciki zan ɗiba in ya zamto na ɗebe nai aure kinajin Alhaji Badamasi zai kuma ban wani jarin ne.
In ada ni kaɗai ne na ɗauko mata dole inci da ita, shekara ɗaya ta haihu wani nauyin ga naku.
Bacin haka ga karatu na kinsan da kantin nake iya samun kuɗin tafi dashi, inna rusa shagon waye zai bani na kuɗin mota in Alhaji zai biyan na makaranta bazai juri bani na mota ba kinsani.
Shi yasa in zakimin auren ni bazance komai ba.
Shiru Umma tai kamin ta ce tom shikenan, naji kaje sai ka shirya ɗin aman ka sani wallahi wallahi ko magana ka kumawa yarinyar nan ban tafe ba.
A firgice ya ɗago ya kalleta, eh kamaji da wai ni bazan laminta ba, bakuma zan taɓa janye batuna ba fuuu tai ɗaki.
Bashir ya jima agun yama kasa motsi, juya yadda zai iya zama da sabarwa kansa rashin yima Ummu hani magana yake, yadda kunnuwansa suka saba da jin muryarta idanunsa suka saba da kallon kyakkyawan murmushin ta.
Yafi minti talatin kamin ya iya tashi yaja ƙafafunsa daƙyar yai ɗakinsa ransa babu daɗi.
Tunda ya shiga ɗaki bai fito ba, yama rasa mai yake tunani da mai yake damunsa.
Washe gari ummu hani batasa ran zuwansa ba, duk da abin na ranta ta kuma damu duk da ba son sa take ba anman tasaba dashi, aka ce sabo tirken wawa, mutuncinsa da karamcin sa na daban ne, hakan yasa yake da mahinmanci agareta.
Haka tai yinin ranar sukuku, sai dai ta basar dan tun jiya ta fahinci su Aisha na cikin damuwa, kan abin da ya faru batason su fahinci rashin kwanciyar hankalinta su kuma damuwa.
Ranar juma'a tana goye da Muhd zata kasuwar sharaɗa dan siyo kayan miya, da yake su Aisha na gida an hutu Aishan ce ke zaune gun abinci hakan yasa ummu hani ta samu faragar fita tun kan yanma tayi.
Hangen Bashir da taine yasa ta faɗaɗa murmushin ta, ta ɗan ƙara sauri dan ta taddashi su gaisa dan ita a saninta ummansa gidansu ta hana shi zuwa, ba yi mata magana ba.
Shiko hangota da yadda take murmushi duk sai yasa yaji wani iri, abunda ke ransa ya taso, yasan indai ta matso dab dakyar zai iya jure rashin mata magana, in kuma yai banza da ita abin zaifi masa ciwo.
Da hanzari ya shiga Masallaci duk da alwala zaiyi ya fasa.
Ita kuwa ummu ɗan tsayawa tai, tabbas yagan ta ko dai bai gane ni ba ta ce ta faɗa aranta, girgiza kai kawai tayi, tai gaba yana hangenta ta taga wani abu ya tsaya masa a wuya umma bata kyauta masa ba, ya ce ya fito yahau alwala ransa a cunkushe.
Duk ran ummu hani babu daɗi kawai ta basar ne dan tana da yaƙinin yaganta haka tai siyayyar ta dawo gida.
*******
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...