39

431 47 4
                                    


Fatima ce zaune agaban Dadin ta dan amsa kiran da ya yi mata, Fatima ya kira sunan ta wannan yasa gaban ta faɗuwa dan ta jima bata ji ya an baci sunan ta ba sai dai ya ce Baby na.

A nutse ya ce alfarma nake son kimin jiya munyi waya da Abban ku wato yana nufin mahaifin su Faruk, gaban Fatiman ne ya cigaba da faɗuwa tsoron ta kar Dady ɗin yace alfarmar ta janye daga auren Faruk yake nema wanda ta sa ni bazata iya wannan alfarmar ba.

Jiya munyi waya da shi yake faɗamin ya miki miji yanason nanda abinda baifi wata ba zaki tare.

Ahankula tayi ajiyar zuciya dan taga alamar Dad bai san waye aka bata ba, a nutse ta ce shikenan Dady insha Allahu zaka same ni mai biyayya.

Daɗi ne ya cika Dady yasan halin Fatima da rikici bai tsammanin zata amin ce ba, albarka yasa mata kafin ya ce yanzu dai kimin lissafin duk abin da kike so zan ce masa ya turo angon ku gana, zan kuma yiwa antin ku magana kan abinda ya da ce asiyo.

Godiya Fatiman tayi ta zubawa gami da ƙoƙarin ɓoye murnar ta tasan tunda Abban yaƙi faɗawa Dady ko wa ya bata baya son ya sa ni ne se an ɗaura aure wannan yasa itama bata nuna tasan zancen ba.

Koda ta koma ɗakin ta gado ta faɗa cike da farin ciki, wayar ta da ke ruri yasa ta ɗauka ba tare da ta duba me kiran ba ranta tas take jin sa.

Sallamar da yayi cikin muryar sa mai cike da kwarjini yasa ta amsawa rai a bace, mun tashi Lafiya Nasir ya tambaya.

Lau kawai ta iya cewa kafin ta ce irin wannan kira da sassafe haka lafiya dai, yaji babu daɗi ya dai daure kafin ya ce daman faɗa miki zan yau zan tawo, to se ka dawo ta faɗa a hasale.

Har ta kashe wayar ta kuma kiran sa, Ko aje wayar baiyi ba, idanun sa na kan wayar baima san mai yake tunani ba kiran ya shigo sanin masifar ta yasa da hanzari ya ɗaga.

Yawwa murna zaka tayani nanda wata guda zan zama matar wani ta faɗa cike da murna.

Ransa ya sosu gabansa ya faɗi ahankula ya ce to Allah yasa albarka ya kashe wayar.

Hawayen da ya zubo idanun sa yasa Ayatullah da ke gefen da sa dariya, wallahi mutumin nan kana ruwa wai mace kakewa kuka macen ma ragowar wani.

Yaushe nayi kukan inji Nasir yo ai gwanda ni mutun nake so, kai kuwa baka san yarinya ba karshan ta ma a mafarki kuka haɗu, inaga ma aljana ce amma ka bi ka ɗorawa kanka masifa.

Murmushi Ayatullah yayi yo ni yaushe na faɗa ma ina sonta kawai na kasa mantawa da ita ba kuma so bane ina mamaki ne yadda yarinya karama irin ta ta iya haihuwa.

Dariya Nasir yayi kaji dashi shi yasa ai harda zana ta, ko baka yadda ba son ta kake, ni kaga bari in wuce ai mun gaisa kar jirgin da zan shiga ya tashi.

Aikam dai ban gode ba yau kwanan ka nawa anan sai yau zaka wani zo shima agaggauce.

*********
Shiko Faruk bayan barin sa gidan su ummu hani da takardun Salma washe gari da wuri ya shirya cikin shaddar sa sky blue, yasan alokacin da ya shirya Umman su lazimi take Abba kuma yana masallacin cikin gida wannan yada kawai ya fi ce yana son yin abubuwa da yawa asafen nan.

Kai tsaye Buk new site ya wuce, senate building ya nufa, inda aka tanada dan parker motoci ya aje motar sa inda yayi office din professor Bashir Umar wanda shine matsayin Registerer wato mahaifin su Umar aminin sa.

Sectary din sa ne ya masa iso zuwa cikin office ɗin.

Mutumin na zaune yana tulawar Alqur'ani kusan ya zame masa ɗabi'a in babu komai agaban sa babu kuma baƙi yana bitar karatun Alkur'ani ne.

Sai da ya kai aya sannan ya ce a'a Faruku kaine a office din fatan dai lafiya ya faɗa lokaci guda cike da kulawa fuskar sa sanye da murmushi.

Murmushi Faruk yayi ya ɗan rissina ya gaidashi mutumin ya miƙo masa hanu a'a salamun Alaik suka gaisa.

Faruk ne ya miƙo masa takaddun Salman yana faɗin daman alfarma nazo nema, Admission ne ta ci jamb din ta sosai sannan post utme ma haka, to first list ya fito bata samu ba na ce bari inzo kafin a fidda second list.

Karɓa dattijon yayi yana dubawa, hakkun kam ta ci, to abinne da yawa kasan masu neman Buk da suka cancanci adauke su sun ninka adadin da makaranta ke buƙata.

Bari in ma deputy register magana , ko da shike bari in duba list ɗin da ya kawon jiya jibi muke sa ran fidda sauran list ɗin.

Jamb number din ta da post utme Number ya dauka yana sawa cikin list din da zasu fitar sai ga sunan ta.

Kaga ikon Allah anma bata Admission tana cikin second list, an bata optometry godiya Faruk ya hau yi, Dattijon yace No karka damu ta cancan ta ne ko baka zo ba sunan ta zai fito.

Murmushi Faruk ya yi kafin ya ce kuma zuwa yaushe zasu fara registration?.

Eh to gaskiya bamu tsayar ba se an fidda calendar anma dai bazai kai February ba.

Oh anma kusa inji Faruk eh to gaskiya an kusa prof. Ya bashi amsa.

Ko ita ce sirikar tamu prof ya tambaya murmushi Faruk yayi a'a ba ita ba ce, sai ta tare nake son ta fara karatun ita wannan yar uwar ta ce

To Allah ya taimaka, bari in ma printing admission letter din kawai nan Faruk yahau godiya.

Yana tafe a mota akan hanyar sa ta zuwa gidan su Ummu Abba ya kirashi.

Na zo ɗakin ka har ka fita na ɗauka sai 9 kake fita, eh Abba naje BUK ne ok yanzu kazo inason ganin ka tun shekaran jiya nake son muyi maganar muke sabani tom ya ce ya juya motar zuwa gida.

************

Ita kuwa Gwaggo ko da taje gidan Kawu Musa ta tura Ibrahim ɗan gidan kawun kan ya kira sauran kawunnan nasu.

Anyi sa'a mutun guda ne baya nan cikin su.

Tana fara bayanin abinda ya kawota Kawu Bala ya hau faɗa ku me yasa baza ku mata ba, ai kuma yar ku ce.

Cikin hasala Gwaggo ta ce eh yar mu ce anma ku Allah ya ɗorawa hakkin kuyi mata tunda ku dangin ubanta ne.
Wallahi inhar bakuyiwa yarinyar nan kayan ɗaki ba wallahi sai na kaiku ƙara sai duniya taji abinda kukayi kuka bar yara ƙanana cikin wani yanayi suke ciyar da kansu suna rayuwa su kaɗai.

Ko ita babbar koda namiji ce bai ci ace tana kula da wasu ba bare kuma mace ce.

Nan da aka kawo kuɗin Aure da kayan aure nunawa kukayi kune iyayen ta ku ke iko da ita yanzu kuma da akazo batun kaya wato mune iyayen ta to wallahi baku isa ba.

Sai da suka hau sama suka faɗo, faɗa kariris tukunna suka yadda zasu haɗa kuɗi suyi mata kayan ɗaki nanda wata guda.

Koda gwaggo ta tafi Su Kawu sukai faɗa su kam Sule ya cuce su wato suna nufin Mahaifin su Ummu hani, Kawi idris ya ce shi yasa ai lokacin auren akai akai kar ya auro zurriyar gidan Malam Abdullahi tunda shi baida ɗa namiji ko ɗaya yaƙi.

Ai kabari kawai gashi abin da ake gudu mu ya bari dashi, daman dan kar ta tara masa yara mata ne ashe mu zata haifawa, yanzu da maza ne ne waye zaizo yana mana fuffukar munƙi kula dasu.

Uhum ni wallahi raina a bace yake kana lallon yarin tar rashin mutuncin da ta mana lokacin mutuwar uwar ta, yanzu ku kalli yadda yar uwar Tata tazo ta ci mana zarafi.

Ita kuwa Gwaggon koda ta koma gida ta kira Ummu hani ta faɗa mata ta ce musun wata guda da sati biyu.

Farin ciki fal ran Ummu tun daren take son faɗawa Faruk tana jin nauyi wannan yasa ta bari tun da yace zaizo kan batun Admission din Salma ta faɗa masa...

Ummu HaniWhere stories live. Discover now