Ƙarkarewa.

340 43 26
                                    

Kar a manta ayi commenting da yadda aka ji labarin tun daga farko har karshe Nagode.

Kafin a karkare labarin bari in fara da godewa duk wanda suka karanta koda shafi ɗaya ne cikin labarin amma godiya ta wadda take ta musamman ita ce ga wanda sukai hakuri suka bada lokacin su suka karanta tun daga farkon fara littafin kawo yau da littafin ya zo karshe.

Azahirin gaskiya wanda suka karanta sukai sharhi sunfi bani kwarin gwiwa kuma naji daɗi sosai, wanda sukai following ɗina dalilin littafin ina godiya ku ci gaba da following insha Allah zanzo muku da wani littafin soon in baku karanta sauran books dina ba ku duba zaku gansu nasan zakuji daɗin su, wanda basuyi following ba kar a manta ayi following, nagode.

*******

Aisha tashin hankalin ta kullum karuwa yake musan man yau da wanda tasa su dunga biyar Ayatullah din suka turo mata da hoton sa da matar tasa haushi ne ma ya kamata ganin yarin yar da ya aura gata karamar yarinya gata kucaka dan ita kam gani tayi ya cuceta da ya auro wannan bakar yarin yar wannan in kawayen ta da fans din ta suka gani ai sai su mata dariya duk cikarta da ajin ta ace mijin ta ya barta kan wannan, ita dai bata ga kyai a yarinyar ba.

Ana gama shooting ta fito daga gurin a burkicen da take a haka ta yi niyyar tafiya Kano Balkisa ce ta hau yi mata faɗa haba Aisha ai sai ki bamu kunya yanzu fisabilillahi in yan blog da fans suka ganki a haka ai sai su yaɗa kin haukace, hararar ta Aisha ta yi to suyi ko me zasuyi ma masana'antar da nake shirin bari mene dan an yi maganar tsohuwar jaruwama, dafa ta Balkisa ta yi eh duda haka anma dan Allah ko danni da ban shirin barin ta ba ki daure ki je ki shirya kinji Aminiyas, tsaki Aisha ta yi gami da kwafa shikenan ta shige ɗaki har lokacin ranta kuna yake.

Kai tsaye daga hotel din da sukai aikin film din filin jirgi suka rankaya a jirgin ma Aisha mita kawai take ji take tamkar taje ta buge Captain din ita taja jirgin. Suna isa kano kai tsaye Centre din da ake bikin su Ummu suka wuce dan tana da information din komai na bikin, masu gadin gurin ne suka hana su shiga Bakisa na buɗe fuskar ta suka hau murmushi ah ranke dade kune Aishan ma buɗe fuskar ta yi nan suka ruɗe dan mutane sun fi son Aisha sun kuma fi son ganin ta, Aisha ce ta ce bikin cousin ɗina ake mun kuma manta da katin mu, murmushi Mai gadin yayi banda abin nayi zato sunan da mutane suka san ta dashi kenan sabida shine Film ɗin ta na farko ai fuskarki ma gate pass ce Allah ya sanya Alkairi bata ce Amin ba ta shige ciki hasalima a ciki cewa tayi Allah dai ya tarwatsa auren nan ita bata taɓa ganin bikin da aka wani daura aure kan ayi shagalin biki ba.

Tuni ido yai gun Aisha mutane na faman murnar ganin yar film har wasu na kokarin hoto, yayin da ita kuwa Aishan Haushi ne ya kuma cikata hango Ummu hani suna raɗa da Ayatullah, ta kuma raina yarinyar data ganta a yanzu suda cewar yanzun tafi a hoto kyau anma ita tasan tafi yarinyar nan komai tafi karfin kishi da Bahaushiyar mace sai dai Balarabiya. Afusace ta matsa gurin tako dago ummu hani sai dai ta kasa taso ta tsaye dan ummun bata miki ba sai cikin zafin nama ta wankawa Ummu mari tana faɗin ke wacece yau she aka yi ki da zaki aurar min miji, sam ummu bata yi zaton Ayatullah Saurayi bane duda basu taɓa maganar ba dan hirar duniya kawai suke haka kuma ita a rayuwar ta tun mutuwar iyayen su ta maida hankali gurin neman kuɗi bata kallo batasan wasu celebrities ba dan haka har cikin ranta kawai wannan din matar Ayatu ce take kishi wannan yasa ta rasa abinyi ta dafe kunci kawai.

A fusace Ayatullah ya mike ya kwashe ta da mari har sau biyu tako dafe gun tana harar Ummu gami da jijjiga cikin fushi Ayatullah ya ce ke wacce irin shasha shace maras hankali da zaki zo har gurin shagalin bikin yarinya ki ce zaki mareta, cikin tsiwa da ko in kula ɗin marin ta ce Ayatu ni kake cewa shashasha? An faɗa din da ke mece in ba jaka dabba... Ummu ce ta dafe masa baki a'a mijin Ummu bansan ka da zagi ba ka kyale antinnan tamu kishi ke damun ta, Haushi ne ya cika Aisha wato ma Anti me yarinyar nan take nufi ni tsohuwa ce ko me.

Ummu HaniWhere stories live. Discover now