A hankula ummu hani ta matsa kusa da Faruk alokaci guda tana tunanin me zata ce masa.
Hannunsa ta kamo ta shigar dashi mota kafin ta sunkuya dedai kunnen sa tayi magana, juyar da kai ya yi kafin ya ce nifa kome zakice se kin zaɓi ɗaya cikin zaɓin da na baki.
Haba mujin Ummu hani kar muyi haka da kai fa, yanzu fisabilillahi me zaka ce da su Abba in ka dawo gidan nan da zama, ta faɗa ayayin da tayi narai narai da ido.
Yawwa kawai to kizo mu tafi ɗin, zaro ido tayi haba mijin Ummu to su kawu fa ai se suce an maidasu ba komai ba tunda sun riga sun sa rana kawai sai aje ace musu na tare.
Ai ba ɗaurin aure bane Hajiya yanzu fa a ƙarƙashin ikona kike ba su ba ke ɗin mata ta ce.
Nasani ai shi yasa yanzu nima nake ce maka mijin Ummu dan Allah kabar maganar dawowa nan ko binka.
Daƙyar Ummu hani ta shawo kan Faruk ya yadda ba za'ai ɗaya cikin zaɓin nasa ba.
Kallon sa ta yi kafin ta ce bari inje ni inda zani.
Kallon ta yayi what ina zaki dariya tayi a hankula dan tasan Faruk rikicin sa yayi yawa in ta yi wani abun zai iya dawo da maganar zaɓi.
Wai tsaya daman bani kika fito tara ba, ya faɗa rai aɓace.
Girgiza kai ta yi, Allah mijin ummu ko me iya zama dakai se ni, inbanda abinka yaushe mukayi waya har ka ce min kazo da zan fito tarar ka.
Gyaɗa kai yayi hakane fa anma tsaya wai kina nufin duk wannan gayun ahaka zaki unguwa.
Kallon kanta tayi kan ta dubeshi ita dai bata ga wani gayu anan ba.
Gaskiya in ahaka zaki ki kawo takardar kawai in kai mata da kaina Faruk ya faɗa fuskar nan a tsuke.Ina zuwa ta ce ta koma cikin gida.
Hijab din Hajiya dake kan igiya ta sanya Hajiya ta ce wannan ai ya cukurkuɗe ina zaki badai har kin dawo daga gidan su Salman ba.
Murmushi ummu hani ta yi kan ta ce a'a banma je ba, da Faruk na haɗu a ƙofar gida shine ya ke cewa wai nayi gayu.
Dariya Hajiya ta yi kan ta ce ina wani gayu kawai fitar ce baya son ki yi.
Murmushi Ummu hani ta yi kan ta ce shi yasa ai nazo in canja hijabin.
Waje ta yi yana tsaye jikin motar sa idonsa kyar bakin kofa, da alamu fitowar ta yake jira.
Suna haɗa ido suka sakarma juna murmushi.
Bari naje kar dare yamin ta faɗa masa alokacin da taje dab dashi.
Ko inzo in miki rakiya ya faɗa idonsa akanta.
A'a kasan mota bata zuwa layin su in kuma mukaje a kafa zakai ta jira ne a kofar gida tunda zamuyi hira da ita.
Tom shikenan ki gaida ta ki ce mata ban manta da Tukwicin ta ba zan bawa kairi ta kawo mata.
Tom kawai ummu hani ta ce kan ta yi gaba kar ya canja shawara.
A dedai gidan Balaraba mai markaɗe Ummu hani ta haɗu da Bashir akai rashin sa'a suka haɗa ido murmushi ya sakar mata wanda yasa bata da zaɓi face itama ta mayar masa da murmushin.
Da sauri tayi gaba badan batason ganin sa ba sai dan abu biyu, maganar Mahaifiyar sa da kuma auren da ke kanta.
Koda ta yi gaba tausayin Bashir ne ya cika ta duk ya yi baƙi ya rame ya wani zama ɗan ƙauye, kamar ba Bashir ɗan gayu da ta sani ba, Bashir ɗan gayu fari dan duk Farin ɗin ta Bashir yafishi fari zan iya cewa har kyauma kawai gata da kuɗi Faruk yafi Bashir.
Aranta duk sai taji ta damu ko me ya maida Bashir haka oho kwanaki dai taji ance ya auri wadda mahaifiyar tasa ke so.
Shikam Bashir baiji haushin wucewa da Ummu hani tayi bata masa magana ba tunda yasan yadda Umman sa tayi yasani sabida shi yasa Ummu hani taki masa magana.
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...