43

212 11 2
                                    

Ya fa mutu tsohon ya kuma faɗe a rikice, cikin faɗa dattijon da ya kaɗeshi ya ce wai ta ya zaku dinga faman ƙaƙabawa mutun mutuwa ku likitoci ne, sosai hankalin dattijon ke a tashe dan shi kam bai shirya azimi sittin ba, Matashin saurin da ke sanye da kayan College of health ne yace muje asibiti please yanzu in bai mutu ba wannan tsayawa rikicin zai iya mutuwa tunda yana buƙatar taimako.

Kan matashin saurayin yayi wani abu tuni wasu matasa sun suri Faruk da ke kwance cikin jini sun nufi motar wanda ya bige shi.

Kai tsaye asibitin Murtala suka nufa yayin da dattijon ya ɗauki waya ya nemo sunan da zai kira bugu daya aka ɗauka.please Ibrahim in cikin mutanen ka akwai ɗan sanda ka turomin shi asibitin Murtala munyi haɗari ne, ya kashe wayar.

Kusan tamkar tare suke da police ɗin suka ɗinguma zuwa cikin asibitin, tun agun neman gadon da za'a tura Faruk ɗin zuwa inda likita yake nurses suka faɗa musu ba gado shima gadon tura wanda aka kawo ɗin wata mara lafiya ce akai ana sa mata jini.
Ran Dattijon ya ɓaci sosai ayadda yake ganin yaron da ke motar sa in har yana raye to tabbas in sukace zasu tafi subar nan zai iya mutuwar.

Ummu HaniWhere stories live. Discover now