Ummu hani bata san sa'adda ta ce kawu ina zaka da shinkafar nan, kar dai kuce min tafiya zakuyi da ita, ina mu aka kawowa?.
Ta ɗan nisa cike da takaici kamin ta cigaba, Ku baku kawo mana ba tsabar rashin adalci wanda aka kawo mana kun ɗebe, to ya kuke so mu rayu?, tsakani da Allah, ni naɗauka kun rabane tun da ku zaku ɗaukemu.
Tsawa Kawu ya daka mata ke yimun shiru ni ba ubanku bane yai waje.
Aisha ta miƙawa Muhammad, tace kairiyya su ɗebe ta gaban su gwaggo ta bi kawo.
Da sauri tabishi, kai ba ubanmu bane, kai wan ubanmu ne, dan mahaifin mu bazai taɓa barinmu ba gata ba, kuma wallahi in baka kawo shinkafar nan ba yadda bakuji nauyin kin daukanmu ba kuka barmu mu rayu da kanmu, matsayinku na wanda haƙƙinmu ke kanku, toni ma bazan ji nauyin kaiku karaba, kan yi mana sata, karkayi zaton zani hizba, a'a bazani inda za'ai silhu asa dole ku ɗaukemu ba, zani inda duk sai kun danasani.
Lallai yarinyar nan bata da mutunci inji inna, kaga yaya mu aje musu abincin nan. Ni na fasama yin sallar agidan nan inna gaje ta faɗa.
Dire shinkafar yai, har tana zubewa yai waje cikin fishi ummu hani ta sunkuya, ta ɗauki shinkafar tai ciki ta aje a ɗaki.
Gwaggo na shirin fita, ummu tace gwaggo kuɗin da na baki ɗazu shi zaki bani, naga ba'ai sadakar ba kuma muna buƙatarsu, sauran jiyowa sukai suna kallon gwaggo irin kallon zargin nan wato daman anbada kuɗi baki bamu ba.
Jiki a sanyaye gwaggo ta curo kuɗi a gefen zaninta ta miƙawa ummu hani.
Hannu tasa ta amsa ta hau lissafawa, kamin ta ɗago kai sauran dubu biyu ta ce.
Takaici ne ya kama gwaggo bata ce komai ba ta ciro ta bawa ummu hani.
Gida ya watse sai su kaɗai, ran ummu hani duk babu daɗi, tasani bata kyauta ba dai dai in har ba haka tai ba to tayaya zasu rayu susu bakwai ba abinci ba hanyar samu.
Miƙewa tai ta zari buhun hunan tace su Khairiyya suzo su riƙe mata.
Duk ta cikin ledojin ta maida buhun hunan ta zauna tana hawaye tana ɗinkewa.
Shiko kawu tunda yaje gida yake masifa, wai yarinya ƙarama ta ci masa mutunci, bacin shi yamanta da yara ƙanana ɗinne yabarsu surayu sukaɗai.
Matarsa keta tausarsa tana ce masa karya damu yana nan zaune zasu nemeshi, ba mata bane duk tsiya shine maɗaurin aurensu, shima sai ya rama kunji fa maimakon ta nuna masa kuskurensa saima kulla masa wata tsiyar take, mata muji tsoron Allah wallahi.
Tun safe ummu kejin ranta babu daɗi toilet ta shiga ta kulle, ta hau kuka har ga Allah batasan ya zatai da ƙannenta ba, yanzu ace itace uwa itace uba garesu, ita kanta ji take tana buƙatar iyaye, sannan kuma ace ita zata zama dukka biyun ga mutun har shida.
Muhammad tafijin tausayi shi ba abin ta bashi abinci ba, ta lissafa kuɗin da suke gunsu batajin zasu isa ko madarar wata biyu ne su siya masa, wanda tasan tabbas in suka ƙare bata da gun samu hakama shinkafar tasu in ta ƙare tasan bata da gun samu, in su Aisha sun san babu muhd da su Hasana basu sani ba kuka ya kuma kwace mata.
Yaya taji Aisha ta kira ta, wanke fuskar ta tai, ta ɗan nutsu sannan ta fito, kallon ta Aisha tai atsanake kamin tace kinga Muhammad na kuka, ta amsheshi ta goya ta zari mayafi, ba inje in dawo, nan yan biyu suka sa kuka muma ki tafi damu, dan duk da Aisha itama yayarsu ce sunfi shakuwa da ummu hani, rike musu hannu tai, sannan ta dubi Aisha, ki kula da su khairi, zan je in nemo abinda zamu dinga bawa Muhammad, A'isha tace to yaya sai kin dawo, ta ja su Hasana suka fice.Kai tsaye bakin titi sukai inda ta samu adai dai ta sahu sai kasuwar rimi.
Gun masu magungunan hausa tai dan ta yanke shawarar ita zata shayar da muhd, dan in ba haka ba tasan yunwa ce zata kashe mata shi.
Bayani taiwa mai maganin kan abinda take so, wato ta haɗa mata maganin da zaisa wadda bata taɓa haihuwa ba ta samu ruwan nono yazo dan shayarwa.
Tashi matar tai ta haɗa mata komai, sannan ta dawo ta zauna ta mata bayani, nasha da wanka ummu ta biyata suka baro gurin.
Sai da ta siyawa su Husaina yar tsana sabida yadda suka azzaba mata sannan suka samu mota sukayo gida.
Mamaki ne ya cika Aisha ganin yayar tasu da magunguna, tace yaya me zamuyi da magani waye ba lafiya.
Ni ce, ta faɗa a takaice, tai maka ki haɗamin, ki dafan ta nuna mata yadda za'ayi.
Nan da nan A'isha ta haɗa itace kan kace me har magani ya dahu, tas ummu ta riƙe yadda za'a ta miƙe ta shiga wanka, ta ce a dora mata ɗayan bayan ta kwantar da muhd a katifar da Makociyarsu ta basu, dansu basu da komai sai matattun tabarmi tun mutuwar Abbansu ummansu ta saida kayanta duk dan su rayu.....
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...