56

228 32 4
                                    

Ran Ayatullah ya baci sosai kawai ya ki magana ne dan mutumin tamkar uba yake gunsa amma in ba haka ba da tuni ya magantu yarinyar ta ci mutuncin sa sannan ace shi ya yi, shirun da Ayatullah yayi ya bawa kawu haushi cikin faɗa yake faɗin wato ina mana kamin shiru sabida ga dan iska ko a kufule Ayatullah ya ce to mai zakce tunda ita Aisha din bazatai ka karya ba aishike nan.

Ah lallai koda yake ba laifin ka bane laifina ne da na nace sai anyi auren nan na kuma san mai yasa baka so sabida kawai ni talaka ne amma ka sani ni din daka raina haka da Uban naka yake Ayatullah bai kuma tankawa ba Kawu ya gama banbamin sa ya ce ya tashi ya tafi ya kuma tabbatar cewar biki ba fashi nan da wata uku za'a a daura aure.

Ayatullah ya jima a mota ransa ba dadi yanzu sam bama auren Aishar ya dame shi ba face yadda zai naimo ummu dinsa tsoron sa shine to inma ya nemo ta to ya yi yaya da auren ta, yadda yake jin son yarin yar yanzu shikam ya kudiri aniyar ko rokar mijin ta ya sake ta ne zaiyi abu daya ne bazai iya ba shine kisan kai anma zai iya komai dan samun ta matsayin matar sa.

Kusan daga nan ma yawon neman ko zaiga ummu ya tafi sai dai wayam tun yana tunanin ganin har ran sa ya fara raya masa kodai bats dawo kano din bane dan ko mai kama da ita bai gani ba tunda ya dawo.

A gida ma Abban sa kiran sa ya yi ya haushi da faɗan dan mene zaije ys ma kawu rashin kunya yasan in ya faɗi cewae baiyi ba nan ma Abba kuma cewa zai yi ya karyata kawu dole ya daure ya yi ta bawa Abba hakuri jiki ba kwari.

********

Salati Umma suka sa lokacin da suka tabbatar jariran gaske ne Hajiya ce ta fita ta kira Ummu wadda yanzu zuciyar ta ke adake dan yanzu ta kudiri niyar koma mene ya faru kawai.

Umman Salma ce ta ce Yanzu Ummu hani kin mana adalci kenan ko dan mu ba iyaye ki bane, kiyi ciki ki haife duka bazaki iya fada mana ba sam kin ban mamaki wallahi ban taba zaton haka kike ba, ban taɓa tunanin ba iyaye kika daukemu ba.

Jikin ummu ne ya yi sanyi kwarin gwiwar da takejin tana dashi duk sai ta neme shi ta rasa cikin shessheƙa kuke take fadin wallahi ba haka bane har cikin raina kudin iyaye nane kawai ina tsoron mai zakuce ta zaku kallen bansan ta yadda zan gansar da ku cewar ciki ne dani ba kuma cikin na halak ne bansani ba shi yasa na kasa fade nayi zaton zaku gane sai sai yaddar da kukai dani yasa kuka kasa yadda ciki ne dani wannan ya kuma ban tsoro na kasa fada muku ina tsoron bazaku yadda na sunna ba ne.

Ruko hannun ta Umman Su salma tayi ki dena kuka ko duniya sunki yadda dake mu masu yadda ne munsan da auren ki ai ko watannin cikin da haihuwar aka duba watannin auren naki kenan yanzu ki shirya zamu je gidan su Faruk din ko ba komai suga jinin su a kuma gyara rabon gadon da akai.

Amshe hannun ta tayi ta hau girgiza kai gami da durkusawa ta hau rokar du dan Allah ku min gata ku dubi darajar Annabi karku kai batun yaran nan gun dangin babban su nasan in sun aminta nasu ne kwace ce su zawuyi Ni kuma bazan basu ba banson ko kadan Shari'a ta haɗa mu dasu tunda ko kin aminta sukai na halak ne bazan amin ta ba dan Allah ku barmin abuna kaddara ta ce nida su.

Shiru Ummq tayi shikenan Allah ya raya su ya bamu ikon kula da su, Amin duk suka ce banda Ummu da ta Fada a ranta kafin ta shige toilet ta kuma sa kuka duk wannan lefin mutuwa ne da Faruk ɗin ta na raye da shikenan tasan sai sunfi kowa farin ciki zuwa yanzu da ta haifa masa yara ya zama.

Su Aisha sunfi kowa mamakin ganin yaran sai dai kuma ba wanda ya tambayi ya akai ko ke yasa hasali ma rungumar yaran sukai tamkar nasu kowa cikin gidan son yaran yake wannan ya ragewa Ummu damuwar ta sosai.

Sannu a hankali Ummu sunyi wata biyu kenak da haihuwa sai dai ko da wasa ko sai daya bata taɓa fita da yaran ba anma abinka da mutun ake kiwo yanzu ba dabba ba kan kace me tuni unguwar tasu ta dauka an haifi shegu har biyu duda cewar ba wanda ya taba ganin yaran.

Ummu HaniWhere stories live. Discover now