Kukan da Ummu tasa ne yasa dukkan su kallon bakin kofa ba wanda ya tsanmaci ganin ta ba ɗakin ta shiga kai tsaye gun Faruk ta nufa tama mance cewar iyayan sa fa sirikan ta ne hannun sa ta kamo tana kuka dan Allah Faruk ka jikaina karka sake ni wallahi bazan iya rayuwa ba auren ka ba, sakin da zaka min shi ne zai zamto cutarwa a gare ni bawai zama da kai ba dan Allah ka dubi rayuwa ta in har ba son gina kiyayya maras yankewa tsakani na da kai ba kar kayi sakin nan bazan taɓa yafe ma ba zuru kawai ya yi yana kallon ta ran sa yana ƙuna yana ji yake ina ma zai iya ɗauga koda hannun sa ne ya goge mata hawaye sai dai ina bazai iya ba.
Mami ce ta taso ta rungomo Ummun yi shiru kinji Hani karki damu nima ban goyi da bayan sakin nan ba koda kuwa hakan na nufin zaki kalleni a matsayin wadda ta so ɗan ta amma bazan so abin ya masa ba ga jinyar jiki ga na zuciya indai har ina raye bazaki ƙara kuka kan bakyason saki ba in kinga kin rabu da Faruk to keda kanki kika buƙaci ku rabun a wannan lokacin ne ko da ina so bazan iya tauye miki hakkin ki ba.
Girgiza kai Ummu ta hau yi indai ni ce bazan taɓa neman rabuwa da Faruk ba har abada Nagode Mami da kika goyi da baya na.
Dady bai ce komai ba ya fi ce daga ɗakin inda Mami ta bi bayan sa alokacin ne Faruk ya juyar da kansa gami da rufe idanun sa kamar me barci, Murmushi Ummu ta yi dan ta gano fishi ya yi matsawa kusa da shi ta yi cikin da shasshiyar muryar ta da tasha kuka ta ce haba Mijin Ummu bama fishi da juna fa dan Allah kayi hakuri a hankula ya kalle ta ni ba fishi nake da ke ba kawai haushin kaina nake ji kina zaman zamanki nazo na fara sonki ba dora miki wahala yanzu da ban san ki ba da duk hakan bazai yiwu ba.
Kuka tasa ni na ce maka kai ɗin wahala in kamin haka baka kyauta min ba, kai ɗin har abada rahama ne a gareni, naji daina kukan and give me a hug matsawa ta yi ta rungume shi.
*******
Shi ko Ayatullah mikewa ya yi yabar gub bayan bacewa ganin sa da Ummu ta yi kai tsaye ɗakin kwanan su ya nufa dan ya gama duty dinsa, bai cewa kowa komai ba ya faɗa gadon sa ko yunwar da yake ji tuni ta bar shi yama rasa mai zaiyi tunani jin sa yake tamkar wani sabon arne wai ya rasa waye zai so sai matar wani da ya tuna haka sai ransa ya baci Astagfirullah kawai yake aransa.
Muryar Abraham ya ji na faɗin mai ya faru zaka sha tea din je in miko ma , No bazan sha ba ya ce taɓe baki Abraham ya yi kawa kanka ya ce sannan ya juya ya ci gaba da duba littafin medical din da ya ke dubawa.
Na gano ta Ayatullah ya ce bayan ɗan shiru da sukai a hanzar ce Abraham ya juyo kuma ba aljana ba ce ko? Ya tambaya eh Ayatullah ya ce kawai, I knew it mutun ce, kwafa Ayatullah ya yi but she's married with kids, what Abraham ya zaro ido.
Kaima ka yi mamaki ko ban san me zan ba just how can I be in love with somebody's woman that fact I annoyed me na rasa mai zanyi.
Dariya Abraham ya yi sai me dan tana da miji kawai kaje ka kwatota win her love and make her yours let her make another choice, you most be mad Ayatullah kawaj ya ce kafin yabar ɗakin ransa ba daɗi duk da chan wani ɓarin na ransa na faɗa masa shi ba Zina zai ba Abraham yana da gaskiya ji yake a ransa in har zai iya jawo hankalin ta ta nemi saki ta dawo tasa nothing matters.
********
Fatima kam hankalin ta duk baya jikin ta tun tafiyar su Faruk danma tun batun auren Farun ɗin da ta janyo Abban ta ke fishi da ita duk dauriyar ta ta kare ta yanke shawara kawai zata je ta samu Abban ta rokeshi ya bar ta taje ta dubo Faruk ɗin dan bata son ya warke ya dawo bata je ba bacin haka ma tasan hankalun ta sai ya fi kwanciya in har tana ganin ta.
Abban na ɗaki ta same shi ba yabo ba fallasa suka gaisa kasa ta zube tana kuka nan da nan hankalin sa ya tashi ya taso inda ta ke haba babin Abbanta mai kuma aka miki, ɗagowa ta yi cikin hawaye ta ce ba kai ne Abba ka ke fishi dani ba, share mata hawaye ya yi a'a ni kam baba fishi da baby na ke ce dai baki fahin cen ba.
To Abba ka hakura faɗa a shagwabance murmushi ya yi dama baki mun komai ba, itama Murmushin ta yi tom nagode Abba kuma dan Allah yau she zanje duba Faruk pls don't say No dan Allah Abba ta faɗa tana riƙe da hannun sa.
Dama gobe nake son muje dukan mu na samar mana jurgi zamu bi na safe, rungume shi ta yi nagode Allah dariya yayi ki cigaba da masa addu'a ki je ki haɗa kayan da zaki ta fi su ɗin, Tom Abba Nagode ta ce kafin ta bar falon.
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...