Yaron na fitowa riƙe da takardu ta miƙe, Congratulations Mijin Ummu 🤣🤣.
Genotype dina AA blood group A positive.
What! yakalle ta cike da Takaici wato daman kin sani.
Eh mana kawai na kyaleka ne in dan ganya zakayi.
Lalle yarinyar nan, zonan ya faɗa, ta ɗan matsa tana dariya takar dun ya bude kamar yadda ta faɗa haka ne, haka kuma babu wata matsala HIV dinma babu me ita a tsakanin su Farin ciki ya cikashi.
A mota suna tafe suna hira ya ce to me yasa baki damu da batun HIV ba?, murmushi tayi kawai nasa araina babu me ita cikin mu, daman Genotype ne kake As to nasan ba ita bace ni, shi yasa na yadda da me raina ya ce na ɗanyi nishaɗi.
Murmushi yayi ya girgiza kai, ai ki bari kawai ɗazun wallahi daurewa kawai nayi, dan ji na dinga yi kamar ama fasa in sace ki in gudu in yaso Dady dole ya hakura, daga baya kuma da kika kuma ƙonan rai naji kodai inna sace kin in haɗa da zane ki.
Dariya tasa tace oh wayaga miji da sace matar sa🤣🤣.
Gida ya sauke su namma sun taɓa hira kafin ya wuce gida. Sunyi Ummu ɗin zata zo ta gaida Hajiyar sa shima dakyar ta amince sai da yayi ta roƙar ta ƙarshe ta ce shikenan in zata kasuwa zata biya
Yai yai ta yadda yazo ya kaita ta ce bata san zance ba.
*******
Faruk na sauke su Office ɗin Dady ya wuce, ko gida Baije ba ya kai masa Dady yaji daɗi dan shi kansa har tunanin ta yaya zai iya shawo kan ɗan nasa ya yadda ya saki matar tasa in an samu akasi yake.
Ko da ya koma gida ma da murna ya ƙarasa ɓan garen mum ya sanar mata, itama ta Taya shi murna nanma yake faɗa mata sunyi da Ummu zata zo gai da ta, tayi murna da hakan dan su in tasu ne ko ba kaya akawo yarinyar dan dai kawai basa son nuna zagewa danginta suyi tunanin kamar ƙoƙarin siyen ta suke.
Ka faɗawa mai gadi sunan ta in tazo ya barta ta shigo, kaga mu muna ciki ba sani zamuyi ba kar ya hanata To ya ce gami da miƙewa.
A'a ina kuma zaka Hajiya ta tambaya zanje in faɗa masa ne girgiza kai hajiya tayi tana murmushi yo to yanzu zata zone ta tambaya.
A'a ya ce kawai dai naga gwanda in faɗa masan to kawai ta ce ta shige ɗakin ta.
Baba me gadi na zaune najin radiyo Faruk ya gai dashi, kafin ya ɗan zauna su taɓa hira ya ce yawwa Daman zan faɗa maka ne matata zata zo sunanta Ummu hani in tazo abarta ta shigo.
Murmushi Baba me gadin yayi to shikenan, ni na ɗauka ma ta kusa tarewa? me gadin ya tambaya.
Eh to muna sa ran wannan watan ko wani Faruk ya bashi amsa.
Tom Allah ya kaimu ya sanya alkairi Baba me gadi ya Faɗa, Faruk ya ce amin kafin ya miƙe ya koma ciki yau kam yayi missing ɗin gurin aiki dole ya haƙura da zuwa.
Yadda Faruk ya dame ta kan cewar ya fa faɗawa Mum ɗin su zata zo yasa ta daure duk da kasan ranta tanajin be dace ba, dan dai kawai ta faranta masa, dan ko Hajiya bata faɗawa ba bare ƙannen ta, ta nufi gidan su Faruk din da zummar daga nan zata wuce kasuwa.
.Ba wata wahala mai gadi ya barta ta shiga, dan tana cewa Ummu hani ce ya ƙara faɗaɗa murmushin sa, sai dai kuma Hajiyar ta fita sai ki kira mai gidan naki ya faɗa mata dan shima ya fita aiki.
To ta ce bayan ta shiga masu aiki suma sukayi ta nan nan da ita, sai yanzu take ƙara kissima girma da iko na Allah da ya bata Faruk a matsayin miji, matsayin su kwata kwata ba ɗaya bane.
Ruwa tasha kafun ta kira ta faɗa masa tana nan fa, ruɗewa yayi ya kashe kiran ya kira masu aiki kan su kakkawo mata abinci yace ta jira gashi nan zuwa ita Hajiya tayi tafiya anma zai kira yayar sa da ƙanwar sa to kawai ta ce ta aje wayar.
Kamar minti goma sha biyar kuwa sai gashi yayi ta nan nan da ita, shine har da zagaya wa da ita cikin gidan duk ya nuna mata ɓan garen kowa.
Ƙarshe shine inda zasu zauna.
Gurin yayi mata kyau koda ace iya haka aka barshi ya ishi mutun rayuwa, fita yayi ya ɗebo kayan abinci kafin su zo ataimaka a girkan me zanci.
Kallon sa tayi da mamaki ni da zan tafi, murmushi yayi Allah kinason in kulle ki anan inje in faɗawa hajiya kin ce kin zo kenan.
Ware ido tayi rufan asiri nida Bama tasan nazo ba.
Madafar ta nufa inda ta hau ƙokarin dafa masa, taliya ta dora inda ta fara gyaran kifin da ya kawo dan tasan shi yake so asa tunda ya kawo.
Ba wani girki me wuya tayi ba sai dai kafin wani lokaci falon ya cika da ƙamshi, dan Ummu gwana ce, kasa jurewa Faruk yayi ya taso ya shigo.
Ya jima yana kallon ta kafin ya ƙaraso inda take, hannayen sa ya ɗan zargo jikin ta hakan ya tsorata ta ta ɗan tureshi mene hakan ta faɗa.
Murmushi yayi ba komai kawai kwakwalwa ta ce ta ayyana min haka zan dunga takura miki in kika tare.
Murmushi kawai tayi ba tare da ta ce komai ba.
Me za'a taya ki dashi?, Ya tambaya ba komai ta ce, Nama fa gama ta faɗa gami da juyowa sauri tayi ta meda kanta inda yake,batai tsammanin ganinsa ahaka ba singlet ce a jikin sa da short, ko yaushe ya cire kayan jikin sa oho ta faɗa aranta.
Taimaka mun da wannan ta nuna masa plate ɗun da ta zuba abincin ya taso ya ɗauka sukayo waje maimakon dining a falo ya dire, ya je ya dauko ruwa da lemo ya dire musu.
Bisimillah ya ce.
Kallon sa tayi nifa bance inajin yunwa ba.Dariya yayi mata in kuma kinga kin bar gidan nan sai mun cinye ya faɗa bayan ya matso da abincin kusa da ita.
Yanaci yana murmushi duniya ji yake yafi kowa sa'a ga shi ya samu mace kamila ga iya girki abincin ya masa daɗi.
Tas suka cinye inda ya daɗo musu shima suka cinye, Ummu na wanke kwano ya shigo riƙe da waya ga Anti Farida kuyi magana.
Rokarta Faridan tayi kan ta jira yara take jira su dawo yanzu zata zo samun kanta tayi da kasa cewa a'a ta ce to, sai da ta dawo Falo sannan ta kira Hajiya a waya kan zata biya ta gidan su ƙawar ta Maryam zata jima, to kawai Hajiya ta ce kafin ta ce in baki dawo ba zuwa uku zan fita sai ki amshi makullun a gidan su Walid to Ummu ta ce sai kin dawo ta katsewa wayar.
Kusa da ita Faruk ya dawo ya zauna ta ɗan Dube shi dan Allah ka canja kaya, to yace muje kiga ɗakinmu banza ta masa.
Dariya yasa ya matso kusa da ita sosai, kasa magana tayi kafin ta ce Allah fa nace maka.
Nima Allah na hadaki da shi kizo kiga dakinmu.......
Kar amanta ai following, comment ɗinku shi zai ƙaran kwarin gwiwa
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...