shafi na sha biyu

961 73 1
                                    




Koda su Ayatullah suka isa gida a parking space suka aje motocin su, kamin daga bisani su ƙarasa cikin gida gabaki ɗayan su a main parlour suka jibge, inda Ayatullah yai ciki dan yadda yakejin jikinsa in be wanka ba bazaiji sa'ida ba.

   Sanye yake da Short da singlet lokacin. Da ya fito daga wanka ko da ya fito daga ɗakinsa tsayawa ya yi daga bakin ƙofa yaɗan kalli inda zai sada shi da inda mutan ke zaune ya kalli hanyar dining area shafa cikinsa ya gun cin abincin ya nufa dan yahajin yunwa in yaje hira za'ayi tayi.

   Abinci ne iri iri jere kan table ɗin, food flask ɗin farko da ya buɗe ne yasa wani farin ciki ya ziyar ce, shi gefe soyayyiyar doya ce sai gefe yam ball, kusan second best food ɗinsa kenan, saving kansa ya yi ya zuba lemon abarba me sanyi ya hau ci.

   Tabbas ba abinda yafi gida daɗi inba a gidanba shi baya taɓajin daɗin girki koda anyi irin wanda yake so ɗin kuwa.

    Sosai ya ci duk da ba wani ci ne dashi ba, har ya miƙe ya dawo ya hau bubbuɗe abincin, aransa yanajin daɗi yasan duk dan shi akai inda ace bai zo shi kaɗai ci ba, da haka yan uwan nasa zasuyi ta mita sai ya ci wanda ko wacce tayi.

  Flask ɗin ƙarshe da ya buɗe ne yasa ya koma ya zauna, wow kamshin miyar kukar da ya daki hancinsa, best food ɗinsa daga tuwo sai doya inda yasan da tuwon nan raba cikinsa  biyu zaiyi, but still in ya tafi baici ba yasan bama zai iya magana ba sai tunanin miyar nan me daɗin ƙamshi.
 

  Kaɗan ya zuba ya ci dan mai da yawun sa, sannan ya maida komai ya rife yana ƙoƙarin tashi yaji muryar zainab na faɗin eyye sannu wato nan kazo kana kwashe mana abinci mu ko oho.

   Dariya yai kinga ni yanzu a koshe nake, in kinajin rigima ki bari zuwa gobe in inajin yunwa yabar gun.

  Main falo ya nufa, kusa da Ya Fatima ya zauna yana faɗin kai Alhamdulillah yau na ci abincin gida.

  Gashi can na rage muku kuje ku ci, Zainab da ke ƙokarin zama ta ce, ce maka akai mu almajirai ne.

  Ya Basira ta ce what wai ka ci abincin kake nufi, murmushi ya yi kaina bisa wuya na.

  To baka isa ba inji kadija dole ka ci abinda na kawo bazan wuyar banza ba, to shi kenan Karki damu ai indai naku ne zanci nasu oh oh ne ko ɗanɗano, Zainab ta ce to daman an ce ma ni zan ɓata lokaci ne in wani maka girki.

  Banza yai da ita dan ya bata haushi, ya dubi Mami ya ce Mami gaskiya tuwon da kikamin yayi daɗi sosai, ya dubi yah Fatima nasan ke kikai dangin doya ko.

   Miyar in tayi ragowa asamin a firgi sai in ɗumama gobe.

  Dariya kowa yasa mamin ta ce, to ni ce maka akai ni na ma tuwon, yayar ka ce tayi, komai kagani akan table ɗin su sukayi ba hannuna.

  Wow shi yasa nake sonki yaya, ya faɗa yana ɗora kansa bisa kafaɗar yaya Fatima.

   Ni Bani nai tuwo ba Zaibab ce ta yi,  what ya faɗa da zare idon wasa, haba no wonder wannan abinci ko taste babu, yanzu haka amai ke tasomin ya faɗa yana barin gurin, da sauri Zainab ta sa dariya tabi bayansa.

**********

Da rana ma sai da Bashir me kanti ya zo siyan shinkafa basu wani yi magana ba yadai yiwa ƴan biyu da ke ta gefenta wasa ta zuba masa ya tafi.

   Tana nan zaune ta kusa tashi ma motar da ke ɗauke da kayan Hajiya Balaraba ta tsaya a ƙofar gidan, matar ce ta fara saukowa ta karaso inda ummu ke wato cikin soronsu.

  Cikin mutunci Da girmamawa Ummu hani ta gaida Matar Dattijuwa ce da baza ta gaza shekara hansin da biyar ba.

   Ke ce Ummu Hani ko Ummu tai murmushi eh ni ce.

  Itama matar murmushi tai sunana Balaraba ni ce wadda Alhaji Ummaru ya muku bayani zamu zauna tare.

  Faɗaɗa murmushin ta Ummu hani tai ayya sannu da zuwa, munata saka ran zuwan  ki sai yau Allah ya nifa inji ummu Hani.

   Eh wallahi wasu uzururruka suka tsaidani.

  Khairiyya Ummu ta kwalawa kira itama da ƙarfi ta amsa gami da fitowa tayo waje.

   Ku shiga ki nuna mata ɗakin ita ce wadda nai muku bayani ƙara gaida ta Kairiyya tayi ta amshi jakarta sukai ciki.

  Ɗakin yayi matar ta faɗa duk da ta ci alwashin ko baiba haka zata zauna bare yanzu da ta kuma ganin yaran sai ta kuma tausaya musu, duk da cewar itama abin tausayi ce anman ba kamar su ba.

  Sajida na wanke wanke Aisha na wasa da muhd ta samesu sai taji duk zuciyarta tayi rauni.

  Yaran data zo dasu ne suka shigo da kayan ba wasu tarkace ne da ita ba katifa ce da kayan sawarta da na girki da ƴan kwanuka.

   Tana zaune riƙe da muhd su A'isha suka shimfiɗa mata leda suka jera mata komai.

   Ji take kamar tai kuka, inama ace yaranta ne da farin cikinta sai yafi haka, da take riƙe da Muhd tausayinsa da nata ya cika ta.

   Balara Bata taɓa haihuwa ba, sun rayu da mijinta kusan shekara arba'in da ɗoriya, tun auren ƙuruciya sai dai Allah bai basu haihuwa ba.

  Ya auri mataye duk sun gudu sun barshi sabida baya haihuwa, itama iyayanta sun sha raba auren har aure tayi sau biyu, sai dai Allah bai bata haihuwa ba haka yasa da ta fito a auren ta na uku iyayanta suka haƙura suka kyaleta ta cigaba da zama da mijin ta.

   Lokacin da yake jinya haka tai shekara biyar tana wahala dashi komai nasu ya kare ƴan uwansa duk suka fujeshi  Allah gatansa ita ce gatansa, kullum cikin ci mata albarka yake dalin rashin lafiyarsa sai ritaya tayi da fanshonsa da nata suke rayuwa.

  Itama danginta ba wani ta tata suke ba kowa kansa da yaransa ya sani.

   Lokacin da mijinta ya rasu lokacin ne ƴan uwansa suka fito su ala dole ga masu ɗan uwa kuma magada.

   Ko arba'in ba'ai ba suka saida gidansa suka bata tuminin takabar ta, tayi kuka iya kuka dan gidan ita dashi sukai wahalarsa kasancewar ba sheda dole ta haƙura da shi tanaji tana gani tabar gidan.

  Gidan su ta koma wanda ya ke yanzu fal da ƴan uwa kasancewar tun rasuwar iyayansu ba'a raba gado ba yasa ba wanda ya kore ta, dan tana da gado agidan sai dai kuma kowa baya baya yake da ita, dan gani suke tamkar zata ɗora musu nauyi.

  Alokacin ta kuma kokawa rashin haihuwa, gashi dai ƴan uwanta ne uwa ɗaya uba ɗaya, anman gudunta suke sabida karta zame musu lalura yanzu da ace tana da yaranta kome take ciki haka zasu kula da ita....

Ummu HaniWhere stories live. Discover now