Koda sajida ta kaiwa momin walid kulolin cewa tayi su aje agunsu kawai ita daman ba anfani take dasu ba, inma ta aje mutuwa zasuyi akawai, in yaso daga baya in sun samu kuɗi sosai sa biya ta.
Koda ummu Hani ta dawo suka faɗa mata da kanta ta shiga taima momin walid godiya, dan daman botiki guda ta iya samu ta siyo kuɗin sun yanke mata, dan ta biya ta ƴan gwanjo kowa cikin ƙannen nata ta siyo masa riga guda ta sanyi, duk da zafi ake ganin anata bonanza naira ɗari yasa taga bara ta siyo tasan in sanyi yazo zasu kai ɗari biyar biyar.
Kamar jiya adaren Ummu hani ta soya komai cikin dare ta kwaɓa fanken ta kamin ta koma bacci.
Da asussuba ta tashi ta soya na ƙannen ta, ta ɗora ruwan koko da ruwan wankansu a ƙatuwar tukunya sannan ta ɗebi kayan suyar ta takai soro.
Gida ta dawo ta gyara ko ina sannan ta koma ɗaki tana jiran ruwan kokon yayi ta dama.
Kusan shida saura minti biyar ta kammala komai ta tashi su Aisha dan su shirya zuwa makaranta kamar kullum ɗaya cikin su ce ta shiga wanka inda biyu ummu ta zuba musu karin su suna ci.
Shida da rabi Ummu ta buɗe gida ta ɗora manta akasko dan suya.
Kamar jiya Bashir me shago ne ya fara zuwa gaishe shi ta fara yi, kamin ta ta ce dan Allah ko zaka ɗan jira yanzu na ɗora kasko ba komai ya ce sai dai bana jurai tsaiwa.
Murmushi tai ta tashi daga kujerar da take ta ce ga wannan ba in ɗauko wata, to kawai ya ce yaja ya zauna.
Tana shiga taga muhd ya tashi yana kuka da sauri ta amsheshi ta hau rarrashi sai da ta bashi mama ta goya shi jikin filo ta jingine a bango tuni yai luf duk da bai bacci ba.
Sai a lokacin ta tuna tafa ɗora kaskon mai da sauri tai waje riƙe da kujera.
Turus ta tsaya ganin Bashir na jefa mata cikin mai har yai kasko ɗaya da alamu ma an siya.
Da sauri ta ƙara tana faɗin dan Allah kayi haƙuri wallahi jaririnmu ne ya tashi shine na manta na ɗora mai.
Juyowa yai ya sakar mata murmushi karki damu na iya aikin gida ai itama murmushin tai eh duk da haka kayi haƙuri.
No ni nasa kaina Aisha tazo zata soya ba ce ta je tai shirin makarantar ta kinga anyi ma ɗari da hamsin tom mungode ta ce.
Kujerarsa yaja gefe ita kuma ta aje tata tana suyar yana kallon ta, tausayin yaran yake ji tun lokacin ma iyayansu nada rai bare yanzu da suke rayuwa su kaɗai lokacin da ummansu ta rasu tinaninsa ya zasu rayu sai dai kasan cewarsa namiji bakuma su taɓa magana ba yasa yaketa tsoron zuwa yaji ya suke dan gudun kar su yaran da jama'a suyi tsammanin yanason yai anfani da rashin iyayansu ya cutar dasu.
Lokacin da su Aisha suka faɗa masa zasu fara sana'a daɗi yaji aransa sai yaji yana son ko yaya ne ya taka rawa a cikin masu yi masu ciniki.
Akaskon da ta juye ta zuba masa harda ƙari yana kallo amsa yai ya maida ƙarin kinga ni wannan ma da badan akwai Bala ba yamin yawa, karki damu banyi dan ki biya ba ya faɗa gami da yin waje murmushi kawai tayi bata taɓa sanin cewar Bashir nada kirki ba sai yau dan ko dariya baya yi.
Aisha da sauran ƙannen ta ne suka fito yaya mu mun tafi ta ce tom Allah ya bada sa'a suka ce amin ta basu kuɗin makarantar su suka wu ce.
Ta kusa tashi Kursum Babbar ƙawarta ta zo sanye ta ke da uniform murmushi suka hau yiwa juna.
Ummu hani ta ce Malama ki ta fi makaranta, kin kusa makara, Kursum ta ce zuwa nai in kuma jin ra'ayin ki dan Allah Ummu Ki daure ki komo makaranta, mutuwa bayana nufin ƙarshen rayuwar mu ba.
Uhum Kursum na rasa yadda za'ai ki gane, inna koma makaranta inyi yaya da Muhd da ƴan biyu.
Kai Ummu sau nawa kikeson in faɗa miki ki kawowa ummanmu su in aka tashi sai ki ɗauke so.
Tom yanzu sa ace na kai mata su inna dawo me zan basu, su dasu Aisha ita ma Umma nema take, ku goma sha uku ne agabanta, sannan a ce na ɗora mata nauyin mutun bakwai.
Karki damu aƙalla nayi hizifi talatin da wani abin, na hadda ce nayi primary nayi jss ss dinma na fars, na iya karantawa in rubuta ya isheni rayuwa wallahi har raina ina gode ma Allah, wasu basu iya yadda nayi ba, inda rabona wataran zan koma duk daɗewa shi girma baya haha neman illimi.
Shi kenan ummu ba in wu ce innadawo zanzo ganin ɗanmu, sukai murmushi baki ɗaya Kursum tai waje inda ummu hani ta bita da kallo kanta ta ɗaga sama dan shanye hawayen da suka biyo mata dan ita yanzu tasa ma ranta babu abinda zaisa tai hawaye, indai kan kula da ƙannenta ne, tasan karatu nada anfani ada shine babban burin ta anman yanzu yadda ƙannenta zasu rayu rayuwa me kyau cikin tarbiyya ingantacciya shi ne babban burinta.
Koda ta koma gida su Hasana ta tasa tai musu wanka ta basu koko da fankensu sannan tayi nata wankan kamin ta zo taima muhd.
Zaune take tanama muhd wasa yan biyu zagaye da ita sunata sheƙa dariyarsu tuni ta nemi damuwar ɗazu ta rasa itama biye musu tai suke ta shirmensu.
Yau batajin bacci hakan yasa ta ɗora miya da wuri kan goma ma ta kammala ta bari sai sha ɗaya ta ɗora shinkafar.
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...