Bakwa voting ba kuma kwa commenting, zan aje labarin sai sanda na samu dama kawai na samu faraga in rubuta.
Ɗakin Abba Faruk ya nufa bayan ya aje motar sa, Abban na zaune yana karin safe Faruk ɗin ya shiga, cike da girmamawa ya ce Abba gani bayan ya gaida shi.
Yawwa daman ina son in faɗa maka ne ɓarin Hajiya babba mai rasuwa zan sa a gyara maka shi zaku zauna da Fatima gaban Faruk ne ya faɗi ya dai daure ya ce Abba Fatima kuma Ummun fa Faruk ya faɗa fuskar sa cike da tashin hankali.
Murmushi Abban ya yi kafin ya ce yo banda abin Faruku ai kai mijin Mace huɗu ne Ummu tana nan a matsayin ta na uwar gidan Faruk.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Faruk ya faɗa a ransa kafin ya ce amman Abba.... Ɗaga masa hannu Abban ya yi, kafin ya ce kaga ba shawara na kiraka muyi ba, ba kuma alfarma na ce kamin ba, umarni na baka in kuma umarnin nawa ne bazaka bi ba to ka faɗan inji, kayan lefe nan da Sati zasu kammala zamu kai, sauran inji kayi wani zancen da ba haka ba wallahi sai na saɓa ma.
Sun sun Faruk yasa ƙafa ya bar ɗakin shi kam ƙarshen rashin adalci da za'a masa arayuwa shine a sa ya auri Fatima, kwata kwata bata tsarin matan da yake son zama dasu ko da ace shi yana da burin zama da mata huɗu baya jin zai iya zama da Fatiman.
Ransa ya ɓaci sosai fasa zuwa gidan su Ummun ya yi, ya nufi gidan su Fatima.
Kasan cewar sashen ta daban yasa kai tsaye bangaren ta ya nufa, a baranda ya hangeta tana saman bene kai kawai yasa ya shiga falon yana ƙoƙarin hawa benen ya dora idanun sa kan ta tana ƙoƙarin saukowa.
Da murnarta ta sauko sanye ta ke cikin ƙananan kaya kusan sun zame mata ɗabi'a da wuya ka ganta cikin kayan hausawa, riga ce da dogon wando sun mata kyau sosai dan ita ɗin mai kyau ce ba karya.
Ai na ganka sanda ka shigo sannu da zuwa ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushi, tsaki Faruk yaja kafin ya ce ni kinga Malama ba sannu da zuwa nazo kimin ba kashedi nazo in miki.
Murmushi ta kuma yi wanda ya kufula Faruk ɗin kafin ta ce koma dai kashe din mene ka dai zauna ko.
Cikin faɗa yake magana, ba zan zauna ba in kuma zaki kamani ki zaunar dani se in gani.
Matsowa ta yi, to mene a ciki ni ba baƙuwae zafi ba ce sai in zaunar da kai ɗin ta fada tana ƙoƙarin kamo hannun sa.
Tankaɗe hannun ya yi wai ke me yasa Dabba ce baki da tunani, kallon sa ta yi ranta ya fara ɓaci bata ce komai ba yayin da shi kuma bai damu da damuwar da ta shiga ba ya ce ki sani ni Faruk nafi karfin zama da mutun irin ki.
Cikin zafin rai ta ce wai Faruk mai ne haka ne, me na maka ka tsane ni haka son ka fa kawai nake.
To ni bana son ki kuma bazan zauna da Yar iska ba wallahi ya faɗa bayan ya tako daf da ita.Taɓe baki tayi kafin ta ce kuma dai, wallahi kaji dashi dan inni yar iska ce kaima ɗan iskan ne tunda tare mukai watsewar mu.
Ke Malama dakata kema kinsan ni ba ɗan iska ba ne ke kika lalatani.
Murmushi ta yi muka dai lalata juna ko?.
Hannu ya kai zai maketa tayi saurin kaucewa, kar ka sake ta faɗa alamar kashedi naji zan ɗauki komai banda duka wallahi.
Tsaki ya yi kafin ya ce na faɗa miki koma me kikai wa Abba ya ce in aureki ki je ki faɗa masa ke kin fasa na faɗa miki.
YOU ARE READING
Ummu Hani
RomanceNot edited!!! Duk da cewar iyayansu sun mutu, an rasa wanda zai ɗauke su cikin dangi, ummu hani yar kimanin shekara goma sha shida ita ta ɗauki ragamar kula da yan uwanta guda shida, ciki harda jaririn da ummansu ta rasu gurin haihuwar sa, wanda ras...