MIEMAH
Page 1
Typing 📲
Story and written by :
Khadija yusuf abba. (Real deejah)Follow me on wattpad @deejatou
Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai da ya bani ikon fara rubuta muku wannan littafi a yau 21 April 2021,ina rokon Allah ya bani ikon rubuta abinda xae anfanar da al'umma sannan kuma ya kareni daga rubuta abinda bai dace ba, fatan xaku bini don jin yanda labarin xata kaya😊
Abuja 1990
Cikin villa na shiga domin dauko muku rohoto😊
Ba sae na fada ba kuma kun sani irin haduwa da kyawun da villa take dashi, wasu yara qanana su biyu masu mugun kama da juna na hango tsaye a parking space, da sauri na qarasa wajensu, masha Allah shine abinda na furta yayin da na isa wajensu, 'yan yarane da baxasu wuce shekaru biyar ba a duniya, kai kana ganinsu kasan yan biyu ne irin Wanda ake kira da identical twins domin kaman har ta 6aci saboda ba a iya banbancesu, kyawawa ne ajin farko, domin sunfi kama da Yaran India jikinsu sanye da uniform da kuma school back da lunch box guda daya a hannun dayar, hankali nah na mayar kan daya yarinyar da naga ta mugun hade rae, cike da tsiwa take kwala wa driver qira, "Idi! Idi!! Idi!!! Wae wane irin shiririta ne tun daxu muna tsaye muna ta jiranka kaqi kaxo ka kaimu ko so kake muyi latti ne🙄". "Ke MIEMAH ba ummie ta ce ki dena yima baba Idi Rasar kunya ba" yar uwar tata ta fada cike da sanyin murya. Cike da masifa miemah ta fara cewa "kinga miemie kimin shiru tun daxu muke tsaye mutumin nan yaqi ya kaimu makaranta kuma fa madam iyabo ce first period " ta qarashe maganar cike da karaya, kafin miemie ta bata amsa sae ga Idi driver yaxo cikin sauri yana cewa"dan Allah yan biyu kuyi haquri wlh na makara ne yau din" Wani wawan Tsaki miemah taja ba tare da tace komai ba ta juya ta kalli body guard 💂 da sauri ya bude musu back seat suka shiga suka xauna sannan ya koma front seat gefen driver aka yi driving dinsu xuwa school.
Ana parking da sauri body guard ya fito ya bude musu motar, miemah ta riqe hannun miemie suka nufi class dinsu, ae kuwa sun samu madam iyabo ta rigasu shiga, kuma ita dokar ta in ta Riga yara shiga to sae ta xane su, ga miemah da shegen tsoron duka, nan da nan idanunta suka firfito alamar tsoro😌, hakanan ta xane miemie a takashi, akaxo kan miemah, tun kafin a ta6a ta fara kuka, ganin haka yasa miemie tayi sauri ta cewa madam iyabo kar ta daki miemah ita ta yarda ayi mata memakon na miemah (saboda suna mugun son junansu) da sauri miemah tace ''a'a habibty (sunan da suke qiran junansu dashi wani Lokacin) ki bari kawae. Miemah Taje aka xaneta ae kuwa har da na mugunta madam iyabo tayi mata saboda dama tana jin haushinta dan rannan tayi mata Rasar kunya, ae kuwa tayi ta kuka tare da jan Allah ya isa tana cewa kuma sae ta rama, nan miemie ta rungumeta suna cigaba da kuka su biyun yan class kuwa sunyi tsit kamar ruwa ya cinyesu saboda sun san halin masifar miemah yanxu sae ta huce a kansu, tsawa madam iyabo ta daka musu tare da cewa "get lost from there! Go and have a seat 💺 👈 "tare da nuna musu kujerar da hannunta, miemah dae bata da alamar tashi daga wajen, sae miemie ce taja hannunta suka bar wajen.
Hakanan yau suke a school din kwata-kwata babu dadi.
During break time, suka fito suka nufi inda suke yin break, har yanxu miemah bata dawo normal ba, kawae neman hanyar da xata rama abinda madam iyabo tayi mata take so, habibty kixo muci abincin mn, nipah yunwa nake ji, cewar miemie. Miemah tace Bana jin yunwa habibty. "Shknn to"cewar miemie itama tare da cire hannunta daga cikin abincin, "A'ah habibty, me yasa xaki dena cin abincin, yunwa fa kk ji" cewar miemah "Ae kin sani Bana iya cin abinci in ba tare dake ba" sorry sis Bana jin yunwa ne amma bani fruit in akwae" "ayaba ne kawae kinsan yau Aunty kareema ce ta hada mana lunch box din. Tsaki miemah taja tare da cewa bani ayaban, miemie ta miqa mata, ae kuwa nan ta saki murmushi sbd wani mugunta da ta tuna. Ta juya ta kalli miemie tace habibty jirani ina xuwa. miemie tace "ok take care of ur self banda tsokala pah sis" murmushi tayi tare da cewa "never mind sis" sannan ta juya da gudu ta nufi office din madam iyabo, cikin sa'a kuwa ta samu madam iyabo bata nan. Dan haka ta jera bawon ayaban nan a office din madam iyabo kuma office din gaba daya tiles ne, tana jerawa ta fita ta buya a dan wani lungu, cikin sa'a kuwa sae ga madam iyabo nan tana tafowa, madam iyabo irin christians din nan ne qatti masu saka qananun skirt ae kuwa ta taho da action dinta tana ta xuba masifa tanayin step daya xuwa cikin office dinta bawon ayaba ya jata suuu ta fadi timmmm!"oh Jesus Christ " shine abinda ta ambata tare da sake wani irin ihu saboda gsky ta bugu😂. Lokacin kuwa yayi daedae da lokacin da yara ke komawa class, ae kuwa nan yara suka tsaya suna ta dariya miemah kuwa har da riqe ciki, miemie tana ganin haka ta tabbatar yar uwarta ce ta aikata hakan, jijjiga kae kawae tayi tare da cewa"sis Allah ya shirya ki". Daedae lkcn da sauran staffs suka qaraso suka kori student xuwa classes dinsu sannan aka dauki madam iyabo daqyar sbd nauyinta aka sakata a mota a ka kaita hospital.During closing hour
Suna fitowa suka tarar da driver da body guard dinsu suna jiransu, nan babu bata lokaci suka shiga aka wuce dasu gida.
Direct side din ummie suka nufa, ummie! Ummie!! Ummie!!! Shine sunan da suke ta ambata yayin da suka shiga falon da aka kashewa dukiya mai yawa a ciki, wani matashi ne kyakkyawa da baxae wuce 15yrs ba yake xaune a palour, da gudu suka qarasa garesa tare da rungumesa suna cewa"yah sadeeq ina ummie" shima rungumesu yayi tare da cewa "twins din ummie, ummie tana side din Abbie" "laahh yaushe abbie nah ya dawo" cewar miemah cike da doki" daxu ya dawo, ae kuwa da gudu suka fita suka dau kekensu (irin na 'ya'yan turawa😉) kasancewar a dan kwae taxara tsakanin su da part din Abbie da sauri suka isa, da gudu suka qarasa suna qiran Abbie. "My twins kun dawo " da gudu suka je suka rungumasa suna cewa "Abbie sannu da dawowa "yauwa twins dina, ya karatu" alhmdllh Abbie ya hanya "alhmdllh my twins" ummie Barka da gida. Cewar twins. Dan harara ummie ta watsa musu tare da cewa "ni bb ruwa na daku, yau dan kunga Abbie shine kuka qi kulani ko🙄" cike da shagwaba suka hada baki suka ce "sorry mom 🙏"murmushi tayi tare da cewa "bakwa laifi my twins, kuje wajen uwani kuce tayi muku wanka kuci abinci sae ku huta ku tafi islamiyya" miemah ce tace "Abbie nah yau tare dakae xamuyi lunch"aunty kareema da take xaune a gefe wacce baqin ciki ya gama cikata saboda yanda aka mayar da ita banxa a wajen ana ta biye ma twins, kwafa tayi , cikin xuciyarta tace "miemahhh sae na halaka ki wlh" amma a fili sae tace"a'a gacan abincinku an Riga da an jera muku a dining din side dinku" cike da tsiwa miemah tace "wae aunty kareema ina ruwanki da ni ne, nace tare da abbinah xanci ai ko 😏" ta karashe maganar tare da jan Tsaki. Tabbas tayi mugun 6atawa aunty kareema rae, sannan a tunaninta abbie xae mata fada, amma ga mamakinta sae taga yayi murmushi tare da cewa "mamana akwae rigima, tashi muje muci" cike da murna ta kama hannun miemie suka bi bayan abbie xuwa dining area. Ummie kuwa tashi tayi ta koma side dinta, aunty kareema kuma taxo ta fara serving dinsu, cooler farko da ta bude fried rice ne a ciki, cike da shagwaba mimah tace Abbie ni gsky Bana cin fried rice. Miemie tace "sis kiyi haquri kici mn"a'a wlh habibty ni baxan ci ba" Abbie yace"mamana me kk so" tace "fried Irish with sauce ". Kareema je ki girkawa maman abinda take so" ae kuwa hakan ya qara dasa tsanar miemah a xuciyarta, tare da cin alwashi daban-daban akanta. Hakanan Taje ta soyo ta kawo mata, tana Cikin soyawa ta sake murmushi saboda wannan ma wani dama ta samu da xata kashe miemah Cikin sauqi, maganin da BOKA MURTU ya bata ta dauko ta barbada akan sauce din, sannan ta kawo wa, su miemah, a lokacin kuwa miemah sae hamma take saboda yunwan da yake cin cikinta, gashi tana iya jiyo kamshin sauce din daga kitchen, gaba daya ta qagu da akqwo abincin nan ta fara ci............Inci gaba ko in tsaya a haka, comment dinku ne xae bani kwarin gwuiwar rubuto muku book din
Wannan dandano ne daga littafin MIEMAH insha Allah bayan sallah xamu Dora daga inda muka tsaya. Sae Kunyi haquri domin littafin
👉me tsawo ne👈.Ina mukubarka da shan ruwa, Allah ya karbi ibadunmu 🙏
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...