👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 6
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
Aunty afrah ta sauka cikin Australia cike da kewar Nigeria da mutanen da ta baro a cikinta, saedae kuma can kasar xuciyarta cike take fal da tsanar Nigeria da kuma da na sanin xuwanta. Cab ta tare ya kaita har kofar gidansu, shiga tayi cike da sanyin jiki idanunta suna tsiyayar hawaye, sallama tayi a falon amma babu kowa don haka ta wuce bedroom din aunty ni'imah direct, cike da murna aunty ni'imah ta taso ta rungume ta tare da tambayarta ina Al'ameen.......... Turus tayi cike da damuwa ganin yanayin da aunty afran take ciki. Nan ta fara tambayarta Meke faruwa ne, kuma ina ta baro Al'ameen, kuka aunty afrah ta sake tare da rungume mahaifiyarta ta "ammah ismail ya koreni kuma ya kwace Al'ameen........... Nan ta bata labarin abinda ke faruwa, itama amman kuka take sosae tare da ba 'yar tata hakuri da kalamai masu dadi "ammah wlh baxan iya rayuwa ba tare da su ba, ina musu xaxxafar son da bana yiwa kaina, ammah sune Rayuwata, ammah xasu kashe min Al'ameen 😭 ina kaunar 'dana, Al'ameen yaro ne sosai baxae iya kare kansa daga sharrin su ba, kuma duk akan mulki suke son tarwatsa mu, tsugunawa tayi a gaban ammah tare da fashewa da kuka mai ban tausayi tana cewa "dan allah ammah kiyi wani abu akan hakan wlh ina kaunarsu😭. Itama ammah kuka take sosae tare da sake rungume afrah "kiyi hakuri afrah, insha Allah baxaki rasa su ba, sarki ismail har yanxu a matsayin mijinki yake, shi kuma Al'ameen danki ne, Allah xae kare miki shi, sharrinsu baxae ta6a kama ki ba. Da kalamai masu dadi ammah tayi amfani wajen kwantarwa afrah rai.Dr. Farhan tun yana driving kan ya isa gida ya daga wayarsa ya kira wata classmate nashi zuby wacce take budurwar yarima ishak ce, bayan ta daga sun gaisa ne yake tambayarta, xuby kina ina ne? "Ina cikin babbar masarauta", ke kuma me ya kaiki babbar masarauta, jiya tare muka kwan da yarima ishak a cikin babbar masarauta,. Dama yana shiga da 'yan mata cikin masarautar ne? Aa a matsayin kawar kanwarsa na shiga, ok ni duk ba wannan ba so nake ki dauko min alameen dan kanin ishak din. "Alameen kuma, a dalilin me xan dauko ma alameen farhan? Look xuby in baxaki dauko min bane kawae ki fada, ae dama na sani ba dagaske kike sona ba, kuma shikenan baxan sake kiranki ba. "Haba my handsome take it easy nah, kasan dae ina kaunarka har raina kaine dae kake shareni, indae alameen kake so na dauko maka to ka bani 30mins xan kawo maka shi yanxu just chill. Murmushi yayi cike da aji tare da cewa gud girl, ina jiranki daga haka ya kashe wayarsa yaci gaba da driving xuwa gidansa, wanka yayi tare da buga waya a abokinsa "kamin booking flight yanxu nan xuwa kano" daga haka ya kashe wayar. Yana gama shirya wa ya sake kiran xuby "muhadu a airport nan da 10mins.
Lokacin da ya isa airport its already time kawae alameen ya karba daga hannunta wanda ta dukunkuno shi a cikin towel kaman jariri tare da cewa 'xan miki bayanin komai in na isa' daga haka ya shige cikin jirgin ta daga xuwa kano.
Bayan ya isa cikin gidansu a cikin mota yabar alameen saboda baya son yawan tambaya, ya shige side din dad direct.
Farhaan kashirya na gama yi maka visa xuwa U. S domin kula da business dina na can duk da ma dae ba fannin bussiness ka karanta ba amma nasan xaka iya, its urgent dole ina da bukatar wanda xae tsaya ya kular min dasu in ba haka ba kuma abin xae iya rugujewa. Karka damu daddy insha allah xan kular maka dasu. To ya maganar aure kuma. Aure kuma dad, am just 22yrs old pah , kawae dan kunyi min jumping na gama university da wuri shine kuke son cusa min aure. Ya karashe maganar cike da shakiyanci, dariya dad din yayi tare da yi masa dakuwa yace "kaniyarka farhan, ka maida ni kakanka pah, ka shirya da wuri 12:00'o'clock jirginku xae tashi gashi its alredy 11:30. Tashi yayi tare da cewa bari na wuce to, ina hakeem pah, mom ma shiru ban jita ba. Duk suna side dinsu. Tashi yayi ya fice daga wajen dad, yana fita side dinsa ya wuce, a gurguje ya shirya yaxo yayi sallama da mom da lil bro dinsa hakeem tare da pecking abdul dan shekara biyu sannan ya shige mota driver yajashi xuuwa airport, yana isa ya dauko alameen tare da saka black speck nashi ya rufe fuskarsa ya shige jirgi, kallonsa ya maida kan alameen daketa baccinsa cike da kwanciyar hankali yayi, dan murmushi yayi tare da cewa little cute, insha allah xan xame maka garkuwa! Daga haka jirgi ya daga suka bar nigeria.
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...