Miemah page 4

34 4 1
                                    


👉🏽MIEMAH 👈🏽
Page 4
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺

Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba

Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽

Bismillahir-rahmir-raheem

***************************************

Akwai wadanda in suna karanta littafi in aka xo inda xa'a bada asalin labari suna skipping basa karantawa, to ina tabbatar muku da cewa littafin miemah in baku karanta asalin labarin ba baxaku ta6a gane inda ya dosa ba

Asalin Labarin
Alhaji muhd (abbie) , 'dane ga alhaji zaid muhd, asalinsu fulanin yola ne. Alhaji zaid muhd hamshakin mai kudi ne wanda kusan duk kasashen duniya sun san da xamansa, hakanne yasa bai fiye xama a nigeria ba, yana xaga kasashen duniya da dama domin business dinsa, a haka ne ya hadu da maryam yar kasar Australia, musulmai ne na asali duka danginsu, a haka suka gina tsatatacciyar soyayyarsu, bai sha wahala ba wajen shawo kan iyayen maryam suka amince da bikinsu kasancewarsa sanannan mutum ne, nan kuwa akayi biki cikin walwala, an kashe kudade sosae wajen bikin nan kasancewar familyn su maryam ma hamshakan masu kudi ne. An dauko amarya an kawota nigeria a cikin garin abuja. Xama suke xaman lpy me cike da kauna da mutunta juna, akai akai takan xiyarci yan uwanta dake australia, a haka har saeda sukayi shekara biyar sannan allah ya axurta su da samun 'da namiji, xo kuga murna cikin wannan familyn 😊, kowa yana murna da karuwar da aka samu, yaro fari tass kyakkyawa tamkar bai hada jini da nigeria ba, ranar suna yaro yaci sunan mahaifin zaid wato muhd, haka akayi suna cike da farin ciki aka watse.
Muhd ya taso cikin kulawa da kaunar iyayensa, yayi karatunsa tun daga primary har xuwa matakin secondary anan Nigeria, lokacin da yake SS3 ne suna xana paper a lokacin ne kuma mamar maryam dake kasar australia allah yayi mata rasuwa, tabbas sunji mutuwar sosai, don haka suka shirya domin tafiya australia, amma ba da muhd suka je ba, kasancewar yana rubuta paper, sun barshi a gidan abokin alhaji zaid mai suna alhaji saleem sannan suka tafi, sunje lpy sunyi gaisuwar, sannan kullum suna waya da su muhd, satinsu biyu a can sannan suka shirya dawowa Nigeria, akan hanyarsu ta dawowa sukayi accident jirginsu ya kone, mutane da dama sunji raunika sosai yayinda wasu kuma allah ya karbi ransu take a wajen ciki kuwa harda alhaji zaid da matarsa merama, 😥.
Nan aka watsa mutuwar nan cikin jaridu da televission kasancewar sa babban mutum, nan aka dauki gawawwakinsu xuwa gidansu (saboda iyayen alh xaid suma sun rasu) inda jama'a suka taru, nan akayi musu wanka aka shiryasu aka kaisu gidansu na gaskiya.
Tabbas muhd yaji mutuwar iyayen nasa sosae, don sai da yayi sati bai san inda kansa yake ba, da kyar da addu'a sannan muhammad ya dawo cikin nutsuwarsa.
After 3months da rasuwar alh zaid, muhd ya kammala rubuta paper din sa har ma result ya fito, hakan yasa dangin mahaifiyarsa suka daukesa xuwa australia domin karasa karatunsa.
A gidan aunty ni'imah kanwar mamarsa ya sauqa, aunty ni'imah yaranta hudu ne, first born nata mace sunanta Afrah, tsakanin afrah da second born dinta kuma bb nisa sosai, twins ne duka mata masu suna Amrah da kuma Amnah, sae last born dinta Rafeeq. Anan ya fara karatunsa cike da nasarori, a haka har ya kammala degree dinsa na farko a fannin public administration, yayi na biyu da na uku sannan yaje yayi masters dinsa ya kammala. To anan pah kasar australia taso rikesa amma fir yaki yace shima yana so yayi wa kasar sa aiki, a lokacin ne kuma aunty ni'imah tace ya kamata yayi aure kafin ya koma Nigeria, ai kuwa yaji dadin hakan don dama soyayya suke da amnah, don haka bb bata lokaci ya sanar da ita kudurinsa, ae kuwa tayi murna sosai da jin hakan, ita ma amrah dama akwae wani dan Nigeria da suka hadu dashi a school sunansa Imraan, shima wani hamshakin mai kudi ne kuma dan boko a kasar Nigeria, yaxo shi australia yin wani course ne allah ya hada sa da Amrah suka fara soyayya, itama aunty afrah wani dan nigeria xata aura mai suna Prince isma'il dan sarki ABDALLAH ne a babbar masarauta.

TARIHIN BABBAR MASARAUTA
Babbar masarauta, wata masarauta ce me cike da ixxa da karfin mulki da kuma dukiyoyi, an Gina ta shekaru da dama tun xamanin kakannin kakan mu, masarauta ce wacce duk wani Wanda ya fito daga cikin ahalinta yake son mulkar ta ciki kuwa har da mata kasancewar masarauta ce wacce ta samu daukaka a cikin Nigeria dama kasashen ketar. Duk wani wanda ya fito daga cikin ahalin babbar masarauta abin girmamawa ne ga al'ummar cikin gari saboda karfin mulki da suke dashi. Haka nan duk wanda aka ce ya xama sarki yana mulkan babbar masarauta topah duk duniya sae sun san dashi saboda masarautar tana da joint da kasahen ketare daban daban, hakan yasa har mata ke son mulkar masarautar amma dae a tarihi babu macen da ta ta6a mulkar BABBAR MASARAUTA.

MIEMAHWhere stories live. Discover now