MIEMAH Page 35
By khadeejat Yusuf Abba
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Gudu suke tsalawa sosai a haka har suka isa gidan boss.
Direct inda jet din yake suka nufa, turus suka tsaya ganin jirgin tana ci da wuta, durkushewa miemie da Ashnaah sukayi a wajen suna kuka mai ta6a zuciya.
Magana sukaji daga bayansu, suna juyawa suka ga miemah ce tsaye babu wani abinda ya sameta, sae jinin dake jikin kayanta, duk da mamaki suke kallonta.
Karasowa inda suke tayi, tare da jan stool dake gefe ta zauna akai tana harararsu.
Amma kun bani mamaki da har kuka yadda yar karamar kwakwalwar aunty kareema xata fi nawa aiki.
Cikin sauri suka karaso gareta suna tambayar ta me ya faru? Ya akayi ta fito daga jirgi lpy kalau?
Bayan Ashnaah ta tafi tafi boss tayi dariyar iya shege tace aje a kunto Miemah.
Cikin sauri aka tafi aka kunco ta, kuma batayi gardama ba ta biyo bayansu dan a tunaninta Ashnaah tana nan.
Ku kasheta, shine abinda boss tace. Daura mata bindiga akayi a kai tayi saurin wafce wa tare da kai mishi naushi ya fadi a wajen.
Bindigar yana nan rike a hannunta, daya daga cikinsu ya sake kawo mata duka, babu 6ata lokaci ta harbeshi a kai.
Daya ma haka yaxo nan take ta harbeshi a zuciya.
Boss tayi matukar tsorata da ganin wannan aika-aika da miemah tayi.
"Kar ku sake ta6a ta, wannan shine umarnin da boss ta basu"
Dan duk a tsorace take da miemah, suma sauran tsoro ne fall a ransu, tabbas in aka barsu da miemah xata iya kashe su gaba dayansu kuma ta kashe banxa.
Daya ne ya sand'a ta Bayan Miemah tare da damke bindigar, bata sake mishi ba kawai ta harba bindigar a cikinshi, nan take shima ya fadi
Ihu boss ta kwala tana cewa ke miemah baki da hankali ne? Wane irin abu kike aikatawa haka ne? Tsaki tayi tare da wurgar da bindigar tace "duk Wanda yake son rasa ranshi ya tunkaro ni ya gani.
Daya ne ya sanda yaje ya hura mata powder ta shafa, ai kuwa nan hankalinta ya gushe.
Gaba dayansu sauke ajiyar zuciya sukayi suna Murmushi.
"Ku sake daure ta". Abinda boss tace kenan, nan kuwa aka daure Miemah.
Kuje ku wulla ta cikin jirgin, tun jiya nayi mana booking flight saboda dama Nasan da xuwar afrah Nigeria kuma Nasan Abdul ne xaije ya daukota tunda sadeeq baya nan, ita kuma wannan shegiyar Ashnaahr in na kama ta sae na yankata, yar karama da ita har xata iya wasa da tunani nah haka?
Kuma yanxu haka ba China xamu je ba, dan shegiyar xata iya binmu dan ita tasan abinda ta shirya a chinar, dan haka London xamu tafi yanxu haka.
Abinda basu sani ba shine Miemah a cikin hankalin ta take duk tanajin abinda suke fada saboda bata shaki wannan powdar ba kawai pretending ne.
Nan kuwa suka dauki Miemah suka wullata cikin jet din.
Duka gidan gidan suka tafi ko tsuntsu basu bari ba, Miemah tana tabbatarwa sun tafi ta jawo jikinta daga cikin jirgin ta fito, a bakin jirgin ta tsaya dan baxata iya fitowa daga steps din ba.
Salmah wacce ta tafi da babies din maryam ce ta shigo gidan, hango jet din tayi dan haka ta tafi wajen, ganin Miemah a wajen yasa ta karasa da sauri.
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...