Part 38

10 1 0
                                    

Miemah page 38

      Naushi alameen ya kai mata cike da huci yace "dan baki da hankali ta yaya xamu yadda da wannan tatsuniyar taki na cewa uncle farhaan bai mutu ba?

      Numfashi take saukewa cike da azaba  tace "Bana so na baku labarin komai anan, Mu tafi babbar masarauta".

     Asibityn da maryam take suka nufa da gimbiya azrah, maryam kam dae jikin da dan sauki, nan sukayi musu bayanin komai, suma cike da shock suke. Hakan yasa aka bar mom da miemie a wajen maryam sannan Duka aka shiga mota aka nufi babbar masarauta.

      Karfe goman dare suka isa babbar masarauta, sun samu tarba me kyau. Masarauta dae tana nan babu abinda aka fasa, sae ma sabon fasali mai burgewa da aka yi mishi.

     Sarki ABDULAZEEZ yana kula da masarautar kan gaskiya da rikon amana, hakan ya kara daukaka darajar masarautar a idon duniya, ta xamo madaukakoyar masarauta, koda mai shafa ne a cikin masarautar nan to Ana girmama shi. Masarauta ce da duniya ke ganin kima da darajarta.

     Kasancewar dare yayi hakan yasa basu samu lokacin tattaunawa ba, kowa ya wuce masaukin da aka tanadar mishi. Sam basu samu damara yin wani bacci ba dan dukansu cike suke da fargaba.

   Washe gari karfe takwas na safe duk aka faru a fadar sarki abdulazeez. Nan aka gaggaisa tare da tambayar bayan rabuwa anan ne kuma aka gabatar da alameen da kuma afrah.

     Ai kuwa Anyi murna sosai da alhinin abinda ya faru.

    Sarki abdallah ne ya dubi gimbiya azrah tare da cewa "azrah ke muke jira" nan kuwa ta fara bada labari.

SOME YEARS BACK
       Lokacin da aka kashe fadawan da sarki ismail ya fita dasu shi daukeshi sukayi suka kaishi wani waje.

     Tun a lokacin kareema tana hulda da yan kungiyar shanye jinin mutane. Godiya ce tace kar ta kuskura ta kashe sarki ismail saboda jininshi xai jawo musu asara da yawa.

     Kareema a lokacin ta so kin amincewa umarnin godiya saboda Ita ta tsani taga ismail yana rayuwa a doron kasa. Da ta fadawa godiya haka sae godiya tace wannan ba matsala bace, xamu asirce shi, xai xama shi ba rayayye ba kuma ba matacce ba, wannan asirin kuma baxai ta6a karyewa ba har sae lokacin da kika bar duniya.

    Kareema tayi farin ciki sosai da jin wannan batu,  tana ma fatar Allah ya kar6i ranshi kafin ta bar duniyar.

    Bayan godiya tayi wannan asirin kareema ya dauko sarki ismail a booth din motar ta ta shigo da shi cikin gidan nan tare da kaishi *dakin tarihi* dake cikin masarautar nan dan dama ya hada baki da wanda ke kula da wajen.

      With shock duk suke kallonta, cike da baking ciki sarki abdallah yace "dama duk tsawon wannan lokaci da aka dauka isma'il yana cikin masarautar nan? Amma Allah ya isa! Allah ya isa tsakanina dake axrah, kuma ma sake ki saki uku.

    Kuka kawai take, tasan duk wani hukunci da aka xartar a kanta she deserve.

    Kallon sarki abdallah tayi tare da cewa "na yarda na dau duk wani hukunci, amma Ina neman gafararka akan cin amanarka da nayi, kareema ba 'yarka bace 'yar boka tsito ne"

      With shock kowa ke ganinta, shiko sarki abdallah murmushin bakin ciki yayi tare da cewa "no wonder, tabbas jini nah baxata aikata haka ba, ya ishak nan duk rashin jinshi bai ta6a kisa ba, sannan duk abinda yake a baya ma ya tuba ya daena"

     Cike da tsanar xuriyar azrah Miemah tace "uncle farhaan pah?

     FARHAAN
    Lokacin da yaran kareema suka kashe farhaan, taje ya sanar wa godiya.

     Godiya tayi fada sosai game da jinin farhaan da suka xubar domin tana hango tsantsar hadari da barazana dake tattare da jinin farhaan a harkallar su.

     Sun tafka babbar asara a lokacin sannan kuma asirinsu ya kusa tonuwa. Ganin asirin nasu bai tonu ba yasa godiya ta fara dube²nta game da farhaan Dan tabbas indae ya mutu to minti goma baxa'a Kara ba asirinsu xai tonu.

     A binciken godiya ta gano farhaan yana numfashi, kidima ne kawae ya hana a fahimta. 

    Lokacin an gama sallatar gawarshi kabarinshi kawai xa'a kaishi, cikin sauri ta tura aljani ya sauya gawan tare da daukowa gawan farhaan ya kawo wa godiya. Daga nan ta kira  kareema ya sheda mata komai.

    Duk cikin kungiyar kareema babu Wanda yasan wannan abu sae drivern jet dinta kuma an kashe shi ma.  Haka ta dauki farhaan a private jet dinta ta kaishi kasar uk likitoci suka fara treating dinshi.

    Lokacin da su miemah suka kai alameen asibity har miemah ya harbi kareema ita kuma tasa aka dauko mata afrah, to lokacin ma farhaan yana cikin asibitin kuma shi suka je dubawa.

    Tsawon shekara guda farhaan ya samu a asibity kafin ya warke. But ya samu loosing memory dan tsawon shekarar nan  a cikin comatose yake.

    Ya mance wanene shi ma bare har ya tuna wani nashi, hakan yasa kareema ya daukoshi ya kawoshi gidan tarihi shima ya hada shi fa sarki ismail.

    Tun daga nan kula da sarki ismail ya dawo hannun farhaan har xuwa wannan lokaci da nake baku labari, a halin da ake  ciki yanxu farhaan ya dawo hayyacinshi sati daya da ya wuce. Shima sarki ismail nasan asirin ya karye tunda dae kareema ta mutu. Karashe maganar tana cigaba da kuka.

    Kowa sae Allah wadae da halinsu yake yi ma mugunta.

     Abdul da alameen ne suka mike tare da cewa "ina ne dakin tarihi?

     Miemah ma mikewa tayi tare da cewa xan Niki nima, ashnaah ma mikewa tayi. Nan kuwa duka falon kowa ya mike yana son xuwa dakin tarihi. Nan kuwa aka tattara aka nufi dakin tarihi!

       Mai tsaron wajen ne ya bude musu yana sussunkuyar da kai cike da kunya. Ko ta kanshi basu bi ba suka shige ciki.

     Suna shiga suka ji an kece da wata kalar dariya mai raxanarwa, sae da akayi dariyar nan na tsawon mintuna goma kafin aka tsaya aka fara magana.

    "Tsakanina da kareema akwai amana mai karfi  Dan haka koda bayan ranta dole ne sai na cika mata burinta, baxan ta6a bari su ismail suyi rayuwa a doron kasar nan ba tunda dae kareema bata so, dan haka na daukesu na kaisu inda baxa'a sake ganinsu ba har abadan!

 

Gashi, na kokarta, na kukkutsa, na daure nayi muku wannan typing din dan farin cikinku. Kuyi manage.

Deejay ce

MIEMAHWhere stories live. Discover now