👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 9
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abbaFollow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽
Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
TUNA BAYA
Masu iya magana kan cewa "waiwaye adon tafiya" to yanxu dae xamu waiwaya baya domin jin asalin labarin familyn da MIEMAH ke ciki.
.
Alh sa'eed da dan uwansa ayuba asalinsu yan RUGAR BABBAR RAFI ne, suna da dukiyan shanukai da akuyoyi sosae a garin, mahaifinsu shine hardon rugar. Tun tasowansu sa'eed yake da burin yin karatun boko yayinda ayuba kuwa boko bata damesa ba, hakan yasa sa'eed yake xuwa yar makarantar primary dake cikin rugar tasu, a haka kuwa har ya kammala sakamako ya fito an turasa makarantar kwana dake cikin takai l.g.a, mahaifinsu kuwa baiyi musu ba ya saeda shanu guda yayi masa duk wani siyayyan da ake bukata a makarantar tare da basa dan kudin kashewa, haka yaje ya fara makarantar har ya gama tare da samun result mai kyau daga nan ne kuma ya nemi admission don xuwa institution kuma ya samu yayi karatunsa cike da nasara har ya kammala ya samu aiki, ya tsallake matakai daban daban har dae yayi suna sosai a waccan lokacin, yayi yayi akan iyayensa da dan uwansa su dawo cikin kano a gidan da ya Gina musu, amma Sam sunki sunce su sun fison xama a tushensu. an masa aure da yar rugarsu mai suna maryam har Allah ya axurtasu da su da 'ya'ya. Muhammad shine babba sae imraan, sae kuma autansu saleem. Sun taso dukansu cikin gata tare da soyayyar iyaye sun samo ilimin boko da kuma islamiyya, lokacin da Muhammad ya gama secondary dinsa aka tura sa Egypt domin cigaban karatunsa, anan ne kuma ya hadu da sarki ismail har suka kulla abota na kud da kud. ya cigaba da karatunsa har xuwa matakin masters, yayi degree a fanni daban daban ya samu ilimi da gogewa wajen muamala da mutane. Egypt sun so rikesa amma yaki yarda yace yana so yayi wa kasarsa aiki da iliminsa, yana dawowa Nigeria kuwa ya samu matsayin prof. Duk da hakan lokaci lokaci yakan xiyarci wasu kasashen domin yin course akan wani abin, ana haka kuma ciki ya bayyana a jikin mamarsu maryam still, kowa dae yayi mamaki kasancewar ta jima rabonta da haihuwa amma duk da haka sunyi murna sosai. a haka dae muhd yake cigaba da samun daukaka har xuwa yanxu da yake matsayin minister of education. Saleem da imraan kuwa a Nigeria sukayi karatunsu, course ne dae suka tafi abroad sukayi. A lokacin ne kuma mama maryam ta haihu ta haifi danta namiji santalele kyakkyawa dashi, ranar suna yaro yaci suna FARHAAN. Haka nan shima ya taso cike da gata yayyensa suna kaunar sa sosai, ana haka ne kuma alh SA'EED Allah yayi masa rasuwa, sakamakon accident din da yayi. Familyn sunji mutuwar sosae da sosai amma babu yanda suka iya haka suka dangana suka barwa Allah. Muhammad yayi auren fari da matarsa fateema wacce itama yar wani hamshakin mai kudi ne, Fatima tunda taga farhaan yaro me shekaru uku a duniya taji tana kaunarsa, tacewa mama maryam ta bata farhaan xata rike shi budar bakin mama maryam tace mata kema ki haifi naki nima haifarsa nayi, haka ba yanda ta iya ta hakura, da ta fadawa Muhammad ne yace mata tayi hakuri indae farhaan ne to xai dauko mata shi, hakan kuwa akayi yaje ya samu mama maryam dakyar Dakyar dai ta hakura ta basu farhaan. Tunda farhaan ya dawo gidansu kuma aka bude masa wata babin gatan Fatima ta shagwa6a sa sosai duk abinda yake so shi take bashi amma hakan bai hanata bashi cikakken tarbiyya ba. Ansashi a makaranta direct primary aka kaisa. suna nan suna xaman su lpy matsalar dae itace Rashin haihuwa don kuwa aurensu yakai shekara biyar amma dae shiru. A lokacin ne kuma mama maryam mahaifiyarsa ta damu dole sae ya kara aure saboda ita dae tana son ganin jikokinta kafin ta mutu, yayi kokarin sanar da ita shifa haihuwa na Allah ne, amma tayi burus tace ta nemo masa mata ma, Aisha 'yar ayuba kanin babansa xata aura masa, babu yanda ya iya haka ya amince yabi umarninta. Da ya sanar da Fatima ma bata wani nuna damuwa sosai ba tace ''Allah yasa hakan shine mafi alkhairi " saboda ita kamilar mata ce mai cike da nutsuwa, a lokacin ne kuma imraan ya bijiro da auran amrah yar kasar Australia, yan uwansa sun basa goyon baya Dari bisa Dari yayinda mama maryam tace ita pah batasan da wannan xancen ba, Alh muhd ne yace mata aure kuwa babu fashi mama tunda dae ya ganta yana sonta kuma sun daedaeta kansu, so babu abinda xae sa a fasa auren nan tunda dae musulma ce. Babu yanda ta iya haka ta hakura saboda bata bijirewa maganar muhd kasancewar shine babba. Nan kuwa akayi aure aka kawo amrah dakinta a kaduna saboda a nan imraan yake aiki. itama Aisha aka kawota gidanta a kano. Ciki dae ya bayyana a jikin Fatima familyn sunyi Murna sosai da faruwar hakan. Aisha da Fatima dae xama suke na amana tamkar ba kishiyoyi ba. Fatima ta dauketa tamkar kanwarta ne, takan xaunar da ita ta koya mata karatu fannin boko da kuma islamiyya, da taga tana da fahimta sosai ne tayi magana a Alh. Muhammad aka kaita secondary itama ta fara daga jss1 saboda tayi primary a rugar su. Tare da farhaan aka kaisu jss1 din kasancewar anyi masa jumping a primary din. Haka dae suke rayuwarsu cike da jin dadi suna xumuncinsu sosai da sosae haka ma ta bangaren amrah bb matsalar komai. Cikin ta ya shiga wata Tara, haihuwa dae ko yau ko gobe. Cikin ikon Allah wata safiyar juma'a ta tashi da nakuda bata sha wani wahala sosae ba Allah ya sauketa lpy ta haifo danta santalele kyakkyawa dashi ranar suna yaro yaci suna ABDULHAKEEM suna kiransa da HAKEEM farhaan yayi murna sosai domin acewarsa wae an haifarmar kani, haka ya dauki haj Fatima tamkar uwa dan mom ma yake kiranta,, alh muhd kuma dad, danshi dae su kadae ya sani a matsayin iyaye Sam baisan akan mama MARYAM ce ta haifesa ba. Farhaan dae haj Fatima tasa anyi masa jumping still don har ya gama secondary ya tafi university a China fannin medicine and surgery. Haka hakeem shima ya taso duk family na kaunarsa, a lokacin da ya cika shekara uku ne Amrah ta haihu ita ma ta haifi yaronta namiji kyakkyawa dashi ranar suna aka sa masa ABDULRA'OUF. A lokacin ne kuma saleem shima yayi auren fari tare da matarsa lubnah. Haka dae familyn suke rayuwarsu cike da farin ciki, shima farhaan yana can yana karatunsa cike da nasarori har allah ya taimakesa ya gama degree dinsa yana da shekaru 20 a duniya, ya xama cikakken saurayi mai ji da kyau da aji, 'yan mata da dama suna rububinsa amma shi Sam ba tasu yake ba. Haka ya dawo Nigeria ya tarar da hakeem ya girma yakai shekaru biyar, ga ABDUL nan wanda aka haifesa baya kasar.
Aisha dae itama har yanxu babu alamun ciki a jikinta sunanan dae suna xamansu lafiya kalau. A daedae wannan lokacin ne kuma farhaan ya hadu da aunty afrah har tace mishi ya dauko alameen ya rike sa, Alh muhd (dad) shine ya tura farhaan US domin kula da business dinsa da yake yi a can.
lokacin da abdul ya cika 5yrs ne lubnah matar saleem itama Allah ya axurta ta da samun da namiji ranar suna aka sa mishi suna UMAR FAROUK Wanda suke kiransa da farouk. Hakeem yana karatunsa nan cikin kano shima Abdul a kaduna yake nasa karatun
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...