👉🏽MIEMAH
Page 10
Sun iso kano kowa da murnar ganin miemah, haka mom ma tayi ta murna da ta ganta (basu fada mata gaskiyar wacece miemah ba) haka kowa a family yake murna da dawowan MIEMAH cikin ahalinsu. A lokacin ne kuma abbah (alh IMRAAN) akayi transfer dinsa a wajen aiki xuwa kano, hakan yasa suka dawo kano gaba dayansu a family house suke xaune, farouk ma ya baro kaduna ya dawo kano da xama, kullum cikin fada suke da miemah duk da ya girmeta da kusan shekaru 5 in ya mata abu bata raga masa ko kadan, hakan yasa suka xama tamkar tom and jerry don babu ranar da basa yin fada. Tsakaninta da yah ABDUL kuwa shakuwace sosai a tsakaninsu, komai take so yana bata, sun shaku dashi sosae haka yah hakeem ma yana ji dasu ita da MARYAM. Tare aka saka su a school ita da MARYAM yawanci mutane suna zaton sudin twins ne saboda tsabagen kamar da suke. Rayuwa dae tana tafiya har yah ABDUL ya gama secondary dinsa, a lokacin ne kuma aka fara shirye-shiryen tura sa US wajen uncle farhaan domin kammala degree dinsa. Miemah tayi kuka sosae harda xaxza6i lokacin da xae tafi US, shima har yaji tafiyar ta fita a ransa don ko kadan baiso yayi nesa da miemah. Haka dae ya tafi ba tare da son ransa ba.
A lokacin da yaje ne kuma yaga AL'AMEEN, yayi mamaki sosai hakan yasa ya tsare uncle farhaan da tambayar waye AL'AMEEN? Shima kansa Al'ameen baisan waye shi ba, don shi duk a tunaninsa uncle farhaan ne mahaifinsa don ce masa yake mahaifiyarsa ta rasu.
Duban Al'ameen uncle yayi tare da cewa "Al'ameen yau xan fada maka abinda na jima ina boye maka, ba nine na haife ka ba.....
Dago firgitattun idanunsa Al'ameen yayi ya watsa su a uncle farhaan "waye mahaifinah? Cewar Al'ameen. Ban sanshi ba! Hawaye ne ya fara tsiyaya daga idon Al'ameen tare da tashi yana shirin barin wajen, da sauri ya abdul ya taresa tare da cewa "haba bros take it easy mn, ya kamata ka sauraresa kaji me xae ce maka" haba abdul, its too late ae, bai sanni ba, bai san ahali nah, kawae taimakona yake yake xaune dani, nidin bani da asali....... Kuka ne yaci karfinsa, shima yah ABDUL din hawaye yake, uncle farhaan ne yaxo ya rungume su duka tare da cewa "sorry my boys, take it easy kinji, Al'ameen ka dena cewa baka da asali, kana da cikakken asali duba da inda na dauko ka.Shekaru goma sha takwas da suka wuce na hadu da wata mata wacce yan ta'adda suka sassare ta tana nan kwance cikin jini tamkar matacciya, hakan yasa na dauketa na saka ta cikin mota ta na wuce da ita guess house dina nayi treating dinta har ta samu ta farfado. Nayi nayi ta fada min wacece ita amma taki don ko sunanta ban sani ba, kawae cewa tayi na taimaka mata na kaita airport ita yar Australia ce, ta tsani xaman Nigeria saboda toxarcin da aka yi mata, nayi nayi da ita ta fada min ko me aka mata amma taki ta fada min, haka na dauke ta a mota ta na wuce da ita airport, akan hanyar xuwarmu airport ne take rokona akan dan Allah in dauko mata danta Al'ameen daga cikin babbar masarauta saboda in aka barshi xasu kashe shi don ba imani ne dasu ba kuma ita dakai da sarki ismail kune rayuwarta bataso wani abu mara kyau ya faru daku, haka na daukar mata alkawarin kula da kai har karshen numfashi nah. Daga nan na kira budurwar yarima ishak yayan sarki ismail mahaifinka inn nace ta sato min kai, kuma ta dauko ka ba tare da sanin kowa ba, haka na taho dakai kasarnan ba tare da sanin kowa ba dake ahali nah. Shekaru sha uku da suka wuce xubaida ta kira ni ta sanar dani an kashe sarki ismail din ma! Amma dae xan sake tunta6ar dad akan maganar sarki ismail din don naga kamar suna da alaka dashi. Hawaye ne yake ta tsiyaya daga idon Al'ameen tare da ABDUL. Mahaifinah ya rasu knn, to ina mahaifiyata kuma pah? Am sorry to say Al'ameen naje ni har Australia na gama iya binciken da xanyi amma ban same ta ba, saboda bani da address dinta bani da hotonta besides ko sunanta ma bansani ba. Jinjina kai alameen yayi tare da cewa ba komai uncle, in tana raye wata rana Allah xae bayyana ta. Dafa kafadar Abdul yayi suka tashi a tare suka fice.
Yah ABDUL ya fara degree dinsa anan cikin US inda yake karantar CARDIOLOGY. A cikin makarantar suka hadu da sadeeq, ae kuwa nan sukaji dukansu suna kaunar juna kasancewar kamar da suke har wadansu suna tunanin su din twins ne, nan kuwa shakuwa da aminta mai karfi ta shiga tsakaninsu har sadeeq shima ya koma gidan uncle farhaan da xama suka hadu da Al'ameen suka xama aminai. Shi Al'ameen a makarantar sojoji (military school) dake US din yake, saboda burinshi knn dama ya xama babban soja. Haka dai suke rayuwarsu cike da burgewa. Kullum yah ABDUL sae yayi waya da miemah da maryam, haka xae tusa Al'ameen da sadeeq gaba yayi ta basu labarin kanwarsa, sadeeq ne ma dae mai tanka masa amma Al'ameen baya sa musu Baki kasancewar shi bai fiye son yawan magana ba, sae dae in sun ishe shi yace"kai Abdul ka dame mu pah da labarin wannan kwailar kanwar taka". Aikuwa nan xa'a fara musu don shi cewa yake kanwarsa ba kwaila bace.
Su MIEMAH dae an shiga secondary school an karo wulakanci, basa kula samari ko kadan acewar su sun girmi yin dating mate dinsu, gaba dayansu suna ji da girma a lokacin ne kuma akayi passing out din su yah hakeem ya xama cikakken soja, ya fito da babbar matsayi kuwa domin matsayin captain ne dashi. Ai kuwa su miemah nan rawar kai ta karu don yanxu jin kunkuminsu suke daedae da na uban kowa, xasu taka duk wanda suka so kuma a lokacin da suka so ba tare da an dau wani mataki ba. Dad ya daukar musu boarding guard guda uku wadanda xasu na tsaronsu Duk inda xasu je, amma karfi da yaji su MIEMAH suka mayar da guard din nan yan ta'addar su, domin cewa sukayi su basa so, taya xa'a yi da girmansu xa'a hada su da gardawa suna binsu duk inda xasu je. Hada guard din sukayi gaba dayansu suka ga mutum na farko suka ce kai ya sunanka, yace "sunana aliyu" kada kai MIEMAH tayi sannan tace to na canxa maka suna daga yau sunanka BEIGON sunan kungiyarka kuma BEIGONS xaka nemo mutane Tara a karkashinka kayi musu training me kyau amfaninku shine idan mutum yayi min babban laifi xan hadasa daku Kuyi masa dukar da sae an kwantar dashi a asibity. Kuyi masa jina jina yah Abdul xae na biyanku salary duk wata cewar maryam. Angama madams. Na biyun MIEMAH ta duba tare da cewa ya sunanka. "Sunana salman" maryam ce tace to daga yau sunanka ya koma RAMBO sunan kungiyarka kuma RAMBOS, kaima xaka nemo mutane Tara a karkashinka amfaninku shine in yarinya tayi mana laifi xamu kira ku ku xane ta". An gama ranki shi dade. Na karshen ta gani tare da cewa kai kuma ya sunanka "sunana Audu" to daga yau sunanka RAZOR sunan kungiyarka kuma RAZORS. Amfaninku shine in yarinya tayi mana rashi da'a xamu kira ku ku yayyage mata sutura, ta karashe maganar cike da iskanci. Dukansu kwashewa sukayi da dariya tare da cewa an gama ranku shidade. Haka dae aka daure musu gindi suna abinda suka so yah ABDUL ne mai biyansu salary.
Haka ko a cikin school ne malami ko dalibi yayi musu abu sai su hadashi da gang dinsu a hukuntsau daedae da laifinsu, tun Ba'a ganesu ba har aka ganesu, to ba yanda aka iya dasu saedae ayi hakuri. Alh IMRAAN ma an maidashi kaduna a wajen aikinsa, yayi niyyar tafiya da MARYAM dad yace a barta ta karasa karatunta in sun samu hutu xasu na xuwa su duka.
US 🇻🇮
Dukansu suna karatun su normal ba tare da wata matsala ba, yah ABDUL da yah sadeeq saura shekara daya su gama, shi kuwa Al'ameen har yayi passing out amma yace shi Sam ba xaeyi aiki a kasar US ba kasarsa Nigeria xae dawo yayi aiki kuma yayi alkawarin nemo duk wanda yake da hannu wajen ruguxa masa family. Hakan yasa akace xa'a maidashi sojan kasa-da-kasa amma dole akwae bukatar dawowarsa Nigeria yayi course tare da samun Karin training ta fannin sojin Nigeria. Dr. Farhaan ma ya gama aikin da yaje yi a US hakan yasa xae dawo Nigeria dan asibitin sa da dad ya bude masa a kaduna har ta fara aiki, so a kadunan xae xauna shima kuma Al'ameen a kadunan xaeyi coarse din nasa. Saura sati daya su dawo Nigeria Al'ameen ya shirya ya tafi Australia neman mahaifiyarsa ba tare da sanin kowa ba. Yama rasa ta ina xae fara neman ta tunda dae shi ba wani saninta yayi ba, gashi bashi da wani details akanta, sae yanxu ya fahimci me uncle farhaan yake nufi, donshi da a tunaninsa kawae farhaan baya son nemo masa mahaifiyarsa ne. Wani eatery dake kusa dashi ya shiga domin neman abinda xai ci, ta dan can gefe guda ya hango wata kyakkyawar yarinya da baxata wuce shekaru sha bakwae ba xaune ita da kannenta suna cin abinci suna wasansu, affan ne ya cika bakinsa da coke tare da fesa mata a fuskarta. Cike da bacin rai ta dago kanta, lahh 😮 ashe MIEMIE ce, kai affan ina wasa dakai ne, ta fada cike da hasala. Shikuwa dariya yake ta mata yana mata gwalo😝. Hasala tayi ta ciko cup din da coke xata watsa mai yayi saurin kaucewa coke din ya xuba a jikin farar T-shirt din Al'ameen. Cike da bakin ciki ya dago yana kallonta "am sorry pls, ba akai naje watsawa ba akasi aka samu, kaxo muje gidanmu in wanke ma" wani banxan kallo ya bita dashi tare da jan tsaki yace "ban nema ba, in banda rashin hankali irin naki tayaya xaki biye yaro kuxo Kuna wasan banxa a mutane, wawiya kawae mara hankali" yana gama fadin haka ya juya domin ficewa daga wajen saboda gaba daya yaji cin abincin ma ya fita a ransa, da sauri Miemie ta bishi don pah ita tana da hakuri amma in aka ta6ota bata da hakuri ko kadan, ganin yana kokarin 6ace mata yasa ta hada da gudu tare da ruko bayan rigarsa, yana tsayawa ta daka tsalle ta wankeshi da Mari tare da cewa "gobe ma in anyi maka abu bisa kuskure ka xagi mutum" tana fadin haka ta kama hannun affan da afrah suka fice daga wajen. Al'ameen tsantsar mamaki ne ta hanasa daukan mataki, wai shine yau wannan kucakar yarinya kwaila da ita har take iya marinsa? Waigawa yayi ko xai ganta amma Sam ko mai kama da ita bai gani ba, hakan yasa shi daukan alwashi daban² akan miemie, ya rantse nan gaba in suka hadu sae yayi mata abinda baxata ta6a mancewa dashi ba tunda dae shi ta mara, take yaji ya tsaneta ya tsani kalan sunanta,' Miemie ' ya ambata a fili tare da cewa xaki gane kurenki, daga nan ya wuce hotel din da xae kwan xuwa gobe.Kuyi manage
Like, comment and share, follow and vote me on wattpad @khadija yusufbaba
ALLAH ya karbi ibadunmu 🙏
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...