👉🏽MIEMAH 👈🏽
Page 8
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
**********************************
MIEMAH SPECIALIST HOSPITAL
Cikin hospital din na shiga. Masha Allah, sabon hospital ne da aka ginashi da tsari mai kyau, a yau hospital din xae fara aiki, cike yake da kwararrun ma'aikata da suka samu horo ta bangare daban² a fannin likitanci, ta bangare guda kuma mutanen da suka xo taya sa murna ne xaune a inda aka tanada don yin walimar. Kowa ya hallara kawae xuwar isowar sa akeyi.Tafe yake xuwa inda aka tanada domin yin walimar, kyakkyawan matashin saurayi ne da baxae wuce shekaru 28 ba a duniya, dogone mai matsakaicin jiki, fari ne amma ba sosae ba, fuskarsa dauke take da wani sihirtaccen kyau mai tafiyar da imanin duk wata mace da xata toxali dashi, yana da manyan ido mai dauke da xara-xaran eye lashes, amma idanun a lumshe suke tamkar mai jin bacci idan ya shanyesu kuwa yakan koma tamkar mai shan cocaine, idanunsa suna daga cikin abinda ke sa 'yan mata macewa a kansa, hancinsa dogo har baka, yana da light pink lips 💋 'yan sirara dasu gwanin ban sha'awa. Fuskarsa gewaye take da kwancaccen saje baki sidik wanda ya hade da 'yar karamar gemunsa me kara wa cute face nashi kyau😍 haka sumar kansa ma yake baki sidik kuma a kwance luff a cikin kan. Dr. ABDULRA'OUF IMRAAN SA'EED (Dr. A. I) kenan, cike da nutsuwa yake tafiya, gefensa yah hakeem ne rike da hannunsa, so confused 😖 na kasa tantancewa tsakanin yah ABDUL da yah hakeem wanne yafi kyau🤔 gaba dayansu sun hadu, yah hakeem sanye yake da da farar T-shirt da wandon sojoji kansa sanye da pacing cap irin na sojoji, bayansa kuma sauran likitocin asibitin ne. Suna karasowa cikin hall din aka fara tafi, iyayensa ne da yan uwa da abokan arziki a hall din, da kuma manyan kasa abokan mahaifinsa da suka samu damar hallarar taron, sae kuma abokansa (sadeeq dae bai samu xuwa ba saboda wani muhimmin uzuri da ya rikesa) ta gefe guda kuma 'yan matan da sukayi school tare ne. YAH ABDUL! Ya jiyo siririyar muryarta ta ambaci sunansa, daga kai yayi ya hangosu ta gefe guda xaune ita da MARYAM dukansu suna sake masa murmushi, shima murmushin da ya bayyana dimple da 'yar siririyar wushiryarsa ya sake musu tare da daga musu hannu. Haka aka fara gudanar da walimar cike da tsari, anci an sha an kuma fadakar an taya sa murna tare da yi masa fatan alkhairi, ya samu gifts da yawa daga hannun mutane daban-daban, da haka dae taro ya watse amma yah ABDUL kam yana cikin jama'a, yan matan school da sukayi makaranta tare kowacce tana son daukan pic dashi, miemah ranta yayi mugun baci ganin yanda yan mata ke rububinsa "lahh besty ga waccan👉👩 tana kokarin rungume yah Abdul" cewar maryam. "Kutmelesy yayanah take kokarin runguma, an fada mata shi dan iska kalanta ne😾". Tashi tayi da niyyan xuwa taci mutuncin yarinyar, maryam tayi saurin rike ta tare da cewa "aa besty, yau pah ranar farin cikin yah abdul ne, don't ruin it pls kawae mu hada ta gang dinmu su koya mata hankali". "amma ta jawa kanta wlh yau sae tayi kwanan asibity". Cewar miemah, shi kuwa yah abdul dan ture ta yayi tare da excusing kansa ya bar wajen ya wuce office din sa domin hutawa. Maryam ce ta daga waya tare da cewa "yanxu besty su waye xamu kira su ladabtar da Ita ne, kodae xamu kira mata razors ? ". Aa besty bar yar iskar, kirawo mata RAMBO kawae su tare ta a hanya su xane mata jiki" hakan kuwa akayi, suka kira RAMBOS, bayan sunxo ta nuna musu yarinyar "ku tabbatar kun mata jina jina" cewar miemah sannan suka wuce office din yah Abdul Dan sunga time din da yayi hanyar office din, kuma sunga wata budurwa tabi bayansa.
My Abdul wacece kuma miemah da har ka bude hospital naka da sunanta, ni ai a tunanina da sunana xaka bude, na xaci xan samo an rubuta feenah specialist hospital ae ko dan kaunar dake tsakaninmu. Abinda su miemah sukaji kenan yayinda suka karasa bakin office din yah Abdul. A haukace suka bude office din, miemah ta karasa gaban ta cike da takun kasaeta "so kike kisan Ko wacece miemah??? " cewar maryam "kiyi shiru besty kar Ki kula ta tayi dirty da yawa" juyawa kan Abdul da ya sunkuyar da kansa yana dariya kasa-kasa tayi, dama shima ya gaji da nacin feenah, shi bai ta6a cewa yana sonta ba amma ita kullum tana cikin yayata shi a media wae fiance nata ne dan har an kusa aurensu ma "yah Abdul dagaske soyayya kk da wannan kucakar" dago kansa yayi tare fa sake mata murmushi amma baice komai ba. Ita kuma miemah ganin haka sae tayi zaton soyayya suke da gaske kawae sae taja hannun maryam suka fice daga office din, suna fita miemah ta fashe da kuka "besty Dan Allah kiga yah Abdul ya rasa wacce xaeyi soyayya da ita sae wannan kucakar?? ". Miemah kodae kina son yah Abdul ne? maryam ta jefo mata tambayar, dago kanta MIEMAH tayi cike da mamaki tare da cewa "haba maryam, wace kalar tambaya ce wannan, kinfi kowa sanin abinda ke tsakaninah da yah Abdul, taya xakice soyayya ce. "To soyayyar haramun ce a gareku? Iye? Nace ko shidin muharraminki ne da aure bai halatta a tsakaninku ba, Ina dae cousin bro dinki ne ba ciki daya kuka fito ba, kuma dae naga kullum in kika ganshi tare da wata sae kinyi kuka, in ba so ba to meye shi? ". Sake baki MIEMAH tayi tana kallon maryam kafin ta fara magana cike da neman fada "Gaskiyarki maryam, kawae ki fito fili kicemin ba uwa daya ce ta haifemu da yah Abdul ba mn, yau kin nuna min iyaka ta, kece uwa daya ta haifeku da yah Abdul, to ba komai naji, daga yau bani bani ke kuma bani ba Abdul" cewar miemah tare da juya wa ta fara tafiya. Oho ke kika sani dae, daga fadar gaskiya sae Ki maida ita fada, kyaji dashi dae ni ba ruwa nah. Nan kuwa sukayi fada baran-baran (dama sun saba yin fadarsu) miemah ta wuce ta shiga motarta kuma tace kar maryam ta shigar mata mota tunda dae ba nata bane. Tana tafiya sae ga yah hakeem ma ya fito xae tafi gida, this tun daga nesa da ta hangoshi ta sake murmushi tare da sunkuyar dakanta tana wasa da 'yan yatsunta, shima tahowa yake yana sake wata kayatacciyar murmushi. "A'ah baby ya na ganki ke daya, Ina miemah pah ". Dan Turo baki tayi cike da shagwaba sannan tace ''ta tafi gida kuma tace kar na shigar mata motar ta kawae don munyi cacar baki kadan" me ya hadaku. Cewar yah Abdul da ya karaso wajen yanxu tare da hararar maryam din. "kawae don nace kai cousin bro dinta ne" dafe kansa yayi "omg" maryam i warn u for the last time, u have to stop making her angry" harararsa hakeem yayi tare da cewa "kaima sae kayi warning miemahr ae ta dena saurin fushi" murmushi kawae yayi tare da tafiya yana cewa nidae kun jawo min rigimar miemah saboda yanxu fadar kaina xai koma. Sannan ya shiga motarsa, shima hakeem mota suka shiga tare da maryam suka wuce gida.Miemah tana parking a compound din da farouk taci Karo, harara ya watsa mata itama kuwa ta Rama tare da jan tsaki tayi tafiyarta tana cewa bani da lokacinka mara aikin yi kawae sae sa ido. Shima yau baiyi niyyar rigimar ba shiyasa ya rabu da ita. Side dinsu ta wuce direct ta shige bathroom ta watsa ruwa tare da dauro alwala sannan ta dauro towel ta fito, maryam ta tarar xaune a bakin gado, harararta tayi, itama maryam din ta Rama tare da cewa yah Abdul yana nemanki, daga haka itama ta shiga bathroom din. Ko kula ta miemah batayi ba ta saka hijab ta kabbara sallah, itama maryam din da ta fito sallar tayi. Bayan sun idar Miemah ta wuce kitchen ta debo musu abinci, suka zauna suna ci suna hararar juna. Har suka gama, suka zauna suna daddanna wayar su. Maryam ce tayi breaking silence din ta hanyar cewa "wato miemah kece da laifi kuma shine bazaki bani hakuri ba ko" ke ya dace ki bani hakuri ae. Cewar miemah "to kiyi hakuri dae ba dan halinki ba" cewar maryam. Dan hararar wasa miemah tayi mata sae kuma suka sa dariya gaba dayansu daedae lokacin da yah hakeem ya shigo kenan. Shima murmushi yayi tare da cewa "tom and jerry har kun shirya kenan" dariya sosae maryam tayi tare da cewa "yah hakeem ka manta ai ni ba jerryn ta bane, jerry dinta yana kaduna duk randa taje xasu Dora daga inda suka tsaya" shima yah hakeem dariya ya fara tare da cewa "ae daya jerry din nata yana gida". Ae bata tsoron waccan ko kadan, ni wlh na kagu next week tayi muje wajen rantsar da su yah AL'AMEEN 💃" harararta MIEMAH tayi tare da cewa "kekam wlh kin fiye kalian dangi, ta ina waccan me fuskar aljanun ya xama yayanki" dariya sosai dukansu suke banda miemah da take ta hararar su. Maryam tace wa yah hakeem "sweetheart saboda yafita kyau ne pah shine take ce masa me kama da aljanu, ni wllh sometimes ma sae naga kaman suna kama da ita kwayar idonsu pah iri daya, wlh yah hakeem guy din ya hadu" kuka miemah ta fara tare da cewa "wlh sae dae ko dake yake kama amma dae nikam badae ni ba, Ae dama na sani ni duk gidan nan babu mai sona sae yah Abdul " tana fadin haka ta fice ta wuce bedroom din mummy. Sukuwa dariya sukayi tare da cigabahirarsu suka cike da kaunar juna sunayi suna darawa.
👉🏽MIEMAH tana shiga falon mom ta tarar da yah ABDUL xaune a cikin falon yana cin abinci, tsayawa tayi ta kura masa ido tana kallon shi cike da burgewa, a jikinsa yaji ana kallonshi hakan yasa shi dago ido, caraf kuwa idonsu ya hade waje daya, murmushinsa mai rud'a ta ya sakar mata ita kuwa harararsa tayi tare da turo Baki ta fara magana "yah abdul wlh kaban kunya, yanxu ka rasa wacce xaka yi dating sae waccan kucakar😐" MIEMAH to idan banyi dating dinta ba wa kike so nayi dating tunda dae ni Ba'a sona laifi dan kadan ma in nayi an ringa suspecting dina kenan kamar wanda yayi kisan kai🙄". Karasa shigowa falon tayi tare da xama kujerar da ke opposite dinsa sannan tace, shknn dae komai ya wuce. Murmushi yayi tare da daga mata hannu alamar jinjina 👍 tare da cewa that's my girl. Hararar wasa tayi masa sannan suka cigaba da hira irinta wa da kanwa.
Besty ya naga kina ta hada kayanki badae tafiya xakiyi ba?? Wlh besty tafiya xanyi bana son nayi missing din xuwa passing out din su yah AL'AMEEN. Hada harda kayana nima xan biki wlh sae na Rama abinda yamin baxan ta6a barinsa ba. Dariya maryam tayi sannan tace "wannan karan kam sae nayi video dan wlh fadarku da guy dinnan burgeni take, ta karashe maganar cike da xolaya.
Kuyi manage, typing da wuya karantawa kuwa babu wuya zirrrrrr har kun gama
Like comment and share, follow and vote me on wattpad @khadija yusufbaba
Allah ya karbi ibadunmu 🙏
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...