👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 27
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
6:30am.
Dakyar take bude idanuwanta wa'anda sukayi mata nauyi tsabagen kukan da ta sha. Akan sallaya ta hangoshi xaune.Kawar da kai tayi a xuciyarta tace mugu kawai. Dan juyowa yayi ganin tana kokarin tashi yayi saurin tasowa yaxo yayi saurin daga ta harararshi kawae take tana cigaba da tsine mishi a zuciyarta, toilet ya kaita ya taimaka mata ta gyara jikinta sannan ya barota ta tsarkake kanta.
Tana gamawa ta fito tana dingisawa da kyar tana dafa bango. Tasowa yayi cikin sauri da niyyar taimaka mata. Hannu ta daga mishi alamar ya dakata tare da watsa mai harara sannan ta wuce wajen pray mat ta kabbara sallah. Murmushi kawai yayi.
Sallah tayi, tana idarwa ta jawo waya ta kira Maryam. Itama Maryam lokacin sae kuka take ta yiwa yah hakeem. Tana daga wayar miemah ta fashe da kuka tana cewa "wlh maryam kixo ki dauke ni daga wajen wannan mugun, wlh in na sake kwana daya mutuwa xanyi, kinga yanxu ma duk ya kakkarya min kafafu dakyar nake tafiya"
Itama maryam kukan ta sake fashewa dashi "wlh MIEMAH nima gidanmu xan tafi na fasa auren, Allah duk kafafuna nima sun gurde dakyar nake iya tafiya". Dariyar shiriritartar su yah hakeem kawai yake, Al'ameen kuwa duk tausayin Miema yake, sam baya so ya ganta cikin damuwa.
Kar6e wayar yah hakeem yayi tare da cewa "MIEMAH sai hakuri wannan shine aure, kowacce mace da haka ta saba, haka xakiyi hakuri ki cigaba da xaman aure kina biyayya ga mijinki, Insha Allah aljannarki tana karkashin kafanshi. Yana gama fadin haka ya kashe wayar.
Kuka ta fashe dashi sosai tana cewa "shikenan yah hakeem ma ya daina sona". A damuwance Al'ameen ya taso ya karaso inda take ya tsugunnah tare da riko hannayenta, cikin lallashi ya fara magana "am sorry Miema, kinji? Kiyi hakuri baxan sake ba wlh har sai kin nema....... Harara ta watsa mai. Murmushi yayi tare da cewa ''thanks for everything MIEMAH, I love u....! Daga jajayen idanunta tayi ta watsa cikin nashi a hankali ta furta "I hate u yah ameen". Kalma mafi ciwo kenan a rayuwarshi, wai sai yaushe bakin Miema xai daina furta kalmar tsana gareshi ne? Murmushi yayi tare da cewa "thank u I know wataran xaki furta kalmar kauna gareni"
"Xan so Allah ya kar6i raina kafin xuwar ranar" abinda ta fada kenan tare da mikewa tana dingishi ta haye gado ta kwanta bacci ya dauketa.
ABUJA
Anyi biki an gama dangi na nesa duk sun koma su Miemie ne kawai suke nan.After 2weeks.
Yah sadeeq ne xaune a falon Abbie, ummie tana gefe tana yanka fruits.Gyara xama yah sadeeq yayi tare da cewa "Abbie Abdul pah yaga Miemie yace yana sonta pah"
Fadada murmushin su sukayi har da Ummie cike da farin cikin maganar. Abbie yace "masha Allah naji dadin wannan magana sosai wlh, ai Abdul yaron kirki ne, in sun daidaita kansu nikam bani da matsala ai na bawa Abdul auren Miemie.
Dago kai ya sadeeq yayi fuskarshi yana bayyanar da damuwa yace "but Abbie miemie, pah ta ce wai bata son Abdul Dr fairouz take so.
Cikin sauri Ummie ta dago kai tana cewa "bata da hankali ne ita Miemien, taci sa'a ma har mutum kamar Abdul yace yana sonta shine xata ce wani bata sonshi tana biyewa waccan fairouz din, sam yaron bashi da kamun kai ya fiye tara yan mata, to nidae indae ni na haifi Miemie to bata da miji in ba Abdul ba tunda dai har ya furta cewa yana sonta.
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...