Part 22

17 3 0
                                    

👉🏽MIEMAH 👈🏽

Page 22
🍀🍀🍀🍀🍀🍀
   🍃🍃🍃🍃🍃🍃
        🌾🌾🌾🌾
              🌺🌺🌺

Typing 📲
      Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
 
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽

Bismillahir-rahmir-raheem

Dan allah kuyi hakuri ku dena bina PC akan complete din MIEMAH🙏. Bansan ta ina xan samo muku ba tunda dae yanxu nake rubuta book din.

    Ina mai baiwa daukacin masoyanah wanda littafin MIEMAH yasa su kuka jiya da yau hakuri.

     Masu shirin daukan fansa kuma ku shirya😂, an kusa xuwa daukan fansa, kuma banason ragwaye, in kinsan baxaki iya bada ranki ba kar kije daukar fansa.
***************************************
Miemah ku shirya ku koma school next week xaku fara exam.  "To yah Abdul kace wa mom ta bar min afrah in tafi da ita".  "Miemah kin fiye rigima, afrah tayi karama sosai, ki barta yanxu sae next semester sae ki tafi da ita".   Dakyar suka yarda suka bar Afrah itama sae kuka take saboda su take gani a matsayin iyayenta.

     Daedae lokacin da xasu shiga jirgi ta tuna lokacin da xasu tafi, uncle farhaan yana musu bye bye tare da cewa *sae wata rana*  a tare suka saki kuka suka karasa shiga jirgin.

Maryam ki dena kuka muci gaba da yi mishi addu'a. Kema ki dena kuka MIEMAH.

   Goge hawayen su duka sukayi, haka trip din yau ya xame musu so silent har suka isa.

     Su husnah sunyi musu gaisuwa sosai na rashin da akayi, suma sun so aka tafo da afrah.

Washe gari bayan sun dawo daga school, MIEMAH ta fita tare da kiran wani abokinta jack.

    Jack soja ne, haka kawae Allah ya hada jininsa da na su MIEMAH.

Bayan sun gaisa tace "jack so nake kamin training sosai kamar soja!".  Dariya yayi tare da cewa "ke kuma me ya hada ki da yin training na soldiers". Bata boye masa komai ba game da abinda ya samu uncle farhaan ta fada mishi da kuma abinda take shirin yi.  Shima yaji babu dadi sosai game da abinda ya samu uncle farhaan.

      "MIEMAH xan taimaka miki, xan yi miki training sosai yanda xaki iya tunkarar kowa kai tsaye, duk lokacin da kike da time kawae kixo ki, in ina da time xanyi training dinki in kuma bani dashi xan hadaki da yara nah".  Godiya tayi sosai. Nan take a wajen ma ya fara bata training.

SECRET PARLOUR
   Duk wani shege yau ya taru ya hallari secret parlour, party sukeyi na musamman saboda sun cika umarnin boss dinsu na kashe uncle farhaan da sukayi.

    Daya daga cikinsu ne ya mike tare da cewa "amma fa ina ga kamar kashe farhaan da mukayi babbar kuskure ne! Abdul shine babban shegen, shi ya dace mu fara hallakawa kafin farhaan"
    "Me yasa kace haka? ".   Boss ta watso mai tambayar.

     Gyara tsayuwa yayi tare da cewa "yanda muka kashe farhaan Kuna tunanin xasu barmu haka ne? Yanxu Abdul xae fara farautar mu, kuma komai yake yi yana yinshi ne cikin sirri dan haka muma ya kamata mu sauya taku!''. 

    Tabbas maganar ka gaskiya ce, muma ya kamata mu sake adding more security ta yanda baxa'a ganemu ba, dole ne muma mu koma yin komai cikin sirri.

     Xamu bar haduwa cikin gari, xamu koma cikin jeji mu gina hall dinmu ba tare da kowa ya sani ba, a xahirin gaskiya kuma ko a titi muka hadu baxamu nuna munsan juna ba, a haka xamu cigaba da tafiya har xuwa lokacin da xamu gano wanene Abdul mu gama da tarihinshi shima kamar yanda muka gama da FARHAAN.

     Dukansu ihu sukayi tare da tafa mata saboda sun yarda da shawarar boss din tasu sosae.

     Shugaban kidnappers ne ya daga hannu  alamar yana da magana, nan ta bashi damar yin magana "boss ya kamata mu nemo ko wanene DSP A. I, jami'in hukumar DSS ne dake gudanar da aikinshi cikin sirri, yana kawo baraxana sosai a cikin harkallar mu, ya kamata musan abinda xamuyi"

MIEMAHWhere stories live. Discover now