👉🏽MIEMAH 👈
Page 18
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
Mom ce tace "wace kuma miemie? Daedae lokacin doctor ya shigo, allurar bacci ya mata nan bacci ya dauke ta, sannan ya juyo ya fuskanci mom ya fara mata bayani "kar ki damu ba wani matsala bane buguwar da kanta yayi ne ya haddasa mata hakan amma in ta farka xata dawo normal. Ajiyar zuciya mom ta sauke tare da yin hamdala ga Allah dan ita sam bata son wani abu ya samu miemah.MIEMAH bata farka ba sae asubah, MARYAM ta hango xaune akan sallaya "besty besty..... Cikin sauri maryam ta taso tare da rike ta "MIEMAH sannu, kin tashi? Me kike bukata? So nake nayi sallah. Okay tashi.
Nan ta taimaka mata ta kaita toilet tayi alwala sannan ta Rama sallolin da ake binta.
7:00am mom ta iso musu da break fast.Jikin MIEMAH yayi sauki sosai a ranar aka sallamesu, suna fitowa harabar asibitin ta hango Al'ameen tsaye a jikin mota da alama shi xae mayar dasu gida nan gabanta ya fadi.
Ita yanxu a duniya babu wanda ta tsana kamar AL'AMEEN, sannan kuma wani mugun tsoronshi take, alkawari ta daukar ma kanta ko me Al'ameen xae mata baxata sake tanka mishi ba saboda tasan xae iya halaka ta.
Sunkuyar da kanta kasa tayi ba tare da ta kalli gefen da yake ba, shima ko kallo bata ishe shi ba. Tanaji suna gaisawa da mom amma ita mota kawae ta bude tayi Saurin shiga back seat, mom ma back seat ta shiga. Maryam kamar xatayi kuka ganin ita aka bari xata shiga front seat.
She's totally nervous dan ita ma wani mugun tsoronshi take ganin yanda ya hade rai a haka dae suka isa gidan.
Part din mom suka wuce shi kuma ficewa yayi daga gidan gaba daya.
Duka maryam ta kaiwa MIEMAH tare da cewa "shine kk barni da wannan masifaffen koh? Xillewa tayi tana dariya tace "to ni ina xan iya da masifarshi.*************************
2weeks later
Ta ware sosae babu sauran ciwo da take ji yanxu.
Bacci me dadi ne ya dauke ta bayan sallar asubah, cikin baccin take jin maryam tana Tashin ta, "MIEMAH ki tashi kije kiyiwa yah AL'AMEEN girki, yau kaina ciwo yake da Na girka mishi". Mika miemah tayi cikin magagin bacci tace "maryam ki rabu dashi, kawae in mun tashi sae mu kaimasa wanda 'yan aiki suka girka". Miemah kina ganin baxae gane ba girkinmu bane......... Cike da hasala miemah ta hayayyako kanta tace "in ya fasa ganewa yaci ubansa". Shiru maryam tayi tare da sake jan bargo ta rufe kanta dan wani mugun ciwon kai take ji ko kadan bata son hayaniya. Itama MIEMAH bargo taja tare da cigaba da baccin ta.
Sae 9:00 sannan suka tashi sukayi wanka sannan MIEMAH ta nufi kitchen ta hado musu breakfast sannan ta hadawa masifaffen nashi a basket.Nasu ta dauko ta kai musu daki suka ci suka koshi sannan sukayi shirin sport, dogon wando da riga mai dogon hannu na ball suka saka dukansu, parking din gashinsu sukayi da karamin ribbon sannan suka dau pacing cap suka sa suka fito parlor suka dau basket din abincin Al'ameen suka nufi side dinshi.
Gaba daya baya jure yunwa, kullum 8:00am yake break gashi yanxu har 10:am har ya dan rame sae manyan idon da suka sake fitowa.
Kallonsu kawae yake, gaisheshi sukayi amma bai amsa ba, ganin irin kallon da yake musu yasa suka gane yau din ba mutunci a lamarinshi, dan haka suka nufi hanyar dining dan jera mishi break din, tsawa ya daka musu tare da cewa kuxo nan. Duk jikinsu na rawa sukaxo, table din gabanshi ya nuna musu, hakan yasa suka fahimci akan table din xasu jera mai.
Fara serving dinshi sukayi, kallon abincin kawae yake, tun daga yanayin yanda yake kallon abincin cikin maryam ya fara kugi saboda tasan ya fahimci ba girkinsu bane, yasha yi musu warning akan su kadae xasu na yi mar girki baya son girkin yan aiki. "Wa yayi wannan girkin!? Nan suka fara xaxxare ido. Tsawa ya sake daka musu tare da cewa "wa yayi wannan girkin!? Cikin karfin hali MIEMAH tace "nice". Karya kikeyi, ku fada min gaskiya ko in xane ku anan, ya fada yana xaro belt dinsa.
Cikin sauri Maryam bakinta na rawa tace "yar aiki ce!
Who brought this idea? Ya fada yana kallon both of them. "Nice" ta bada amsar bakinta na rawa.
Saboda kun raina ni ko? Bankai in sa ku yin abu kuyi ba.
Oyah up-and-down all of u, xubewa sukayi a kasa suna bashi hakuri.
Wlh in bakuyi abinda na saka ku ba sae nayi shut daku. Sun san karamin aikinshi ne Wnn, hakan yasa suka mike suka fara up and down din. Kusan 30mins sunayi sun gama gajiya saosae sae kuka suke suna hawaye. Tsawa ya daka musu "ku rufan bakinku wlh ko kuma in xane ku anan.
Tsit sukayi da bakinsu sae hawaye dake cigaba da tsiyaya daga idonsu, kusan 1hr sannan ya dakatar dasu gaba daya cinyarsu tayi tsani, dyar suke tafiya.
A tunanin su xaice su tafi sae kuma suka ga ya sake basu wani aikin. "Ku gyare min part dinnan gaba daya". Yana gama fadin haka ya shige bedroom din shi,
Gyarawa suke suna kuka a haka sae da suka gama tsaff sannan yace su shiga kitchen su mashi girki.
Hakanan suka shiga suna girkin suna tsine masa, MIEMAH cikin kuka tace "besty wlh na tsane shi" daedae lokacin ta ciko hannayenta duka biyu da attaruhu tasa a blender. Itama MARYAM tace "Allah ya isa tsakaninah dashi". Itama ta ciko hannunta da gishiri tasaka akan kwai guda biyu da ta fasa. Indomie da kwae xasu soya mar dan basu da time din girki me wuya. Wlh yau baxaeci girki me dadi ba. Haka suka ci gaba da girkin suna kuka suna xaginsa.
Suna fitowa suka ganshi xaune a falo da haka suka je sukayi serving dinshi, tun da ganin abincin ya hadiye miyau, yanda yaga abincin yasan dole xaeyi dadi, ga yanda kamshin attaruhu yake tashi a wajen, suna gama serving dinshi yace su tafi, ae kuwa da gudu suka fice, saeda suka isa part dinsu sannan suka fara rike cinya suna xubda hawaye.
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...