👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 11
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
Kwanan shi daya a Australia ya koma US, yaso ya sake haduwa da miemie amma Sam ko mai kama da ita bai gani ba haka ya tafi amma yaci alwashin in suka sake haduwa sae ya koya mata hankali.
Ranar asabar shida uncle farhaan suka taho Nigeria suka bar Abdul da sadeeq a can. Kasar US ta hado sa da Securities wadanda xasu n kula dashi saboda basa so wani abu ya sameshi. Karo na farko kenan da yaxo Nigeria a rayuwarsa tun lokacin da farhaan ya tafi dashi. Hawaye ne ya fara tsiyaya daga idon shi, Sam baya iya jure wa idan ya tuna da Iyayen sa, wannan itace kasar haihuwar sa, inda aka haifesa, wai shin wadansu marasa imanin ne suka tarwatsa masa family, suka rabasa da iyayensa, tabbas baxae ta6a yafe musu ba they must pay for what they have done! "I wish an barni nima sunkashe ni...... Abinda ya fada knn a fili lokacin da suka gama fitowa daga jirgin, da sauri uncle farhaan ya rufe masa baki tare da cewa stop it Al'ameen, nima ina kan bincike insha Allah xan nemo maka inda mahaifiyarka take. "Ina ne BABBAR MASARAUTA! " shine tambayar da AL'AMEEN ya watso wa uncle farhaan. Kar ka damu Al'ameen xan kaika har cikin babbar masarauta nida kaina amma ba yanxu ba, abinda nake so dakai yanxu shine ka nutsu ka kwantar da hankalinka ka gama aikin da aka turo ka, kasan ba'a tunkarar makiya kai tsaye, gashi bamusan su wanene masu kulla sharrin ba, so dole sae Munyi shiri, Munyi bincike. Daga masa kai Al'ameen yayi alamar gamsuwa. Still dafa kafadar sa farhaan yayi tare da cewa muje gida sae mu karasa maganar a can.
Da haka suka tafi gidan uncle farhaan dake kadunan, wanka sukayi suka sake shiryawa sannan suka wuce eatery suka ci abinci sannan ya komar da AL'AMEEN gida shi kuma ya tafi xuwa gidansu MARYAM.
Da sallama ya shiga falon Ammi (amrah) ita kadaice xaune a falon, da fara'arta ta amsa masa tare da cewa "Aa mutanen america, saukar yaushe" shima da fara'arsa ya amsa da "yanxun nan wlh" tare da xama a kujerar da ke pacing dinta. Nan suka fara gaisawa tare da tambayar sa Abdul, ya sheda mata yana nan lafiya. Aahh FARHAAN saukar yaushe? Cewar abbah (alh imraan) dake saukowa daga stairs. Yanxun nan wlh Abba. Nan suka gaggaisa. Ina MARYAM pah, naji gidan shiru. Maryam ae tana kano tare da MIEMAH yau sun samu hutu mah I think gobe xasu taho. Cewar Ammi. Dariya farhaan yayi tare da cewa "iyayen rigima, fatan dae yanxu sun rage rigimar " rigima ae sae ma abinda ya karu, Abdul da hakeem sun daure musu gindi. Nima goben nake tunanin xuwa kanon ai. Nan suka ci gaba da hirarsu irin ta family har sae da yayi sallar isha'i sannan yace wa Ammi tasa mishi abinci a flask daedae cin mutum biyu, hakan kuwa tasa mishi ba tare da tambayar shi da wa xae ci ba.
Ya tafi musu dashi suka ci tare da AL'AMEEN, sannan suka dan ta6a hira tare da tattauna yanda xasu fara tunkarar BABBAR MASARAUTA.
Shidae farhaan bashi da wani buri da ya wuce ya sake haduwa da afrah ya damka mata amanar da ta bashi, kullum cikin addu'a yake Allah ya barshi da ranshi ya sake haduwa da ita ya mika mata amanarta.
Washe gari
Farhaan ya gama shirinsa tsaf xuwa kano. Dakin Al'ameen ya shiga ya sameshi kwance yana bacci, dan kare masa kallo kadan yayi tare da yin murmushi ya shafa kanshi tare da cewa "son, my boy, oyah wake up" a hankali ya fara bude kyawawan idanunsa har ya sauke su akan uncle farhaan , dan murmushi kadan shima yayi sannan ya mike ya xauna bakinshi dauke da addu'ar tashi daga bacci. Good morning son. Morning uncle. Nan suka gaisa sannan yace "Al'ameen xan wuce kano yanxu kuma xan kai one week acan, hope u can manage to live lonely there? " murmushi yayi tare da cewa "sure, I can" OK xan nemo maka kuku wanda xae na girka maka abinci ko?? Aa uncle kar ka damu, xan na xuwa eatery. Ok am leaving. Save trip uncle ya fada tare da tashi ya rakashi xuwa compound ya shiga motarsa. Shi kuma Al'ameen ya koma ciki.Su MIEMAH an samu hutu sai shirin tafiya kaduna suke. Karfe 12:00 suka shirya suka tafi da motar MIEMAH, suna tafiya FARHAAN ya iso cikin kano shima sunyi sa6ani dasu Miemah knn.
Da gudu suka je suka rungume Ammi tare da cewa Munyi missing din ki Ammi tare da kissing chic dinta. Itama dariya take cike da farin cikin ganin Yaran nata tace "miss u more my twins" kyalkyalewa da dariya sukayi tare da cewa Ammi kema twins din kike cewa? Dole ince twins mn. Ammi ina Abba? Cewar maryam. Abbanku yana wajen aiki. Kun hadu da farhaan kuwa? Lahh dama uncle farhaan ya dawo? Suka hada baki wajen furtawa. Eh jiya ya dawo yau kuma ya wuce kano. Wayyo allah da mun sani wlh da bamu taho ba munyi missing uncle sosai, koh besty? Wlh kuwa. Ammi me kika dafa mana ne? Cewar miemah. A'a ni ban dafa muku komai ba, nasan ku da shegen tsiri, sae na 6ata lokaci nayi muku girki kuxo kuce baxaku ci ba, in Kuna so ku shiga kitchen ku girls. Dukansu turo baki sukayi, to Ammi babu snacks ne? Gaba daya sun kare. Ammi yanxu mu 'ya'yanki xamu dawo amma babu abinda kika ajiye man. Cewar miemah cike da shagwaba . Bunch din 200 Ammi ta dauko ta Miko musu tace gashi kuje eatery kuyi order abinda kuke so. Kar6a sukayi dukansu suna turo baki sannan suka fice suka nufi eatery.
Cike da nutsuwa suke driving suna dan tadinsu har suka isa eatery din sukayi parking suka fito suka nufi wajen cin abincin, xama sukayi tare da odar snacks da drinks suna xaune suna ci suna tadinsu suna murmushi. Sun kusa kammalawa kenan wayar MARYAM tayi kara, dubawa tayi taga yah hakeem ne ke kira, murmushi tayi tare da tashi tace "miemah jirani ina xuwa" tabe bakinta tayi ba tare da tace komai ba ita kuma maryam ta tashi tabar haraban wajen.
Tsawon mintuna goma MIEMAH tana nan xaune tana jiran maryam amma shiru bata iso ba, hakan yasa ta Mikewa ta fara dudduba ta hannunta rike da cup cike da lemo tana sipping, tafiya take tana waige waige not minding wake gabanta ko bayanta daedae lokacin shigowar Al'ameen wajen kenan, ba tare da ta kula ba taci karo da wani table tayi baya baya xata fadi cikin Sauri ya tareta ta fada kirjinsa lemon hannunta ya xube a jikinsa gaba daya, dago kanta tayi cike da firgicin watsa masa lemon da tayi, daedae lokacin da shima ya dago kansa idonsu ya hade cikin na juna, xaro idonsa yayi tare da maganar xuci yace ITA CE ta watsa min lemo kuma ta mareni a Australia! MIEMAH kina ina ne, ta jiyo muryar maryam tana nemanta kokarin xamewa daga jikinsa take tare da cewa gani nan, hakan kuwa ya kara tabbatar masa da xarginsa akan itace ta watsa mai lemo saboda waccan din ma sunanta irin haka ne dan haka yayi saurin damke hannunta tare da cewa babu inda xaki yau sai kinsan ni kika mara!............. ✍
Saura kuma ace banyi typing ba🙄🙄 kuyi manage, sae ranar Monday xanci gaba. Sam comment dinku yayi kasa, bakwa min sharhi yanda ya kamata shiyasa nima banayi muku posting yanda kuke so, pages din MIEMAH ina dasu da yawa a wattpad duk ranar da naga comment dinku yamin yanda nake so xakuga post sau biyu, ga wannan dae ku karanta sae Monday xanci gaba
Like comment and share, follow and vote me on wattpad @khadija yusufbaba
Allah ya kar6i ibadunmu🙏🏽
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...