Miemah part 39
Kowa dake wajen nan jikinshi rawa yake da jin wannan batu, kareema kareema ta mutun ma amma ayyukan da ta aikata baxasu tarwatse ba.
Waziri ne ya fice tare da kiran liman. Liman babban malami ne sosai kuma yana harka da aljanu, bawae tsubbu yake yi ba, kawai dae yana alaka da aljanu ne.
Ko magana bai tsaya yayi da ita ba ya debo wani magani ya barbada a dakin, sannan ya fara addu'o'i.
Wani raxanannen ihu aka sake, saeda kowa wajen ya tsorata. Malam ya isa haka, ya isa wlh xan dawo dasu.
Liman bai tsaya ba sae da ya tabbatar ta jigata sannan yace ya dawo dasu duk inda ta kaisu.
A wahalce tace "wlh ban kaisu ko ina ba, a dakin nan ma barsu kawae labule nasa a tsakaninku da su, kareema tace bata so a fidda su daga nan, tafi so su karashe rayuwarsu a dakin tarihi, shiyasa ban fita dasu KO ina ba, kuma duk lokacin da aka shigo dakin nan labule nake sawa tsakaninsu da mutane shiyasa babu wanda ya ta6a ganinsu"
Ikon Allah, kowa jinjina irin rashin imani na kareema yake a ranshi, liman yace "to maxa yaye labulen"
Malam baxan yaye ba, baxan ta6a cin amanar kareema ba.
Karatun alqurani malam ya koma, nan take ta koma yin ihun da take tana bada hakuri shiko baima san tanayi ba. Saeda ya jigata sosai face xata yaye sannan ya tsaya.
Oya, ki yaye labulen. Nan take su farhaan suka bayyana. Da gudu aka karasa inda duke, nan take aka kaure da koke-koke ana tsinewa kareema.
Liman ne yace "ya isa haka, abinda ya dace shine mu bar nan mu koma cikin masarautar.
Hakanan aka koma cikin masarauta, su farhaan sukayi wanka suka fito fess da su.
Mom afrah dae tana tare da rabin ranta, yau rana ce ta farin ciki a garesu wacce baxasu ta6a mancewa da ita ba.
Shiko uncle farhaan mutuwar matarshi ce ya daga mishi hankali sosai, Dan duk a tunaninshi tana raye bata mutu ba.
Ashnaah ce ta kawo mishi little afrah, hakan ya sashi farin ciki sosai ganin yarshi tana raye. Mom afrah dae sai albarka take sa mishi tare da bashi hakuri dan duk ta sanadinta ne wadannan abubuwa suka faru da shi, and he showed her its nothing else.
Sarki abdulaxix ne yace ya kamata kowa yaje ya huta xuwa gobe akwai taro sannan kuma xa'a bawa alameen sarautarshi.
Haka nan kowa ya watse cike da farin ciki azrah kuwa ance taje ta da abinda ya shuka Allah xai saka ma kowa. Haka nan tana kuka tat tattara kayanta ta koma kasarsu.
Friday 10:am
Kowa ya hallara a falon nan har fa fadawan fake cikin masarautar.Sarki abdallah ne ya bude taron adduoi sannan sarki abdulaziz ya cigaba da jawabi.
"Mun gode wa Allah da ya kawo my wannan rana mai cike da farin ciki, familyn mu ta dawo yanda take da, muna rokon Allah kuma ya sake tsare mu daga sharrin makiya"
Duk aka amsa da amen.
Nan sarki abdulazeez ya mika jawabin godiya sosai da yah Abdul da kuma uncle farhaan visa kokarin da sukayi sannan ya cigaba da fadin "tunda mai waje yaxo dole mai tabarma ya nade, mulkin nan dae as u know na alameen ne, to a yau xan damka mishi mulkinshi tamkar yanda nayi alkawari"
Murmurshi alameen yayi tare da fara magana "Sam ban cancanci na mulki al'umma ba, am not bold enough to handle this. Bubbuga kafadar yah Abdul yayi tare da cewa "ra'ouf shi ya dace ya mulki wannan masarautar ba ni ba, ina neman alfarmarku da ku bashi wannan mulkin, dani da shi duk abu daya ne, Bana tantama akanshi xai iya rike wannan masarautar da al'ummar dake cikinta"
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...